‘Da tuyar kosai na dauki nauyin ’ya’yana bakwai’

Wata dattijuwa mai suna Hadiza Aliyu wadda ta kwashe kimanin shekara 28 tana tuyar kosai a kusa da kantin UTC da ke kan Titin Ahmadu Bello a garin Kaduna, ta ce da sana’ar ta dauki nauyin ’ya’yanta bakwai har ta aurar da wadansu.Dattijuwar mai kimanin shekara 72, ’yar asalin Jihar Gombe ta bayyana hakan ne […]

‘Da tuyar kosai na dauki nauyin ’ya’yana bakwai’
‘Da tuyar kosai na dauki nauyin ’ya’yana bakwai’

Wata dattijuwa mai suna Hadiza Aliyu wadda ta kwashe kimanin shekara 28 tana tuyar kosai a kusa da kantin UTC da ke kan Titin Ahmadu Bello a garin Kaduna, ta ce da sana’ar ta dauki nauyin ’ya’yanta bakwai har ta aurar da wadansu.
Dattijuwar mai kimanin shekara 72, ’yar asalin Jihar Gombe ta bayyana hakan ne yayin da take tattaunawa da Aminiya a lokacin da take bakin sana’arta a makon jiya.
Ta ce, “Da wannan sana’ar ni da iyalina muka dogara, kuma ba na sha’awar wata sana’a face ita, saboda babu abin da na rasa a cikinta. Ina samun abin da nakan biya bukatuna na yau da kullum. Kuma ina taimaka wa ’ya’yana bakwai da ’yan uwana, a cikin wannan sana’ar da na yi shekara 28 ina gudanarwa, saboda haka na gode wa Allah Madaukakin sarki”.
Ta ci gaba da cewa: “Mijina ya rasu ya bar ni da marayu a shekarar 1987, amma hakan bai sa na fuskanci wani kalubale ba, saboda yadda na rike wannan sana’ar hannu biyu-biyu. Ba irin sana’ar da ban yi ba, amma ba wadda na dade a cikinta kamar wannan.
“A gaskiya babu wani kalubale da zan ce na taba fuskanta daga wannan sana’ar, sai dai abubuwan da ba za a rasa ba. Da farko ina yin koko da kosai ne kafin yanzu da girma ya fara kama ni, inda na rage wa kaina aiki na koma yin kosai kadai. A da a kullum nake gudanar da sana’ar sabanin yanzu da nake gudanarwa daga Litinin zuwa Juma’a saboda na samu damar gudanar da ayyukana na gida da kuma samun lokacin ziyarar ’yan uwa da abokan arziki,” inji ta.
Dangane da fa’idar da ta samu daga sana’ar sai ta ce: “Na samu alheri sosai albarkacin tuyar kosai. Da sana’ar na rike kaina bayan mutuwar mai gidana, na aurar da ’ya’yana kuma a yanzu nake ci gaba da kara taimaka musu hade da jikokina da sauran ’yan uwa da abokan arziki. Kuma ba ni da wani buri da ya wuce fatan cikawa da imani,” inji ta.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya