Da sanin gwamnati ake kashe-kashe a Arewa -Gwamna Nyako

Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako ya bayyana cewa da sanin gwamnati ake kashe-kashe a Arewacin Najeriya, kuma an kirkiro rikicin Boko Haram ne domin a kassara Arewa.Ya bayyana hakan ne yayin taron kwana uku kan tattalin arziki da kalubalen da ake fuskanta kan tsaro a Arewacin Najeriya da aka yi a Birnin Washintong D.C da […]

Da sanin gwamnati ake kashe-kashe a Arewa -Gwamna Nyako

Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako ya bayyana cewa da sanin gwamnati ake kashe-kashe a Arewacin Najeriya, kuma an kirkiro rikicin Boko Haram ne domin a kassara Arewa.
Ya bayyana hakan ne yayin taron kwana uku kan tattalin arziki da kalubalen da ake fuskanta kan tsaro a Arewacin Najeriya da aka yi a Birnin Washintong D.C da ke kasar Amurka. Cibiyar Zaman Lafiya da ke Amurka ce ta dauki nauyin shirya taron daga 17 zuwa 19 ga watan Maris, 2014.
Gwamna Nyako ya ce mutanen Arewa sun fara zargin akwai wadansu manyan shugabanni a gwamnati da ke daukar nauyin kashe-kashen da ake yi a Arewa, inda suke taimakawa da kudinsu da kuma duk wata dama da suke da ita don bunkasa kashe-kashen.
Ya kuma yi zargin akwai kyakkyawar alaka da kuma shiri tsakanin ’yan kungiyar Boko Haram da kuma wadansu daga cikin manyan kwamandojin jami’an tsaron kasar nan.
Ya ce ya rubuta wa fadar shugaban kasa wasiku biyu masu dauke da bayanin yadda za a magance rikicin Boko Haram, amma da yake Gwamnatin Tarayya ba ta da masaniyar babban kalubalen da take fuskanta dangane da rikicin, sai ba ta yi komai a kai ba.
Akwai alamun da suka nuna wadansu daga cikin gwamnonin da suka halarci taron ba su yi amanna da abin da Gwamnan Nyako ya fada ba, amma sai suka yi gum da bakinsu.
Bayan taron ne, sai a ranar Litinin da ta gabata, Gwamna Nyako ya aika wa kafofin watsa labarai da kofin mukalar da ya gabatar yayin taron na Amurka, wanda yake dauke da nazarin da ya yi kan rikicin Boko Haram.
A mukalar ya ce: “Da farko ana tsammanin cewa rikicin Boko Haram yana da alaka da addini, amma yanzu babu wanda yake alakanta rikicin da addini, idan ba wanda yake da gurguwar fahimta ba, kasancewar duk wuraren da ’yan kungiyar suka kai hare-harensu a yankunan Musulmi ne. Yanzu mece ce alkiblar rikicin Boko Haram? Ya kamata mu amsa wa kanmu wannan tambayar don mu fahimci alkiblar rikicin don mu gane wane irin yaki muke yi.
“Su kansu ’yan Boko Haram din a rude suke tun da sun gaza tabbatar da wane irin yaki suke yi, da farko sun kona Hedikwatar Majalisar dinkin Duniya da ke Abuja, sannan sun kona masallatai da majami’u, sun kuma kashe jama’a masu yawa daga ciki akwai Musulmi da Kirista, ba kuma tare da sun bambance kowane yare ba. Rikicin ya rutsa da kowace kabila.
“Don haka wannan abin bakin ciki da takaici ne a ce duk da cewa na rubuta wa fadar shugaban kasa wasiku biyu masu dauke da shawarar yadda za a magance rikicin amma ta yi watsi da shawarwarin da na bayar, wanda hakan ke nuna ba ta fahimci irin kalubalen da ake fuskanta dangane da rikcin ba. Tabbas, ba ta fahimci wane irin yaki take yi ba. Shin yaki ne da ’yan ta’adda ko mahara ko kuma yaki ne da aka shirya don a kassara Arewacin Najeriya? A takaice dai, ko kashe dimbin jama’a da barnata dukiya da bata muhalli da ake yi duk shiri ne na gwamnati kamar yadda wadansu suke cewa?
Gwamnan Nyako wanda shi ma tsohon sojan ruwa ne, ya yi wa jami’an tsaro wadansu tambayoyi da ke nuna akwai sakacinsu ko kuma hannunsu cikin rikicin.
Ya ce: “Ya kamata mu fuskanci matsalar. An ce an kama jama’a da dama da ake zargin ’yan Boko Haram ne, sai dai Gwamnatin Tarayya ko jami’an tsaron Najeriya har zuwa yanzu sun kasa gudanar da binciken da zai sa su gano manyan kwamandojinsu ko masu yi musu tsare-tsare ko kuma wadanda suke tallafa musu ko suka dauki nauyinsu ba.  
