Da siyasa cikin dakatarwar da aka yi wa Sanusi -Lawan Inuwa

Wani matashin dan kasuwa mazaunin garin Benin a Jihar Edo mai suna Alhaji Lawan Inuwa ya danganta sallamar da gwamnatin tarayya ta yi wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi daga mukaminsa da saddabarun siyasa. Alhaji Lawan ya yi furucin hakan ne a wata hira da Aminiya a garin Benin, fadar mulkin gwamnatin Jihar […]

Da siyasa cikin dakatarwar da aka yi wa Sanusi -Lawan Inuwa

Wani matashin dan kasuwa mazaunin garin Benin a Jihar Edo mai suna Alhaji Lawan Inuwa ya danganta sallamar da gwamnatin tarayya ta yi wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi daga mukaminsa da saddabarun siyasa.
Alhaji Lawan ya yi furucin hakan ne a wata hira da Aminiya a garin Benin, fadar mulkin gwamnatin Jihar Edo a farkon wannan makon, inda ya nuna matukar damuwa da wannan matakin na gwamnatin tarayya, wanda tun ba a je da nisa ba, an fara ganin illarsa dangane da tafiyar tattalin arzikin kasa.
dan kasuwan ya ce hakan bai bi tsari ba, “Kuma tun farko ma yin hakan ya kauce wa dokar tsarin mulkin kasa, kodayake ba wani abin mamaki ba ne kuma bai kasance wani abu sabo ba, idan aka yi la’akari da wannan lokacin da muke ciki, inda shugaban kasa ya bi cikin dabaru na siyasa yana sauke duk wadanda suke gaya masa gaskiya daga cikin gwamnatinsa”.
Ya ce da ana son a kyautata salon shugabanci, a halin da ake ciki, kamata ya yi a fuskanci lamarin da ya danganci tsaro da sauran ayyukan da za su kawo kyakkyawan cigaba da kwanciyar hankali ga jama’a. “Ina ganin akwai rashin adalci, idan muka duba a can baya ai akwai ministocinsa biyu, wadanda suka tafka almundahana a bakin aikinsu, wanda bincike ya tabbatar da hakan, amma da yake ’yan gaban goshin gwamnatisa ne kuma shafaffu da mai a wurinsa, sai aka yi shiru.” Inji shi.
dan kasuwan ya ce, “Cire Sanusi a kan zarginsa da yake yi na son dora masa laifin da bai aikata ba, wannan rashin adalci da neman hanyar cin mutunci ne kurum, kuma a fili ya nuna akwai siyasa hade da kabilanci tare da bambanci na addini da nuna bangaranci a ciki, na fifita wani bangare, a wulakanta wani bangare. Kuma ya nuna hakan ba yana nufin zai yi wani adalci ko gyara ba, ya yi ne don biyan bukatar kansa ne kurum”.
A karshe ya nemi Malam Sanusi Lamido Sanusi ya tashi tsaye ya nemi  hakkinsa, kuma yana goyon bayansa da yi masa fatar alheri tun lokacin da ya shigar da kara a kotu, “Domin  ta hakan ne kurum za a bi masa kadinsa kuma a nan gaba za a tabbatar da an baiwa kowane dan Najeriya hakkinsa, kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanadar. Ita kotu ce kadai za ta iya tantance komai ta ture kariya, ta tabbatar da gaskiya da adalci”.