Da sana’ar sassakar turmi nake daukan karatun ’ya’yana biyu a jami’a – Ibrahim Dabai

Sana’ar sassakar turmi tsohuwar sana’a ce da a yanzu za a iya cewa zamani na kokarin gurguntar da ita lura da yadda ake samun karuwar kayayyakin da fasahar zamani ke ci gaba da kirkira da suka hadar da injinan nika masu aiki da man fetur ko wutar lantarki. Sai dai a zantawar da Aminiya ta […]

Da sana’ar sassakar turmi nake daukan karatun ’ya’yana biyu a jami’a – Ibrahim Dabai

Sana’ar sassakar turmi tsohuwar sana’a ce da a yanzu za a iya cewa zamani na kokarin gurguntar da ita lura da yadda ake samun karuwar kayayyakin da fasahar zamani ke ci gaba da kirkira da suka hadar da injinan nika masu aiki da man fetur ko wutar lantarki. Sai dai a zantawar da Aminiya ta yi da Malam Ibrahim Abdullahi Dabai wanda ke sana’ar sassaka turame da sayar da su ya ce, ko kadan fasahar zamani ba ta taba sana’arsa ba kuma ba ya ganinta a matsayin kalubale da ka iya gusar da sana’ar tasu domin har yanzu al’umma na sayen turame kuma suna yin amfani da su kamar yadda suke yi a baya.

Malam Ibrahim Abdullahi Dabai wanda ya ce, shi dan Jihar Kebbi ne ya shaida wa Aminiya cewa sana’ar sassakar turmi sana’a ce mai muhinmmanci da ke tattare da albarka, ya ce suna zuwa dazuzzukan Jihar Neja ne su sayo turamen sannan su gyara su, su goge su har sai sun yi sumul sannan su shafa musu mai ko kitse ta yadda za su yi kyau siffarsu ta fito tana kyalli, “Wadanda muke saye a wajensu a can dajin ba su gyarawa sassaka kawai suke yi, mu ne muke sake alkinta su idan mun sayo ta yadda za a gani a yi shaawa,” inji shi.

Ya ce fasahar zamani ta Bature ba ta taba daga musu hankali a sana’arsu ta gargajiya ba, “Domin ka gani ina kawo turmi nan Legas ne in gyara shi in sayar, kuma akasarin masu sayen turmin su ne masu yin sakwara da ake yi da doya wadda bayan an dafa ta sai a sanya ta a turmi a kirba sai ta yi laushi a yi ta mara-mara kamar yadda ake yi wa tuwo, to ai Bature ya yi injin daka sakwara amma sakwarar da aka yi da injin Bature ba ta zamowa guda da wacce aka yi da turmi, domin ta injin za ka ji ta kamar tuwon masara. To ka ga wannan bambancin shi ne ya sa kake ganin har gobe ana yi da mu, domin inji ba ya yi kamar turmi, don haka ka ganin ga ni ga kasuwar doya ta Ilepo mutane kan shiga kasuwar su sayi doya su zo wajena su sayi turmin daka sakwarar,” inji shi.

Ya ce, masu sayen turamen akasarinsu Yarbawa ne da ke yin sakwara don haka turmin da suke sassaka ya bambanta da wanda ake amfani da shi a Arewa, “A Arewa turmin surfe ne ya fi yawa wanda ake surfa hatsi za ka gan su dogaye ne akasarinsu, mu ko namu gajeru ne wadanda ake yin sakwara babu irinsu da dama a Arewa har sai ka je yanki Gwari da Nupe inda su ne suke yin sakwara a Arewa,” inji shi.

Malam Ibrahim Dabai ya ce cinikin turmi abu ne mai sirri kwarai, ya ce suna sayar da turmi daya daga Naira dubu shida zuwa dubu 12. “Ya danganta da kyansa  da kuma irin itacen da aka yi shi da kuma mai sayen kansa, wani zai saya da daraja wani kuma akasin haka, shi turmi abu ne da in wani ya saya ba ya kuma saye har mutuwarsa, amma hakan ba ya hana samun ciniki domin a lokacin da wani ya riga ya sayi nasa wani kuma yana can yana shirin saye wani kuma na da niyyar saya nan gaba, wani  kuma har ya mutu ma ba zai samu ikon saya ba sai dai aro, to haka abin yake. Guda-guda da ake zuwa saye shi ke rike sana’ar, kuma alhamdulilahi kusan kullum sai an zo an saya mun samu na abinci,” inji shi.

Ya ce, ya sami alfanu da dama a sana’ar tasa domin a ciki yake dawainiyar karatun ’ya’yansa biyu wadanda suke karatu a Jami’ar Aleiro da ke Jihar Kebbi suke kuma dab da kammala karatunsu,  daya na karantar Kimiyyar Kananan Halittu (Micro Biology), daya kuma yana karantar kimiyyar hada sinadare. “Da shekaranjiya ka zo nan za ka samu ’ya’yan nawa a nan suna kama min aiki,  amma yanzu sun koma Arewa,  fatana su kammala karatu su samu sana’a wacce ta fi tawa. Sai dai kiran da zan yi wa matasa shi ne su guji raina sana’a komai kankantarta duk sana’ar da ka gani da irin nata alherin, don haka in kana da sana’a ka rike ta da muhinmmanci ka tsaya wa ’ya’yanka su yi karatu domin gudanarwa kada ku tsaya a waje guda,  wato uwa a kwance da a kwance,” inji shi.

Ya ce, babban kalubalen da yake fuskanta shi ne janyewar cinikin turmin a lokacin damina wato lokacin da doya ta fara janyewa a kasuwa. Ya ce idan babu doya kasuwarsu na samun tawaya, sannan kalubalensu na biyu shi ne wajen sayo turmin idan lokacin aikin damina ya yi suna fuskantar