‘Da sana’ar tukin Keke Napep na bauki nauyin karatuna’
Umar Salihu Jama’a wani matashi ne da ya kwashe fiye da shekara 13 yana sana’ar acaba da tukin Keke Napep a garin Kafanchan. A wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya, ya bayyana yadda ya bauki nauyin karatunsa da albarkacin sana’ar har matakin gaba da sakandare: Aminiya: Za mu so ka fara da gabatar da […]
Umar Salihu Jama’a wani matashi ne da ya kwashe fiye da shekara 13 yana sana’ar acaba da tukin Keke Napep a garin Kafanchan. A wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya, ya bayyana yadda ya bauki nauyin karatunsa da albarkacin sana’ar har matakin gaba da sakandare:
Aminiya: Za mu so ka fara da gabatar da kanka?
Sunana Umar Salihu Jama’a, amma mutane sun fi sani da banladi No Ribal. Ni haifaffen cikin garin Kafanchan ne kuma a nan na yi karatu tun daga firamare har zuwa matakin gaba da sakandare, inda na samu takardar shaidar Difloma kan Harkokin Shugabanci (Public Administration) a Kwalejin Horar da Malamai, wato College of Education Kafanchan. San nan na sake zuwa makarantar koyon kwamfuta na yi karatun satifiket kan harkar kwamfuta.
Aminiya: Bayan ka kammala karatu ne ka fara sana’ar acaba?
A’a, kafin sana’ar acaba na ban taba wasu harkoki kafin daga baya na dawo kanta. Tun muna yi da babura har zuwa lokacin Keke-Kapep. Gaskiya ni wannan sana’ar da ita nake alfahari saboda da ita na bauki nauyin kaina na yi karatun gaba da sakandare. Ka ga ke nan ba sai da na yi karatu sannan na kama sana’ar ba. Sana’ar ce ta dau nauyin karatuna kuma ita na ci gaba da yi kafin in aikin gwamnatin ya samu falillahil hamdu domin na nemi aikin soja da na ban sanda da hukumar kula da kiyaye haburra ta kasa (Road Safety) da na kwastam duka ban samu ba, duk lokacin da na samu zan yi, in ma ban samu ba ina da madafa.
Aminiya: Yanzu ka gamsu da sana’ar tukin Keke Napep ke nan?
kwarai kuwa. Domin kamar yadda na faba maka da ita nake ci da sha nake komai da komai gaskiya tana rufa min asiri don babu ranar duniya da zan fita in ce ban samu wani ba. Kuma na faba maka dama da shi na yi karatun Difloma bina don haka ina mutunta sana’a ta.
Aminiya: Wabanne irin matsaloli kake fuskanta a wannan sana’ar?
Da farko dai sana’ar acaba ka san tana cike da habarurruka, musamman na rashin kula da dokokin kan hanya da na tuki daga wasunmu. Matsala ta biyu ita ce ta barayi da ke tare ’yan acaba su kwace baburan wani lokaci ma su bubbuge shi su tafi, ko ni hakan ta taba faruwa da ni kamar shekaru uku da suka wuce, wannan su ne kaban daga cikin matsalolin da muke fuskanta.
Aminiya: Ko kana da wani kira ga matasa?
Babu matsalar da ta wuce zama babu sana’a. In ma arziki kake nema ai babu sana’ar da Allah ba zai iya azurtaka da ita ba. Idan ka dubi yawancin direbobin da muke da su za ka ga daga sana’ar acaba suka fara don haka mu rungumi sana’a komai kankartarta tare da hakuri da kawar da kai daga abin hannun mutane shi ne rufin asirinmu.