Da wacce ’yan Arewa za su tunkari taron kasa?

Tun daga lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa wani kwamitin mutum 13 don share fage da kuma kwaba kullun irin wainar da za a toya a wajen taron kasa sai aka tabbatar da cewa da gaske yake yi, mutanen kudancin kasar nan kuma suka shiga cewa ai abin na yi ne.  Kafin sauran talakawan […]

Da wacce ’yan Arewa za su tunkari taron kasa?
Da wacce ’yan Arewa za su tunkari taron kasa?

Tun daga lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa wani kwamitin mutum 13 don share fage da kuma kwaba kullun irin wainar da za a toya a wajen taron kasa sai aka tabbatar da cewa da gaske yake yi, mutanen kudancin kasar nan kuma suka shiga cewa ai abin na yi ne.  Kafin sauran talakawan Najeriya su farga game da inda aka dosa, har ‘yan kudu sun fara yi wa ‘yan Arewa yarfe, suna kuma shafa masu kashin kaji, suna cewa ba su bukatar wannan taron, domin da ma su ne masu taka birki a dukkan lokutan da aka yunkura don ciyar da ita gaba.
Manufarsu a nan ita ce zuga wasu ‘yan Arewa don su kyamaci wannan taron, ta yadda kawuna da bakunansu za su rarrabu kan matasaya da kuma alkiblar da za su kalla yayin taron, alhali kuwa su ‘yan kudun sun dinke dif, babu wani mai jin kansu.  ’Yan Arewar da ba su fahimci manufar irin wannan taron ba, na fargabar cewa an tsuro da shi ne musamman don a taso da batun korar wasunsu daga kwaryar tarayyar Najeriya kamar yadda ‘yan kudu suka gwada a watan Afrilun 1990, sa’ilin da suka nemi hambarar da wata gwamnatin mulkin soja ta wani dan Arewa.
To koma dai mene ne manufar wannan taron akwai abu guda da ya kamata a yi la’akari game da shi. Wannan kuwa shi ne yadda tun can fil-azal aka haddasa bakar gaba da kiyayya tsakanin al’ummomin Kudanci da Arewacin kasar nan da gangan, aka kuma kasa samo maganinta, ga shi nan har yanzu wadannan masifun na wahalar da kasar, sun kuma sa mun kasa amincewa da juna, muka kasa hada kai, babu kuma  sauran yarda da jituwa tsakanin kabilun kasar, shi ya sa shekaru 53 bayan samun ’yanci muke ta wadari a duhu don neman bakin warwaren zaren matsalolinmu, kuma duk da yawan tarurrukan da muka sha yi, irin wannan da ake son gudanarwa nan gaba, babu wata takamammiyar nasara da aka cimma game da haka. Haka nan kuma a shekarun baya, lokacin da kasar ke karkashin mulkin mallaka,  an sha yin tarurruka bila-adadin, a nan cikin gida da kuma birnin London, don tsara makomarta bayan samun ‘yancinta, kuma hakan ya sa shugabanninmu fahimtar irin bambance-bambancen da ke tsakaninmu, suka kuma kago dabarun mancewa da su ko kuma nakaltar yadda za a biye masu ba tare da sun jawo wata wahalar zamatakewa ko ta mulki ba.
To idan har kokarin da magabatanmu suka  yi yayin tarukkan neman ‘yanci bai kara fadada bambancin da ke tsakaninsu ba, har aka kai ga nasarar samun ‘yancin, me zai sa kuma sai bayan samun ‘yanci ne aka bar wadancan bambamce-bambance suka dauki  wani dogon lokaci suna ta rarraba kawunanmu, muka kasa sarrafa al’amuranmu, cikin sauki, muka yi ta yin abin kunyar da ya zubar da mutuncinmu da na kasarmu?
A lokutan baya shugabannin jihohin Arewa da na Yamma da na Gabas kan tafi taron tsarin kundin mulki, bayan samun ‘yanci ne, inda kowacce tawaga da irin nata manufa ra’ayin daidai da muradin mutanenta, amma kuma ba a gamuwa da rashin fahimta juna, a kuma dawo da manufa guda bayan dukkansu sun amince da juna, ana kuma yin aiki da ita bayan komowa ba tare da wata matsala ba.
Dangane da haka ne shugabannin Najeriya na farko suka fahimci muhimmancin hadin kai muddin suna son cimma burinsu na ‘yantar da kasarsu. Bayan Turawan Ingilishi sun fahimci haka ne, sai kuma suka amince da bukatarsu, aka ba su damar cin gashin gansu. To amma sai ga shi nan bayan samun dabbar da za su gasa sai bambance-bambancen da ke tsakaninsu suka yi kamari, har suka hana su yin haka, daga bisani kuma wannan al’amari ya buwaya, zaman tare yana neman gagara.
Ana sane da irin sakamakon tarurrukan baya da abubuwan da suka raunana su ko wadanda suka hana su yin tasiri har aka kasa yin amfani da su. To an magance su ne a yanzu balle a ce a nemi komawa gidan jiya?  Wai shin ‘yan Arewan da ke dari-dari da wannan taron za su saki jiki, har su tunkare shi da zimmar farfado da martabobin Arewa a fannin hakar ma’adinai da habaka aikin gona da magance dukkan abubuwan da ke sa ‘yan kudu na yi musu hawan kawara, suna wulakanta al’adunsu da dabi’unsu, har ma da  kokarin hana su yin addininsu bisa umurnin Mahaliccinsu? Ya kamata dai a san da wacce Arewa za ta tunkari wannan muhimmin taron?