Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. Littafin Ijara (Haya):
Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.Littafin Ijara (Haya):Abin da ya shafi ladar kwadago (jinga): Babi na Farko: kwadago (jinga) da mutumin kwarai. Bisa fadin Allah Mazaukaki cewa: “Hakika mafi alherin wanda za ka yi jinga da shi cikin mutane ya zamo mai karfi amintacce… (k:28:26).” […]
Buhari da Muslim
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus
Almashgool, Bauchi
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
Littafin Ijara (Haya):
Abin da ya shafi ladar kwadago (jinga):
Babi na Farko:
kwadago (jinga) da mutumin kwarai. Bisa fadin Allah Mazaukaki cewa: “Hakika mafi alherin wanda za ka yi jinga da shi cikin mutane ya zamo mai karfi amintacce… (k:28:26).” Da bayanin hukuncin mai tsaron taska amintacce da bayanin wanda bai daukar wanda ke da tsananin bukatar aiki.”:
1. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: “Muhammad dan Yusuf ya ba mu labari ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari, daga Abu Burdata ya ce, “Kaka Abu Burdata ya ba ni labari daga Babansa Abu Musal Ash’ari (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (S.A.W) ya ce, “Amintaccen mai tsaron taska wanda yake ba da kyautar abin da aka umarce shi bisa dadin ransa, yana daya daga cikin (wadanda ake rubutawa daga) masu yin sadaka (wato shi da mai dukiya).”
2. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga kurratu dan Khalid ya ba mu labari, ya ce, Humaid dan Hilal ya ba ni labari, ya ce, Abu Burdata ya ba mu labari, daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Na fuskanci (na tafi zuwa ga) Annabi (SAW) da wasu mutum biyu daga kabilar Ash’ariya sai na ce, “Ban san lallai su suna neman aiki ba ne (ma’ana yana son aba su aikin jinga),” sai (Annabi SAW) ya ce, “A’a mu, ba mu ba da aiki (jinga) ga wanda yake tsananin bukatarsa.”
Babi na Biyu: Jingar kiwon tumaki bisa kimar kiradi (daya cikin shida na Dirhami):
3. An karbo daga Ahmad dan Muhammad Almakkiyu ya ce: “Amru dan Yahya ya ba mu labari daga kakansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah bai taba aiko wani Annabi ba, face ya yi kiwon tumaki.” Sahabbai suka ce, “Har da kai? Ya ce, “Na’am, na kasance ina yi wa mutanen Makka kiwo bisa wasu ’yan kiradi (daya bisa shida na Dirhami).”
Babi na Uku: Jinga da mushirikai saboda lalura, ko idan ba a samu Musulmi ba ga wannan bukata. Saboda Annabi (SAW) ya yi jinga da Yahudawan Khaibara:
4. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham ya ba mu labari daga Ma’amar daga Zuhuri daga Urwata dan Zubair daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Annabi (SAW) da Abubakar sun yi jinga da wani mutum daga kabilar Dailu, sa’annan suka yi da wani daga kabilar Abdi dan Addiyu a matsayin jagora. Saboda ya kasance kwararre wajen jagoranci kuma lokacin ya warware rantsuwar jinga da iyalan Asi dan Wa’il. Kuma shi yana bisa addinin kafiran kuraishawa, sai (Annabi da Abubakar) suka amintar da shi suka ba shi abin hawansu (taguwarsu). Suka kulla mahadarsu (wurin haduwarsu) a kogon Sauru a bayan kwana uku. Sai ya cika alkawarinsa ya zo musu da taguwarsu a washegarin yini (dare) na uku, suka haye suka fara tafiya tare da Amir dan Fuhair na yi musu rakiya, Dalil Daili na yi musu jagora. Ya bi da su ta karkashin Makka bisa hanyar gabar teku.”