Da yardar Allah zaman lafiya ya dawo ke nan a Jos – Shugaban Dattawan Berom
Shugaban Dattawan kabilar Berom na karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Mista Ibrahim Choji ya ce in Allah Ya yarda zaman lafiya ya dawo ke nan a garin Jos da Jihar Filato baki daya. Mista Ibrahim Choji ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron zaman lafiya da kyautata […]
Shugaban Dattawan kabilar Berom na karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Mista Ibrahim Choji ya ce in Allah Ya yarda zaman lafiya ya dawo ke nan a garin Jos da Jihar Filato baki daya.
Mista Ibrahim Choji ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron zaman lafiya da kyautata danganataka da kungiyar Sakkwatawa da Zamfarawa da Kabawa mazauna Jihar Filato ta shirya a tsakanin ’ya’yan kungiyar da kabilun Berom da Anaguta a garin Jos.
Ya ce “Babu shakka zaman lafiyar nan da aka samu kowannenmu yana jin dadinsa, don haka mu yi kokari mu rungumi junanmu mu mance da abubuwan da suka faru a baya don dorewar wannan zaman lafiya.”
Ya ce “Mu iyaye mu rika gaya wa ’ya’yanmu gaskiya ta fannin addini da zamantakewa, su kuma matasa su ji abubuwan da iyaye suke fada musu na gaskiya, idan muka yi haka zaman lafiyar da muka samu zai dore.”
Mista Choji ya yaba wa kungiyar kan kira wannan taro da ya ce irin wadannan tarurruka suna matukar karfafa musu gwiwa kan zaman lafiya a jihar.
A jawabin Dagacin Unguwar Kongo Rusha da ke Jos kuma jagoran kabilar Anaguta a wurin taron Mista Bala Auta Agada ya ce “A gaskiya mun ji dadin wannan zama, saboda zai sanya a rika shiga juna.
Ya ce bayan rikice-rikicen da aka samu a jihar, kowa tsoro ya shiga jikinsa, amma yanzu kowa ya saki jikinsa.
Tun farko a jawabin Shugaban kungiyar Sakkwatawa da Zamfarawa da Kabawa mazauna Jihar Filato Alhaji Ahmad Muhammad Bagobiri ya ce sun kira taron ne don su kara sada zumunci tsakanin Kirista da Musulmi dangane da zaman lafiyar da aka samu a jihar.
Ya ce a shekarun baya an samu rikice-rikice a jihar da suka yi sanadin dan wata kabila ba ya zuwa wani wurin da wata kabila ta fi yawa. “Amma a yanzu kowane lungu a Jihar Filato, musamman a garin Jos ana shiga, ana mu’amula mutane suna harkoki yadda ya kamata,wannan abu ya yi mana dadi kwarai da gaske,” inji shi.
Alhaji Bagobiri ya ce babban burinsu shi ne su ga zaman lafiyar da aka samu ya ci gaba da dorewa “Rikice-rikicen da aka yi a baya a jihar nan, sun cutar da kowa babu wanda ya ci riba tsakanin Musulmi da Kirista. Don haka ina kira ga al’ummar jihar nan su rungumi juna su manta da abubuwan da suka faru a baya su zauna da junansu lafiya,” inji shi.