Da wuya Drogba ya buga wasan Arsenal da Chelsea a jibi

Saboda raunin da Didier Drogba dan kwallon Chelsea da ke Ingila ya samu a wasansu da Manchester United a ranar Asabar da ta wuce, da wuya dan kwallon ya buga wasan da za su yi da kulob din Arsenal a jibi Lahadi. Drogba dai ya buga wasa na minti 90 a wasansu da United inda […]

Da wuya Drogba ya buga wasan Arsenal da Chelsea a jibi
Da wuya Drogba ya buga wasan Arsenal da Chelsea a jibi

Saboda raunin da Didier Drogba dan kwallon Chelsea da ke Ingila ya samu a wasansu da Manchester United a ranar Asabar da ta wuce, da wuya dan kwallon ya buga wasan da za su yi da kulob din Arsenal a jibi Lahadi.

Drogba dai ya buga wasa na minti 90 a wasansu da United inda Chelsea ta samu nasara da ci 1-0.
dan kwallon ya samu rauni ne a idon kafa a wasan, da hakan ta sa Likitocin kulob din suke ganin da wuya dan kwallon ya murmure har ya buga wasansu da na Arsenal a gasar firimiya ta Ingila a jibi Lahadi.
Kocin Chelsea Jose Mourinho ya yi amfani da Drogba ne a wasannin da kulob din ya yi da kPR da kuma na Manchester United saboda raunukan da ’yan kwallon gabansu Diego Coasta da kuma Loic Remy suka ji.
A da kocin ya yi niyyar dawo da Diego Costa fagen daga ne idan wasannin gasar firimiya suka rage hudu amma dole ya canza shawara a yanzu saboda raunin Drogba.