Da sauran Gwamnonin Arewa za su bunkasa noma

Dukkan ma`abucin bibiyar wannan shafi ya kwan da sanin cewa yadda za a samu habakar ayyukan gona da kiwo musamman a jihohin Arewa 19, na cikin batutuwan da na fi mayar da hankali wajen yin tsokaci kansu. Wasu daga cikin dalilan da suka sa na fi damuwa da wannan fanni ba su wuce irin yadda […]

Da sauran Gwamnonin Arewa za su bunkasa noma

Dukkan ma`abucin bibiyar wannan shafi ya kwan da sanin cewa yadda za a samu habakar ayyukan gona da kiwo musamman a jihohin Arewa 19, na cikin batutuwan da na fi mayar da hankali wajen yin tsokaci kansu. Wasu daga cikin dalilan da suka sa na fi damuwa da wannan fanni ba su wuce irin yadda nike ji daga masana tattalin arzikin kasa da na ayyukan gona  cewa tattalin arzikin kasashen duniya da suka ci gaba ya dogara ne kacokan a kan irin yadda suka rungumi ayyyukan gona gadan-gadan. 

Amma mu a nan kasar, tarihi ya tabbatar da cewa daga lokacin da man fetur ya bulla a shekarar 1957, yau sama da shekaru 60, muka fara ja da baya da ayyukan gona, alhali daga kudaden gyada da auduga da kwara da fatu da kiraga da danko da koko, da manomanmu suka samar aka aza harsashin duk wani abu na tattalin arzikin kasar nan, hatta man fetur da a yau wasu mutanen yankunan da suke da shi, suke yi wa Arewa gorinsa, daga kudin wadancan kayayyakin amfani gona aka fara hako shi.

Ka gani mai karatu, tun daga wancan zamani wasu daga cikin wadanda suka yi mulki a jihohin Arewa har zuwa yau suka yi watsi da ganin ingantuwar ayyukan gona, alhali shi kadai ne  abin da ka iya ceton tsohon lardin daga afkawar da mutanensa da ma sauran `yan kasa suka yi cikin mayatar fatara da talaucin da har ake yi wa `yan Arewan sun zama kaska a kan arzikin man fetur.

Duk kuwa da kasancewar daga lokaci zuwa lokaci masana fannin tattalin arzikin kasa da ma na fannin ayyukan gona da ma na fannin tattalin arzikin kasa sun sha ba Gwamnonin Jihohin Arewa shawarwari wala alla a kan radin kan masanan ko bisa ga bukatar gwamnonin (kamar yadda Gwamnonin Jjihohin Arewa zubin farko a wannan jamhuriyar 1999 zuwa 2003), suka kafa wani kakkarfan kwamitin masana ayyukan gona da suka ba su shawarwari a kan yadda za su farfado da ayyukan gona da kiwo a jihohinsu, lokacin da gwamnonin da ake hako man fetur da tsagerun matasansu suka yi ta matsin lambar sai a bar ba su dukkan arzikin man fetur dinsu, neman da har yanzu ba su daina ba. Gwamnoninmu na Arewa kuma kama yanzu ba wanda ya waiwayi rahoton Kwamitin. 

Don haka jin labarin gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma, wato, Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar na Jigawa da Alhaji Aminu Waziri Tambuwal na Sakkwato da Dokta Abdullahi Umaru Ganduje na Kano da Alhaji Aminu Bello Masari na Katsina da Alhaji Abubakar Bagudu na Kebbi da Malam Nasiru eL-Rufa`i na Kaduna, bayan tattaunawar tsawon shekara daya da suka yi ta yi, yanzu bayan wani taro da suka yi a Masaukin Gwamnan Jihar Katsina da ke Abuja a ranar Juma`ar makon jiya, sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya da za ta ceci jihohinsu da mutanensu, ta hanyar habaka ayyukan gona da kiwo.

A wajen wancan taro, Gwamnonin Shiyyar Arewa maso Yamman a karkashin sabuwar kungiyarsu ta Gwamnonin Shiyyar Arewa maso Yamma sun amince, tare da daukar alwashin za su kara samar da filayen noma masu yawan gaske kuma ingantattu, don gudanar da ayyukan noma daban-daban, da zai ba da gagarumar dama ga manoman jihohin bakwai, su noma dukkan abin da suke bukata, tare da samar musu kasuwar da za ta rinka sayen dukkan abin da suka noma a kan ingantaccen farashi kuma a kan kari.