“An ce sansanin ’yan Boko Haram na cikin Dajin Sambisa, an kuma ce cike yake da ’yan kungiyar da kuma dimbin  makamai, sannan jami’an tsaron da ke Arewa maso Kudu suna da masaniyar yadda dajin yake, amma abin bakin ciki sai dai mahukunta su rika yi mana bayani lokaci zuwa lokaci, hakan ma ba gamsasshe ba.
“A yanzu dai mun sake fahimtar wata makarkashiya, inda ake kashe dimbin jama’a da kuma lalata dukiya a yankin  Arewa maso Gabas da sunan Boko Haram, bugu da kari ga yadda ake sace shanu a dukkan jihohin Arewacin Najeriya, wanda kuma an yi hakan ne don a gaddasa rikici tsakanin kabilun Arewa ko kuma tsakanin Musulmi da Kirista a yankin Arewacin Najeriya.
Nyako ya ce, ta yaya za a shigo da dimbin makaman da ’yan Boko Haram ke amfani da su ba tare da an gano ba?
Ya kara da cewa, “Bari na yi wa wadanda suka halarci wannan taron wani bayani. Kowa dai ya sani harsasai da bindigogi da bama-baman da ’yan Boko Haram suke amfani da su ba a Najeriya ake kera su ba. Idan kuwa hake ne to wane ne ya shigo da su, ya kai su wuraren da za a kai hare-hare da su, kasancewar shingayen jami’an tsaron da ake su a Arewacin Najeriya sun fi na lokacin da aka yi Yakin Basasa yawa, kuma idan aka cire shugaban kasa da mataimakinsa da manyan mahukunta da gwamnonin jihohi da kuma jami’an tsaro babu wadanda suke wuce wadannan shingayen ba tare da duba su ba. Idan kuwa haka ne za mu iya zaton cewa wadannan rukunin ne suke safarar makaman a kasar nan daga tashar jiragen ruwa bayan jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro sun ba da izinin shigowa da su cikin kasa.
“Don haka za a iya cewa wadansu bata-gari da wadansu jami’an gwamnati da sauran jama’a ne ke dauakr nauyi da kuma tallafa wa matsalar tsaron da muke fuskanta a Arewacin Najeriya don siyasa. Babu wani mutum ko mutane daga Arewa maso Gabashin Najeriya da yake da arzikin da zai iya daukar nauyin ayyukan Boko Haram. Don haka wani daga wata shiyya ne zai sayi harsasai da bindigogi da kuma bama-baman daga wani wurin da za a iya ganowa, tun da za a biya kudi, za a sauke makaman a tashar jirgin ruwa, sannan a yi safararsu a cikin kasa bayan an wuce shingayen jami’an tsaro, sannan a ajiye su a wuraren da ake so kafin a raba su ga makasa.
“Yanzu dai ta bayyana karara akwai kyakkyawar alaka tsakanin ’yan Boko Haram da kuma manyan kwamandojin da ke rike da manyan ofisoshi a ma’aikatar tsaron kasar nan.  Me ya sa ake kai hare-hare a wuraren da ake so a kai, kamar makarantu da kwalejoji da zarar jami’an tsaro sun bar wadannan wuraren? Ba wai kawai a da zarar jami’an tsaro sun bar wadannan wuraren ake kai hare-haren ba; masu hare-hare kan dauki awanni masu yawa suna barna ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba, duk da cewa a wadansu wuraren jami’an tsaro za su iya jin karar harbe-harbe ko tashin bama-bamai.
“Akwai lokacin da ’yan Boko Haram suka kona jirgi mai saukar ungulu na jami’an tsaro; an kona jirgin ne a kusa da barakin sojoji. Abin mamaki sojoji ba su iya yin komai ba. Ba ma wannan ba, akwai lokacin da ’yan Boko Haram suka kashe wani tsohon Janar din da ya yi Yakin Basasa don Najeriya ta ci gaba da kasacewa a matsayin kasa daya, abin takaicin hakan ya faru ne a kusa da shingen jami’an tsaro, wadanda aka dora musu alhakin samar da tsaro a wannan yankin, amma har aka kashe Janar din makasan suka tsere, jami’an tsaro suka kasa katabus.
Nyako ya kara da cewa, tabbas jami’an tsaron da suke Arewa maso Gabashin Najeriya suna fama da matsalar karancin kayan aiki da abinci da sauransu.
