Da tsiran sule 10 na fara sai da nama – Umaru Gwama

Malam Umaru Gwama mai tanderu, mai sana’ar sayar da nama a babbar kwatar Maiduguri, ya bayyana yadda ya fara wannan sana’a ta sayar da nama, wacce ta dalilinta ya yi suna a fagen sayar da nama. Umar Gwama ya bayyana cewar tun yana zuwa kwata yana aikin yade yadi a jikin nama, har ta kai […]

Da tsiran sule 10 na fara sai da nama – Umaru Gwama

Malam Umaru Gwama mai tanderu a bakin sana’a

Malam Umaru Gwama mai tanderu, mai sana’ar sayar da nama a babbar kwatar Maiduguri, ya bayyana yadda ya fara wannan sana’a ta sayar da nama, wacce ta dalilinta ya yi suna a fagen sayar da nama.

Umar Gwama ya bayyana cewar tun yana zuwa kwata yana aikin yade yadi a jikin nama, har ta kai ya fara sarar kashi, wanda sannu a hankali ya koma yin aikin babbaka daga nan sai likkafa ta yi gaba, inda ya fara sayen nama na Naira 100 ya fara soka tsire-tsinke daya na sule 10 a wancan lokaci. Ya ce yana gasa naman a nan cikin kwata, ya dauka yana talla.

Sannu a hankali ya samu wuri ya bude tugufarsa, ya fara sayen nama har na Naira dubu kuma Allah cikin ikonSa a kullum naman yakan kare, ba ya kwantai.

A cewarsa: “Bayan wani lokaci na fara yanka da kaina amma ba na saida nama haka. Akan sarrafa shi zuwa tsire, tanderu, kamaniya da dai sauran nau’i na gasa nama.

“Yan shekaru kadan na koma yanka rakumi, domin shi yafi nama da yawa kuma ana sayen shi sosai. Ina cikin haka na sake bude wani wuri na sarrafa nau’in nama da ka ga ake yi a yanzu a nan kwata kuma duk tsawon lokacin nan, ban bar nan cikin kwata ba, a nan na ci gaba da wannan sana’a, har ta kai na zama abin da na zama a yau.”

A gaskiya na yaye yara akalla sama da 30 kuma duk wanda ka gani nan cikin kwata yana wannan sana’a yarona ne, in ban da mutum daya, sannan a yanzu haka ina da yara da muke aiki tare sun fi mutum 20, don a yanzu haka a kullum ina yanka rakumi 10.”

Ya ce sana’ar nama ta yi masa riga da wando: “Ina matukar godiya ga Allah, domin a dalilin wannan sana’a na gina gidaje, na dauki nauyin duk yarana suna karatu, akwai wadanda sun kammala jami’a baya ga wadanda suke makaranta sakandire. Kuma a yanzu akwai uku suna manyan makarantu daban-daban, sai godiyar Allah.”

Sa’annan ya yi kira ga matasan da suka kammala karatu da kar su raina sana’a komai kankantarta. “Ka ga kamar ni, da kadan na fara amma gashi a yau ina alfahari da sana’ar nan, domin ta yi min komai  a rayuwa sai godiya,” inji Umaru Gwama.