‘Da wuya a iya kawo karshen Ebola a nan kusa’

Majalisar dinkin Duniya ta ce da wuya a iya kawo karshen cutar Ebola a ranar 1 ga watan gobe kamar yadda aka yi  hasashe tun farko, saboda yadda cutar take ci gaba da yaduwa a kasar Saliyo da sauran wurare.Kwamitin Magance Yaduwar Cutar Ebola na Majalisar dinkin Duniya ya ce a watan Satumbar da ya […]

‘Da wuya a iya kawo karshen Ebola a nan kusa’
‘Da wuya a iya kawo karshen Ebola a nan kusa’

Majalisar dinkin Duniya ta ce da wuya a iya kawo karshen cutar Ebola a ranar 1 ga watan gobe kamar yadda aka yi  hasashe tun farko, saboda yadda cutar take ci gaba da yaduwa a kasar Saliyo da sauran wurare.
Kwamitin Magance Yaduwar Cutar Ebola na Majalisar dinkin Duniya ya ce a watan Satumbar da ya wuce, an yi hasashen cewa za a iya ganin bayan cutar kafin ranar 1 ga watan Disamba. Amma a ranar Litinin da ta gabata shugaban kwamitin Anthony Banbury ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa za a wuce ranar da aka yi hasashe a wasu yankuna. Amma kuma akwai tabbacin cewa annobar za ta ja baya a wasu yankunan. Mista Banbury ya ce wuraren da hankula suka kamata su karkata su ne yankunan karkarar kasar Saliyo da birnin Makeni da ke tsakiyar kasar da kuma garin Port Loko da ke arewa-maso-yammacin kasar.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce wannan ce annobar Ebola mafi muni a tarihi, inda mutum 5,459  suka rasa rayukansu cikin mutum 15,351 da suka harbu da kwayar cutar a kasashe takwas kafin ranar 18 ga wannan watan. Kuma kasashen da annobar tafi kamari su ne Guinea da Saliyo da Laberiya.