“Lokacin da aka dibar mini ya yi kadan da na yi bayanin  wadansu abubuwa. Amma ina so a sani, kusan dukkan sansani ko barakin sojoji a yankin Arewa Maso Gabas suna fama da karancin kayan aiki, suna da bindigogi amma babu harsasai, wadansu   ba su cin abincin da ya kamata, duk da makudan kudaden da aka ce ana kashewa a kansu da sunan yaki da ta’addanci daga Abuja (Gwamnatin Tarayya). Abin mamakin shi ne jami’an tsaron da suke Abuja (garin da ba a yaki), an fi lura da su, an fi kuma wadata su da kayan aiki fiye da wadanda suke Arewa maso Gabas.
“Don haka wadannan manyan kwamandojin suna yaki da Arewa ne kawai bayan sun yi amfani da sunan  ‘yaki da ta’addanci’ don hakan ya zama musu garkuwa wajen cim ma kudurinsu na kassara Arewa, musamman ma a bangaren siyasa. Wadansu ma suna ganin an kirkiro Boko Haram ne don a kashe sarakuna da kuma manyan ’yan siyasar Arewa, ko kuma don a kawo silar da za a raba Najeriya.
“Mutanen Arewa sun fara zargin an ki magance matsalar Boko Haram ne don a hana ’yan Arewa damar gudanar da zabe, wato za a yi amfani da rikicin don a ki yin zabe ko kashe zabe, ko kuma a yi ta kashe mutane, musamman ma matasa don a rage yawan mutanen Arewa da za su yi zabe mai zuwa ko zuwa nan gaba.   
Nyako ya yi wa fadar shugaban kasa wadansu tambayoyin dangane da Boko Haram. Ya ce: “Wane ne yake ba da izinin kashe-kashen da kuma ayyukan Boko Haram, kasancewar an sha yunkurin kashe wadansu gwamnoni ciki har da ni da kuma Gwamnan Jihar Binuwai, da manyan sarakunan Arewa kamar su Shehun Barno da Sarkin Kano da sanatoci da kuma manyan ’yan kasuwa da aka rika kai musu hare-hare da ranar tsaka, inda suka rika tsallaka rijiya da baya. Wane ne ya ba su izinin kashe mu? Me muka yi musu?
“Shin ko Arewacin Najeriya na sake fuskantar ajandar kashe-kashen manyan ’yan siyasarta da sojojinta ne kamar yadda aka yi a shekarar 1966? Don haka ya kamata fadar shugaban kasa ta amsa mana wadannan tambayoyin, ba ma son masu Magana da yawun shugaban kasa su zage mu maimakon su ba mu amsoshin da za su gamsar da mu. Muna bukatar amsoshin tambayoyin; ’yan Najeriya ma na bukatar amsoshin tambayoyin. Haka sauran kasashen duniya ma suna da bukatar sanin amsoshin.
Gwamnan ya bayar da misali da wasikar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wacce ya aike wa Shugaba Goodluck Jonathan da kuma tonon sililin batan Dala biliyan 20 da Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya yi, wanda a yanzu aka dakatar da shi.
Ya ce amsar da masu Magana da yawun shugaban kasa suka bayar ko kadan ba su gamsar ba.
Ya ce: “Bari na dan taba wadansu bangarori da suka taimaka wajen bunkasa matsalar tsaro a Arewacin Najeriya da kuma Najeriya gaba daya. Cin hanci da rashawa da taka doka da sama da fadi da kudaden al’umma da wadansu manyan shugabanni a gwamnati suke yi, kamar yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana a wasikarsa da kuma bayanan da tsohon Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya yi kan batan dabon biliyoyin daloli na al’umma sun tayar da kura.
“Amma amsoshin da aka bayar masu daure kai ne, wadanda suke nuna karairayin da aka shara. Taka doka da cin hanci da rashawa sun zama jarunntaka a Najeriya. Suna tsammani za su yaudare mu har mu amince 16 ta fi 19, kuma 5 ta fi 27.
“A bangare matsalar tsaro babu wanda ya haura tudun mun tsira idan dai a Arewa yake. A kowane lokaci za ka iya jin ciwo ko ka mutu duk a dalilin izinin kisa da ake samu daga wadansu tsirarun bata-gari daga Abuja. Masu wayo a cikinmu su ne masu barci da ido daya. Ta yaya za mu yarda da wadanda muke zargi da kashe mu? Wane ne zai yarda da wadannan shugabanni har ma ya yi huldar kasuwanci da su? Haba, shi ya sa ba zai zama abin mamaki ba da kasashen duniya da abokan huldar cinikayyarmu daga sauran sassan duniya suka yi watsi da Arewa da ma Najeriya gaba daya.” Inji Nyako.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton fadar shugaban kasa ko hedkwatar tsaro ta Najeriya ba su mayar wa Gwamna Nyako da martani ba, kuma duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ba bakin Kakakin shugaban kasa Dokta Rueben Abati lamarin ya ci tura.