Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
Tare da SheikhYunus Is’hakAlmashgool, Bauchi Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. Babi na Farko: Bayanin rubutun fansa. Shi ne bawa ya dauki alkawarin biyan kimar kudin da aka saye shi zuwa ga shugabansa: Babi na Biyu: Laifin wanda ya yi wa bawansa ko baiwarsa kagen zina: Babi na Uku:Bayanin wanda aka rubuta masa biyan […]
Tare da Sheikh
Yunus Is’hak
Almashgool, Bauchi
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
Babi na Farko:
Bayanin rubutun fansa. Shi ne bawa ya dauki alkawarin biyan kimar kudin da aka saye shi zuwa ga shugabansa:
Babi na Biyu:
Laifin wanda ya yi wa bawansa ko baiwarsa kagen zina:
Babi na Uku:
Bayanin wanda aka rubuta masa biyan fansa da watannin da zai rika biya kowace shekara. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Wadannan da suke neman rubutun fansa daga abin da hannun damarku ke mallaka daga (bayi). Ku rubuta musu in har kun san da wani alheri a cikinsu, kuma ba su cikin dukiyar Allah wadda Ya ba ku (azurtaku da shi)….” (k:24:33). Rauhu ya ce, daga dan Juraij, na ce, wa Adda’u shin wajibi ne a kaina idan na san yana da dukiya in rubuta masa fansa? Ya ce, “Ban tsammaci komai ba face wajibi ne.” Amru dan Dinar ya ce, na ce wa Adda’u cewa: Shin kana da kyakkyawar hujja ce daga wani? Ya ce, “A’a.” Sa’an nan ya ba ni labari cewa: “Lallai Musa dan Anas ya ba shi labari daga Sirin ya taba tambayar Anas rubutun fansa don ya kasance mai yawan dukiya sai (Anas) ya ki. Sai ya tafi (kai kara) zuwa ga Umar (Allah Ya yarda da shi), sai (Umar) ya ce: “Rubuta masa.” sai (Anas) ya ki sai Umar ya buge shi da wata bulala ya karanta masa cewa: “Ku rubuta musu kudin fansa idan kun san akwai alheri a cikinsu (gaskiya da rikon amana….)” (k:24:33). Laisu ya ce, Yunus ya ba ni labari daga dan Shihab ya ce, Urwatu ya ce, “A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Hakika Bariratu ta shiga gare ta wata rana tana neman taimakawarta game da biyan kudin fansarta lokacin da ake bin ta ukiyya biyar kuma an sanya mata lokacin biya a cikin shekara biyar. Sai A’isha ta ce, bisa niyyar biya mata: “Shin kin gani idan na yi musu tattalin biya lokaci daya, sai in saye ki, in ’yanta ki waliccin yaya zai komo (kasance) gare ni? Sai Bariratu ta tafi zuwa ga iyalanta (shugabanninta) ta ba su labari game da haka sai suka ce: “A’a, face dai walicci na gare su.” Sai A’isha ta ce: “Sai na shiga zuwa ga Manzon Allah (SAW) na ba shi labarin haka, sai Manzon Allah (SAW) ya ce, mata: “Ki saye ta, ki ’yanta ta domin lallai waliccin (bawa) yana ga wanda ’yanta.” Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya mike yana cewa: “Me ya samu wadansu jama’a suna gitta sharudda da wasu irin sharuddan da ba su cikin Littafin Allah? Duk wanda ya gitta wani sharadi wanda ba ya cikin Littafin Allah, to sharadin banza ne (batacce ne). Sharadin Allah shi ya fi cancanta kuma ya fi aminci.”
Babi na Hudu:
Sharudan da ke hallatta ga wanda ake rubata masa kudin fansa. Da hukuncin mutumin da ya shardanta sharadin da babu shi cikin Littafin Allah. An karbo haka daga dan Umar.
274. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga dan Shihab daga Urwatu cewa: Lallai A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ba shi labari cewa: Hakika lokacin da Barira ta zo mata tana neman taimakawarta don biyan kudin fansarta wadda ba ta ida biyan komai ciki ba. Sai A’isha ta ce, mata: “Ki koma zuwa ga iyalanki (shugabanninki) idan sun yarda in biya miki kudin fansarki waliccinki ya kasance gare ni, to zan aika ta haka.” Sai Barira ta ambata haka ga shugabanninta suka ki. Sai suka ce, “Idan za ta biya miki bisa cewa, waliccinki na wurinmu to tana iya biya miki. Sai (A’isha) ta ambaci haka ga Manzon Allah (SAW), sai Manzon Allah (SAW) ya ce mata: “Ki saye ta kuma ki ’yantata domin hakika waliccin bawa na ga wanda ya ’yanta shi.” Sai (mai ruwaya) ya ce: “Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya mike ya ce: “Me ya sanya wadansu mutane suna rika gitta sharudda wadnada ba su cikin Littafin Allah? To duk wanda ya gitta wani sharadi wanda ba ya cikin Littafin Allah, to ba ya da wannan hakkin koda ya yi sharadi sau dari ne, hakika sharadin Allah shi ya fi cancanta kuma ya fi aminci.”