‘Da yatsun kafa nake komai, hannuwana ba sa aiki’

Maganar da Hausawa ke cewa babu nakasasshe sai kasasshe ta fito fili a rayuwar Hajiya Abu Dikko, wacce duk da nakasar da Allah Ya halicce ta da ita ta rashin hannu da kafa bai sa ta zauna ta dogara da ‘yan uwanta ko kuma ta bi layin mabarata ba, maimakon haka sai ta shiga sana’o’i […]

‘Da yatsun kafa nake komai, hannuwana ba sa aiki’

 Tana kunna risho. Maganar da Hausawa ke cewa babu nakasasshe sai kasasshe ta fito fili a rayuwar Hajiya Abu Dikko, wacce duk da nakasar da Allah Ya halicce ta da ita ta rashin hannu da kafa bai sa ta zauna ta dogara da ‘yan uwanta ko kuma ta bi layin mabarata ba, maimakon haka sai ta shiga sana’o’i daban-daban.
Hajiya Abu wacce a yanzu ta kai shekaru hamsin da biyar da haihuwa, da a halin yanzu take zaune a gidanta da ke kofar dan’agundi cikin birnin Kano, kamar kowane dan Adam da Allah Ya halitta, tana da hannaye da kafafuwa guda bibbiyu, sai dai nata hannayen ba sa aiki gaba daya, sakamakon shanyewa da suka yi. Haka kuma kafafuwanta ba su takuwa.

kafafuwanta ke aikin da hannu zai yi mata
Sai dai wata baiwa da Allah Ya yi wa wannan baiwar Allah ita ce duk  da cewa ba ta iya tafiya da kafafuwan nata, amma kafafuwan nata sukan yi mata dukkanin amfanin da hannu zai yi mata.
Mutum  zai yi mamakin irin yadda wannan mata take gudanar da rayuwarta ta yau da kullum, ganin cewa dukkanin hannayenta ba sa amfani.  Takan yi girki da wanka da wanki da wanke-wanke da kwalliya da sanya tufafi ta hanyar amfani da kafafuwanta.  Yadda take sarrafa kafafuwanta dan bambancin kadan ne da hannaye, domin su kansu kafafuwan yau da gobe ta sa sun tankwara, saboda yawan amfani da take yi da su.
 A cewarta, dukkanin ayyukan cikin gida babu abin da ke gagararta sai shanya, idan ta yi wanki takan nemi taimakon na kusa da ita su yi mata shanya.
 Hajiya Abu tana duba mudubiWakiliyar Aminiya ganau ce game da yadda Hajiya Abu ke yin amfani da kafafuwanta ta girka ruwa. Tun daga kan kyasta ashana inda ta jefa a cikin rishon tare da murda injin rishon don karo wutarsa. Sannan ta sake amfani da kafarta ta dauko tukunya ta dora a kai ta sa murfi ta rufe.
Haka kuma Hajiyar ta yi amfani da kafafuwanta ta yi wa fuskarta kwalliya, inda ta shafa hoda ta rike mudubi a tsakankanun yatsun kafarta ta hagu. Sai kuma ta dauki hankici da kafar dama ta dangwalo hoda ta sunkuyo da fuskarta kan kafafuwan nata ta shafa mata hoda tare da gyaggyarawa har sai da komai ya yi daidai, sannan ta karasa kwalliyarta da shafa janbaki da jagira.
Aminiya ta nemi sanin shin ko ta samu wani horo ne game da yadda take amfani da kafarta a madadin hannunta tun tana karama? Sai Hajiyar  ta ce, “Babu wanda ya koya min yadda zan sarrafa kafafuwana, ikon Allah ne kawai. Haka kawai na tashi na samu kaina ina sarrafa kafafuwan yadda suke yi min amfani kamar yadda hannuwa suke yi. Sai dai zan iya cewa a kullum nakan samu karin gogewa tare da dabarun yadda zan aikata wani aikin. Idan yau na yi kuskure to gobe zan yi tunanin yaya zan bullo wa aikin, sai kuma ka ga na samu nasara. Cikin ikon Allah babu aikin da ba na iya yi wa kaina, shanyar kayan wanki ce kawai ba na iya yi. Ita ma don saboda a tsaye ne ake yi. Idan na yi wanki nakan nemi taimakon na kusa da ni su yi min shanyar.”

