Da wane ne kake wannan shiri?

Mutane da yawa suna da niyyar yin abubuwa da dama a wannan shekara. Dalilan yin wadannan abubuwa sun bambanta daga wani mutum zuwa wani, daga wata mace zuwa wata. Haka mutum yake. A kullum akwai wani buri da muke so mu cin mawa, amma idan aka duba a hankali kuma muka tambayi kanmu da gaske, […]

Da wane ne kake wannan shiri?
Da wane ne kake wannan shiri?

Mutane da yawa suna da niyyar yin abubuwa da dama a wannan shekara. Dalilan yin wadannan abubuwa sun bambanta daga wani mutum zuwa wani, daga wata mace zuwa wata. Haka mutum yake. A kullum akwai wani buri da muke so mu cin mawa, amma idan aka duba a hankali kuma muka tambayi kanmu da gaske, ko mene ne dalilin da ya sa muke son mu cin ma wannan buri? Yawancin lokaci mutane suna so ne su yi fahariya cewa sun iya yin wani abu ta wurin kokarinsu ko ta wurin gwanintarsu; duk wannan mai yiwuwa ne, amma tambayar ita ce – a ina ne Allah Yake cikin wannan shiri da kake yi a yau? 

Akwai manufofi daban-daban a cikin tunanin mutane, musamman game da wannan shekara; ga wadansu, suna ganin dole ne su ci gaba da yin mulki; ga wadansu kuwa, suna gani dole ne su karbi mulki daga hannun wadanda suke kan shugabanci a yanzu; wadansu suna ganin cewa cikin wannan shekara; dole ne su cin ma burinsu na zama manyan ’yan kasuwa da suke da babban jari, wadansu kuwa suna cewa wannan shekara, zan gina gida, ko zan yi aure, ko zan je kasar waje da dai sauransu. Ko ma mene ne muradin zuciyarka cikin wannan shekara, dole ne ka tambayi kanka ko kanki mene ne kuma nufin Allah game da rayuwarmu cikin wannan shekara? Mu tuna akwai mutane da yawa wadanda suka yi shiri sosai domin su yi wani abu da watakila zai kyauta ta musu rayuwarsu na duniya; amma a yau ba sa cikin wannan duniya, sun rigaya sun kwanta dama; burinsu ya kare ke nan. Bari in tambaye ka mana; kai din; wani irin abu mai kyau ne ka yi wa Allahda ya sa Shi Allah Ya bar ka cikin masu rai a yau? Gaskiyar ita ce, babu! Ba mu fi wadanda suka rigaye mu ba ko kadan, lokacinmu ne kawai bai yi ba. Kowane mai bin Yesu Kiristi na gaske zai dauki lokaci ne gaban Ubangiji Allah cikin addu’a mai yiwuwa har azumi domin su fahimci manufar Allah game da rayuwarsu cikin wannan shekara. Maganar Allah na yi ma kowa wannan gargadin cewa: “Tafi, ku da kuke cewa, ko yau ko gobe za mu tafi cikin wannan birni, shekara a wurin, mu yi ciniki, mu ci riba, ku kuwa ba ku san abin da za ya faru gobe ba, wane irin abu ne ranku? Tururi ne ku, abin da yakan bayyana kadan, kana ya watse. Da ma kun ce, Idan Ubangiji Ya yarda, za mu yi rai mu yi abu kaza da kaza. Amma yanzu kuna fahariya cikin alwashinku: irin fahariyar nan duka mugu ne.” (Yakub 4 :13–15). Ubangiji Allah a koyaushe yana fadakar da mu a kan cewa ran mutum ba komai ba ne, ya kwatanta ran mutum da tururi, abu guda da tururi shi ne da wuya ka ga yana tashi haka nan kuma nan take yana bacewa. Wannan tuni ne ga kowane dan Adam; cewa Allah bai halici mutum domin ya dauwama a cikin wannan duniya ba; dole ne akwai ranar mutuwa; kuma babu wanda ya san nasa ranar. Kowa akwai nasa iyaka. Idan kuwa haka gaskiya ne, to mene ne ya sa