Da yaran Kudu aka sace…
A kwanakin da suka gabata ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ceto wadansu yara da aka sace aka raba su da mahaifansu daga birnin Kano zuwa Jihar Anambra da ke kudancin kasar nan. A yadda labarin ya fito yaran an sace su ne tun kusan shekarar 2014. Wadannan yara dai mafi yawansu ana sace su […]
A kwanakin da suka gabata ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ceto wadansu yara da aka sace aka raba su da mahaifansu daga birnin Kano zuwa Jihar Anambra da ke kudancin kasar nan. A yadda labarin ya fito yaran an sace su ne tun kusan shekarar 2014. Wadannan yara dai mafi yawansu ana sace su ne yayin da suka fito daga gida zuwa makarantun Islamiyya ko a kan haryarsu ta dawowa. Mafiya yawan yaran da ake sacewar kuma ba su haura shekara biyar zuwa shida da haihuwa ba.
A ’yan shekarun baya kafin dubun wadannan barayin yara ta cika, duk lokacin da yaro ya bata aka kuma rasa shi sai ake zargin cewa ’yan kungiyar asiri ne ke sace yaran. Ashe ba haka lamarin yake ba, domin gara ma sata ta ’yan kungiyar asiri da sata irin ta wadannan barayin domin kuwa su ’yan kungiyar asiri idan har suka samu nasarar sace mutum suna raba shi da duniyar ce baki daya, yayin da su kuma wadannan barayin sukan yi wa yaran kisan mummuke ne wanda da shi gara mutuwa domin kuwa su sukan raba mutum ne da iyayensa, addininsa da kuma kabilarsa wanda wannan ba karamar hasara ba ce musamman ma ta raba mutum da addininsa na Muslunci. Lallai babu wata asara da ta fi a ce mutum ya taso ba ya bautar Allah (SWT). Alhamdulillahi tunda yanzu asirinsu ya fara tonuwa an samu yara tara daga cikin 47 da aka ce sun bata ko an sace.
Saura da me kuma? Bayan bayyanar wadannan yara, muna so Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su kara matsa lamba da bincikar wadanda aka samu yaran nan a wurinsu domin kuwa mu al’ummar Arewa muna zarginsu a kan wadancan din ma suna wurinsu dogaro da abin da daya daga cikin yaran mai suna Faruk ya ba da labari ga ’yan jarida cewa ya sha ganin Madam Ebere tana sayen yara a gabansa. Ke nan ba iya wadannan da aka samu ne suka sata ba, don haka a bincike su sosai har sai sun fito da sauran yaran sannan a yanke musu hukunci mai tsanani lura da irin mummunan ayyukansu na cin amana da suka yi wa mutanen Arewa musamman na Kano wurin da suke da zama.
Ina da yakinin cewa da a ce yaran Kudu ne ake sacewa ake kawo su Arewa kuma asiri ya tonu, da tuni duk duniya ta san abin da ake ciki ta hanyar kwarmata lamarin a kafafen labarai da na sada zumunta saboda sun maida ’ya’yansu ne kawai ’ya’ya.
Idan ban manta ba akwai wata shekara da wani dan Arewa daga Jihar Neja da ke zaune a Kudu (na manta jihar da yake zaune) suke soyayya da wata yarinya amma a gidan su yarinyar aka ki yarda ta aure shi karshe yarinyar ta biyo shi Arewa aka daura musu aure a fadar Mai martaba Sarkin Bidda, iyayenta da sauran al’ummar Kudu suka kafe kan cewa sato ta ya yi suka yi ta yayata abin a kafafen labarai na zamani. Ba su rabu da shi ba har sai da suka kai shi kotu aka daure shi sannan hankalinsu ya kwanta. Ga kuma labarin Yunusa Yalo dan Jihar Kano da ke zaune a Bayelsa har yanzu yana tsare a kurkuku saboda yana soyayya da wata yarinya ya taho gida ta biyo shi har suka yi aure, shi ne suka yi ta yayata maganar a kafafen labarai kai ka ce yara dubu ya dauko.
Amma mu ’yan Arewa saboda sakaci irin namu da rashin hadin kai da kuma nuna halin ko-in-kula, lokacin da ake labarin batar yaran sai kowa ya yi shiru kai hatta jami’an tsaro banzatar da maganar suka yi ba don Allah Ya sa an samu wani hazikin dan jarida daga Arewa ba wato Ahmad Isah mai gidan rediyon Human Right da ke Abuja ba, to ina ga da sai dai zancen yaran ma ya bi iska.
Me yake damunmu ne al’ummar Arewa? Sai yaushe za mu farka daga dogon barcin da muke yi mu dawo mu zama tsintsiya madaurinki daya? Ina kira ga ’yan Arewa musamman sarakunanmu da lauyoyinmu da kada su zuba ido wannan magana ta tafi a iska don Allah ku tsaya tsayin daka har sai an yi wa wadannan barayi tsattsauran hukunci da wani ma ba zai sha’awar aikata makamancin laifin ba.
Ina kuma kara yin kira ga kungiyoyinmu na shiyyoyi da na addinai da kungiyar kare hakkin Musulmi da ACF ta kare muradun Arewa da sauransu don Allah a kara kaimi wajen ganin an hukunta wadannan mutane. Iyaye kuma sai a kara kula da yara. A karshe ina fatar alheri ga lauyoyinmu da suka kafa kungiyar “Justice for 47” don ceto da ganin an bi wa yaran hakkinsu, Allah Ya saka muku da mafificin alheri Ya kuma kare mu da yaranmu daga sharrin masharranta.
K. Bello Kiyawa
(0703-252-8895)
kbellokiyawa93@gmail