Da Sunan Allah Mai Rahama Maijinkai.
25. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyata dan Asma’u ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya bayar da jingar (hayar) gonakin Khaibara ga Yahudawa bisa ga su yi aiki su yi noma suna da rabin abin da aka samu daga […]
25. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyata dan Asma’u ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya bayar da jingar (hayar) gonakin Khaibara ga Yahudawa bisa ga su yi aiki su yi noma suna da rabin abin da aka samu daga amfanin gonar.” Kuma lallai dan Umar ya ba shi labari cewa: Lallai gonakin sun kasance ana hayarsu bisa ga wani abu sananne kamar yanda Nafi’u ya ambace shi ban kiyaye shi ba, kuma Rafi’u dan Khadija ya ba da labari cewa: Lallai Annabi (SAW) ya hana game da hayar gona.” Ubaidullahi ya ce, daga Nafi’u daga dan Umar cewa: “Maganar hayar da aka yi da Yahudawa, Umar ya kore su daga baya.”
Da Sunan Allah Mai Rahama Maijinkai.
Babi na Farko:
Hawwala (daukar lamuni na bashi). Shin ana komai a cikin daukar lamunin bashi? Alhasan da kattada sun ce: “Idan a yinin da aka kulla lamunin ne ya kasance da lokaci mai tsawo ya halatta babu warwarewa.” dan Abbas ya ce: “Idan masu tarayya wajen kudin bashi da wanda ke hannu, suka kulla lamunin karbar bashi ga wasu a maimakon rabonsu, wasu kuma suka karbi wanda ke hannu, idan bashin bai karbu ba saboda mutuwar wanda ake bi bashi ko saboda rashin kudin biya ko ya yi musun bashin, to wanda ya karbi kason bashi ba shi da wani hakkin neman wani fansa da abokan tarayyarsa, (saboda haka aka kulla da shi).” Haka ma hukuncin yake ga magada.
26. An karbo daga Abdullahi danYusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Rashin biyan bashi zalunci ne, idan aka bi (yi lamunin bashin) dayanku mai arziki, to lallai ya yarda da haka.”(Ma’anar babu laifi a yi lamunin karbar bashi ta wajen wani wanda zai iya karbo bashi ga mai taurin biyan bashi alhali yana da arziki).”
Babi na Biyu:
Idan aka yi lamunin karbar bashi na mamaci bisa ga wani mutum ya halatta. Haka idan aka yi lamunin karbar bashi daga wajen mai taurin (jinkirin biyan) bashi, bai da ikon kin yarda.”
27. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga dan Zakhwan daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Jinkirin biyan bashi zalunci ne, wanda duk aka yi lamunin karbar bashi daga mai jinkirin biyan bashi lallai ya yarda da haka.”
Babi na Uku: Idan aka yi lamunin karbar bashin mamaci bisa ga wani mutum ya halatta:
28. An karbo daga Almakkiyu dan Ibrahim ya ce: “Yazid dan Abu Ubaida ya ba mu labari daga Salmata dan Ak’wa’i (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance wata rana a wurin Annabi (SAW) sai aka zo da wata gawa sai suka ce: “Ka yi mata Sallah, sai (Annabi) ya ce, “Shin akwai bashin wani a kansa? Suka ce, “A’a, ya ce: “Shin ya bar wani abu? Suka ce, “A’a, sai (Annabi) ya yi mata Sallah. Sa’an nan aka zo da wata jana’iza (gawa) suka ce, “Ya Manzon Allah! Ka yi mata Sallah,” ya ce; “Shin akwai bashin wani a kansa? Sai aka ce, “Na’am, ya ce, ‘Shin ya bar wani abu na dukiya? Suka ce, “Dinari uku ya bari.” Sai ya yi mata Sallah. Sai aka zo da wata jana’iza (gawa) ta uku, suka ce, “Yi mata Sallah (Annabi), ya ce, “Shin ya bar wani abu? Suka ce, “A’a,” ya ce, “Shin akwai bashi a kansa? Suka ce, “Dinari uku ake bin sa.” Ya ce, “Ku yi wa abokinku Sallah.” Sai Abu kattada ya ce, “Yi masa Sallah Ya Manzon Allah! Bashinsa na kaina, sai (Annabi) ya yi masa Sallah.”