Da sana’ar yankan farce na sauke farali —Abdulkadir

Alhaji Ali ya watsar da noma da kiwo ya koma sana’ar yankan farce.

Da sana’ar yankan farce na sauke farali —Abdulkadir

Wani mai sana’ar yankan farce, Alhaji Ali Abdulkadir, ya ce sana’ar ta yi masa komai na rayuwa, ba shi kadai ba har da makusantana.

Sana’ar yankan farce sana’a ce da ba ta bukatar wani babban jari, domin da Naira dubu daya za a iya yin ta.

A yayin zantawarsu da Aminiya a garin Kalaba na Jihar Kuros Riba, Alhaji Ali Abdulkadir ya ce “Wannan sana’ar ta yi min komai a rayuwa,” domin a cewarsa, daga lokacin da ya fara sana’ar zuwa yanzu kwalliya ta biya kudin sabulunta.

Ya ce ya fara sana’ar noma da kiwo sannan daga bisani ya fara sana’ar yin yankan farce a shekarar 2005.

Sana’ar ta kai ni Saudiyya

Ya ci gaba da cewa yana yi wa manyan mutane yankan farce da suka hada da sojoji da kuma manyan jami’an gwamnati.

A cewarsa, yana tsaka da yin wannan sana’a ce Allah Ya hada shi da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kuros Riba, a lokacin suna mulki, wanda dama shi ke yanke masa farce da iyalansa kafin ya samu mulki.

“Yakan aiko da mota a zo a dauke ni, in je gida in yi musu yankan farce,” inji shi. Ya ce kuma har yanzu bai daina yi masu yankan farce ba.

Ya kara da cewa, “Wata rana ina yi wa Mataimakin Gwamna Effiok Cobham yankan farce, sai ya tambaye ni ko na taba zuwa aikin Hajji, na ce masa a’a, sai ya ce da ni to bana aikin Hajji da ni za a yi shi.

“Ina ganin abu kamar tatsuniya, ina zaune a bencina ina yankan farce sai aka kira ni, aka ce in kawo hoto kanana guda biyu.

“Bayan na bayar ne sai daga baya kuma aka sake kira na a Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Ribas, inda aka tabbatar min da cewa da ni za a yi aikin Hajji.

“Haka dai lamarin ya kasance, na ci gaba da shiri har lokacin tafiya ya yi; muka yi aikin Hajji a shekarar.”

Hakazalika ya ce a wannan sana’a ta yankan farce ya samu dimbin alheri da ba za su misaltu ba .

“Na yi aure, na mallaki muhalli nawa na kaina, ina taimaka wa iyaye, ’yan uwa da abokan arziki.

“Don haka, babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Ina zaune lafiya kalau da kowa, babu wata matsala,” kamar yadda matashin ya bayyana wa Aminiya.