Da ya sayar da mahaifiyarsa mai kusumbi kan Naira miliyan 7 ga matsafa

Yanzu haka ’yan sanda a Jihar Ondo sun dukufa wajen neman wani matashi da ake zargin ya sayar da mahaifiyarsa mai kusumbi a kan Naira miliyan 7. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo Mista Femi Joseph ya tabbatar da sace matar mai suna Rukayat Abodunde mai shekara 60 da ke da kusumbi a bayanta. Wata […]

Da ya sayar da mahaifiyarsa mai kusumbi kan Naira miliyan 7 ga matsafa
Da ya sayar da mahaifiyarsa mai kusumbi kan Naira miliyan 7 ga matsafa

Yanzu haka ’yan sanda a Jihar Ondo sun dukufa wajen neman wani matashi da ake zargin ya sayar da mahaifiyarsa mai kusumbi a kan Naira miliyan 7.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo Mista Femi Joseph ya tabbatar da sace matar mai suna Rukayat Abodunde mai shekara 60 da ke da kusumbi a bayanta.

Wata majiya ta kusa da matar ta shaida wa ’yan jarida cewa, da misalin karfe 10 na dare ne wadansu mutum biyu suka ziyarci gidan matar da ke Titin Ayetoro a garin Ondo da nufin sayen kifi a  wurinta, amma sai suka yi ta harba bindiga a sama wanda hakan ya sa makwabta suka gudu.

“A daidai lokacin ne ’yan  bindigar suka sace matar suka tafi da ita cikin wata motar da ke jiransu a kofar gida,” inji majiyar wacce ta ce nan take aka sanar da ofishin ’yan sanda wadanda suka zo gidan domin bincike a lokacin.

Majiyar ta ce bayan ’yan kwanaki da aukuwar lamarin ne ’yan bindigar suka sake dawowa neman matashi kan ya mayar masu da kudinsu Naira miliyan 7 bisa zargin cewa kusumbin da suka cire daga jikin matar bai yi aikin tsafin da suke bukata ba, inda suka yi barazanar hallaka matashin idan ya ki mayar musu da kudinsu. Majiyar ta ce, matashin wanda ya fara taba kudin yana fannin sayen kyawawan suturu ga mahaifiyarsa kafin a kashe ta da gyara gidansu ya shaida wa ’yan bindigar cewa zai iya mayar musu kudin ne idan suka dawo masa da mahaifiyarsa a raye.

Da yake karin haske a kan lamarin, Kakakin ’Yan sanda Femi Joseph ya ce abin bakin cikin shi ne a daidai lokacin da ’yan sanda suka je gidan domin samun bayanan da za su ba su damar ceto matar, dangi sun ki ba su cikakken bayanin da zai taimaka musu wajen gudanar da aikinsu. Ya ce, a daidai lokacin wadansu daga dangin matar suke ziyartar ofishin ’yan sandan da bukatar janye wannan matsala daga hannun ’yan sanda inda suka ce, za su yi amfani da hanyar gargajiya domin shawo kan lamarin.

Kakakin ya tabbatar da cewa za su ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Yanzu haka dai matashin ya boye kansa a wani wuri da ba a sani ba kuma ’yan sanda sun ce za su yi duk abin da suke iyawa wajen gano ’yan bindigar da wannan matashi.