Haka aka haife ta da nakasa
Hajiyar wacce ta ce ta yi aure har da samun rabon ‘ya mace, daga bisani Allah Ya yi mata rasuwa,  ta bayyana wa Aminiya cewa ba ciwo ko hadari ne ya yi sanadiyyar samun kanta a halin da take ciki ba, iyayenta sun shaida mata cewa haka aka haife ta: “Haka aka haife ni a cikin wanann yanayin, iyayena sun gaya min cewa da farko lokacin ina karama ko zama ba na iya yi da mazaunaina, sai dai da bayana, amma a hankali, a hankali na fara iya zama kamar yadda kowa ke yi, sai dai ba na iya tafiya sai dai na ja jikina ko kuma na yi amfani da keken guragu.” Inji ta.

Sana’ar da take yi
Hajiya tana dinka HulaBaiwar Hajiya Abu ba ta tsaya kawai a ayyukan gida ba, ta kasance takan yi amfani da kafafuwanta wajen gudanar da sana’o’i daban daban. Ta bayyana cewa kafin girma ya saukar mata  takan yi sana’ar dinkin hula da saka, a wancan lokacin takan hada hular zanna bukar guda daya a tsawon makonni biyu . Idan sun taru sai ta kai wa wani kawunta inda shi kuma yake kai wa Kasuwar Kurmi yana sayar mata da su: “Ada lokacin da kuruciya, na yi dinkin hula da saka sosai. Yanzu ma girma ne ya hana ni, saboda yanzu da kyar nake iya sanya allura da kaina saboda matsalar idanu.
Da Aminiya ta tambaye ta yadda take sarrafa kudin da take samu daga sana’arta, ta bayyana cewa takan sayi duk abin da take so da kudinta, haka kuma takan yi zumunci da su: “Kasancewar ni ba na son zama haka kawai, ko na dogara da wani, ko kuma na je na yi bara shi ya sa na kama sana’ata, babu shakka kuma wanann sana’a tawa ta rufa min asiri. Nakan iya tunawa a wancan lokacin nakan yi amfani da kudin da nake samu daga sana’ata na biya wa kaina bukatuna na kuma yi harkar zumunci da sauran kudin.”
Hajiya Abu dai ta bayyana cewa ba ta taba samun wani tallafi daga gwamnati ba sai dai alkawurra wadanda suka gagara cikawa: “Ban taba samin wani tallafi daga gwamnati ba, asali ma ko dan tallafin da ake cewa gwamnatin Jihar Kano na bayarwa ga nakasassu ban taba samu ba. Sai dai zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnati cewa ta taimake ni, musamman yanzu da nake zaune wuri daya ba na yin sana’a” Inji ta. Da yake yi wa Aminiya karin haske game da rayuwar wanann baiwar Allah, Jamilu Madaki wanda  Akanta ne a wata ma’aikata da ke Jihar Kaduna, kuma da ne ga Hajiya Abu, ya bayyana cewa, duk da Alalh Ya yi wa gwaggon nasa nakasa a halittarta amma ba ta yarda yanayin da take ciki ya sa ta zama nakasasshiya a zuci ba; ta yarda ta rika gudanar da sana’o’i don ta biya bukatun kanta da kuma na ‘yan uwa.
Tana bude kayan kwalliya“Ba wai batun ta kai kuka wurin wani ya biya mata bukata ba, hatta ta bangaren  zumuncin ‘yan uwa ba ta yarda ta zama Allah-sarki ba, domin a duk lokacin da wata hidimar ‘yan uwa ta taso takan yi iya kokarinta ko kuma ma ta yi abin da masu lafiyar ba za su  iya yi ba wajen gamin ta yi abin da ya kamata da dan abin da take samu daga sana’arta. Idan aka ce an yi haihuwa kuwa  to ita ke daukar nauyin kayan yaji, idan kuma batun aure ne har kayan lefe take yi.  Ko ni a aurena ta bayar da gudummawa mai tsoka a abin da ya shafi harkar lefe da sauran hidimar auren. Ba wai a nan wannan baiwar Allah ta tsaya ba, hatta harkar karatuna ta taimaka min sosai wajen ganin na zama abin da na zama a yau.’’