jama’a suna rayuwarsu kamar su suke da iko bisa nasu ran? A cikin dukan shirye-shiryenka na wannan shekara, wane ne madogaranka? Mutane da dama suna gani domin kudin da suke da shi, za su iya yin komai da suke da damar yi, sun manta cewa kudi ba ya iya sayen rai; da dama suna gani iyayensu a yau su ne a matsayin manya a cikin jiharsu ko kuwa mu ce cikin wannan kasa, sun manta cewa iyayen nasu su ma; ta kansu suke yi, idan lokacinsu ya yi, su ma dole ne su fuskanci nasu lokacin. Idan rayuwar mutum kamar tururi ne mene ne ya sa ba mu yin koyi da wannan? Mu sani cewa babu abin da zai yi nasara cikin wannan rayuwa idan ba tare da ikon Ubangiji Allah ba. Watakila ka ce mene ne ya sa wadansu masu mugunta suke cin nasara cikin duk abin da suke yi? Ba kai ka soma irin wannan tambayar ba; mutane da dama sun yi wannan tambaya! A cikin Littafin Zabura 73:1–17, Maganar Allah tana cewa: “Hakika Allah Mai alheri ne ga Isra’ila, Ga irin wadanda suke da tsabtar zuciya. Amma ni dai kafafuna sun kusa su zame, saura kadan takawata ta yi talalabiya. Gama na ji kishin zuci ga masu girman kai, sa’anda na ga arzikin masu mugunta, Gama a cikin mutuwarsu babu mirkaki: karfinsu yana cike. Ba su cikin wahala kamar sauran mutane; Ba a yi masu masibu kamar sauran mutane ba. Domin wannan girman kai yana rataye a wuyansu kamar murjani; Suna yafe da zalumci kamar tufa. Idanunsu sun zazzare don kiba, Samunsu ya fi abin da zuciya ke guri, suna ba’a, cikin mugunta kuma suna furta zalunci: Suna yin fankama. Sun kafa bakinsu a sama, harshensu kuwa yana yawo a kasa. Domin haka mutanensa suna komowa nan; Suna kuwa tatsan ruwan da ya cika koko. Sukan ce, kaka Allah Ya sani? Da wani sani kuma a wurin madaukakin? Ga shi, wadannan su ne masu mugunta, kuma, da shi ke suna zaune a huce tutur, suna karuwa da wadata. Gaskiya, banza na tsarkake zuciyata, na wanke hannuwana da rashin laifi; gama duk yini, masifa nake sha, da horo kuma kowace safiya. Da na ce, haka zan fadi; Ga shi, da na yaudari tsara ta yayanka. Sa’anda na nemi yadda zan gane wannan, Sai na zama mai ciwo ainun; sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah, Na lura da matukarsu.”
Ba za mu iya gane mutum cikakke ba, sai Shi Allah da kanSa Wanda Ya san ko mene ne yake tafe cikin zuciyar mutum. Amma kai dan uwana, wane shiri kake da shi domin wannan shekara? Allah Yana cikin wannan shiri ko kuwa ka rigaya ka ware Shi a gefe? Babban kuskure ga dukan masu bin Yesu Kiristi su yi guri, ko ya shiya yin wani abu ba tare da neman nufin Ubangiji Allah ba; mu tuna fa cewa komai wadatarmu, komai ikon da muke gani muna da shi, komai iliminmu, ba za mu iya kare ranmu daga hannun Shi Allah Wanda Yake rike da ikon dauke rai a lokacin da Ya ga dama ba; ashe kuwa, dole ne mu kawo shi cikin duk abin da muka sa a gaba domin mu aiwatar idan muna so mu ci nasara. Mu ci gaba da addu’a domin wannan kasa, bari Ubangiji Allah Ya cire gaba tsakanin al’ummar wannan kasa. Mu kuma roki Ubangiji Allah Ya yi mana jinkai Ya yaye mana wannan kalubalen tashin hakali da ya ki ci, ya ki cinyewa. Allah Ya ci gaba da tsare kowane dayanmu daga hannun masu mugunta, amin.