Taken shirin dai shi ne “Gawurtaccen  hadin kan tattalin arziki na jihohin shiyyar Arewa maso Yamma,“ da gwamnonin suke fatan ya haifar da wani juyin juya hali, ta hanyar haifar da tsare-tsare da matakai da za su taimaka wajen habaka tattalin arziki da na zamantakewar shiyyar da mutanenta, musamman miliyoyin matasan da suke zaman kashe wando. Wata kungiya mai zaman kanta mai sunan kungiyar Bincike da Ci gaban Arewa, da ke karkashin shugabancin Dokta Usman, ita za ta zama mai ba da shawarwari cikin gudanar da shirye-shiryen ayyukan gonar a shiyyar.

Mai masaukin gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, daga bisani ya fada wa manema labarai cewa, gwamnonin sun yanke shawarar za su rinka zuba makudan kudi a cikin shirin ta yadda kowace jiha za ta rinka noma amfanin gonar da ya fi karbuwa, yake kuma samar da kyakkywar yabanya a yankin da aka noma shi.

Ba ko shakka jin labarin wannan yunkuri na gwamnonin shiyya ta Arewa maso Yamma, shiyyar da ta fi sauran shiyoyin kasar nan biyar yawan jama`a da yawan madatsun ruwa, shiyya kuma da take ta biyu a yawan filin kasa in ban da shiyyar Arewa maso Gabas, wani babban abin da za a yi maraba da shi ne. Alal misali Jihar Kano ita ta fi kowace jiha yawan al`umma da kuma yawan madatsun ruwa 17, amma manoman jiharsu na ta kokawa a kan yadda mahukunta suka kasa inganta wadannan madatsun ruwa, balle samar da filayen noman rani da za su bayar da dama manoman jihar su rinka yin noma rani da damina a kalla sau uku a shekara. Haka wannan labari yake a sauran jihohi shiyyar irinsu Sakkwato da Katsina da Kebbi da Kaduna da Zamfara da Jigawa.

Tunda yanzu gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamman, sun sha wannan alwashi, to kuwa ya kamata su mayar da hankali wajen wadata manomansu da takin zamani da sauran kayayyakin ayyukan noma, kamar ingantaccen iri kuma dan wuri da maganin kwari da fari da na ciyawa da ma kudin da za su yi noman a kan lokacin da ya dace da sunan rance mai saukin kudin ruwa. Ba kamar yanzu ba da sai damina ta gama sauka tana kokarin ma fita kana za a rinka jin kururuwar gwamnatoci suna samar da wadancan kayayyaki noma. 

Su kuma manoma ya kamata su sa tsoron Allah a cikin zukatansu, ta yadda za su daina ganin kyashin biyan dukkan kudin kayayyakin ayyukan gona da aka tallafa masu da zarar sun girbe, sun kuma sayar da amfanin da suka noma, musamman a wannan sabon shirin, Gwamnonin Shiyyar Arewa maso Yamman sun tabbatar da za su samar da kasuwa a kan dukkan abin da manomansu suka noma. Abin da ya sa na kawo wannan batu, bai wuce irin yadda yanzu rahotanni suke tabbatar da cewa Manoman Jihohin Kebbi da Kano da suka ci gajiyar tsarin tallafin Gwamnatin Muhammadu Buhari na noman shinkafa da alkama, sun yi mursisi sun shafa wa idanuwansu toka sun ki biyan basussukan, duk kuwa da irin dimbin ribar da suka samu. 

Mai karatu kin biyan basussukan da manoman suka yi ya nuna ma karara irin mugunta ko mugun ra`ayin da aka dade ana fama da shi na cewa ai kudin gwamnati ne. kokarin ganin manoman Jihar Kano da suka ci gajiyar wancan bashi ya sa yanzu gwamnatin jihar take ta shirye-shiryen kafa Kotunan da za su karbo basussukan ko ta halin kaka. Haka zalika akwai bukatar gwamnonin sauran shiyyoyin Arewa biyu, su ma su himmatu su kafa irin wannan kungiya, tunda dai yanzu ta tabbata arzikin man fetur ba mai dorewa ba ne, kamar yadda ayyukan noma da kiwo suke dauwamammu, kuma masu bunkasa tattalin arziki tun daga can kasa.