‘Da yatsun kafa nake komi ba ni da hannuwa’
Wani matashi mai suna Ibrahim Amadu, dan kimanin shekaru 27 a duniya, ya ce duk da lalurar da yake fama da ita ta rashin hannaye biyu yakan iya yin abubuwan da masu hannu ke yi da yatsun kafarsa.Ibrahim Amadu, wanda dan asalin kauyen Kargo ne da ke cikin karamar Hukumar Sumaila ta jihar Kano da […]

Wani matashi mai suna Ibrahim Amadu, dan kimanin shekaru 27 a duniya, ya ce duk da lalurar da yake fama da ita ta rashin hannaye biyu yakan iya yin abubuwan da masu hannu ke yi da yatsun kafarsa.
Ibrahim Amadu, wanda dan asalin kauyen Kargo ne da ke cikin karamar Hukumar Sumaila ta jihar Kano da ke yawon bara a jihar Legas, ya shaida wa Aminiya cewa da yatsun kafarsa yake yin komai.
‘Ka ganni ba abin da ba na iya yi da yatsun kafata. Ina kirga kudi da su, ina ma’amala da wayar salula, don ina iya buga waya ina kuma iya amsawa. Ina yin garegare na yara da motar kara ta yaran kauye. Kuma da kaina nake gyaran janaretona idan ya samu matsala, ina sanya kaya. Ina yin abubuwa da yawa ba tare da an taimaka mini ba’. In ji shi
Sai dai kuma ya bayyana cewa, ‘Akwai abubuwan da ba zan iya yi da kaina ba sai an taimaka mini, kamar wanka da wanke bahaya, wani lokaci ma sanya kaya yana yi mini wahala sai an taimaka mini. Ka san yadda rayuwa take ko wanda yake da hannaye biyu ma ba komai yake iya yi da kansa ba, wata rana sai ya nemi taimakon jama’a a wani abu. Ni gaskiya na gode wa Allah da Ya ba ni damar yin wadansu abubuwa da yatsun kafa ta, ina fatan Allah Ya yi mini sakayya da gidan aljanna sakamakon wannan lalura da Allah Ya dora mini.’
Ya ci gaba da bayyanin cewa haka Allah ya halicce shi babu hannuwa biyu, amma lafiyarsa kalau, don har matar aure yake da ita a garinsu.
Ya ce dole ce ta sanya yake barace-barace a kan titin Legas don ba shi da jarin da zai gudanar da harkar kasuwanci.
Ibrahim ya kara da cewa, zai daina yawon bara a Legas idan da zai samun tallafi daga ’yan siyasa da gwamnatoci.
‘Har wajen dan majalisarmu na je mai suna Kawu Sumaila don ya taimaka mini ya ba ni jari na bude shagon sayar da kaya amma sai ya ce na je garinmu na samu Sani Ahmed, da na je wurin Sani ban samu komai ba, sai kawai na yanke shawarar na zo Legas na cigaba da bara don na samu jarin da zan fara sana’a a Kano. Kuma ko yanzu na samu tallafin jari da zan bude sana’ar saye da sayarwa zan bar bara na koma gida Kano.’ In ji shi.Da Aminiya ta tuntubi dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Sumaila Alhaji Kawu Sumaila bai musanta zargin da Ibrahim ya yi ba. Kawu Sumaila a sakon wayar salula da ya aikowa Aminiya ya bayyana cewa, ‘Gaskiya ne, amma ban sake jin labarinsa ba.’
kanen Ibrahim wanda yake tare da shi a Legas mai suna Yakubu Amadu, dan kimanin shekaru 15 da haihuwa, ya ce ‘al’amarin Ibrahim yana da ban mamaki, domin yana iya yin abubuwan da masu hannu ke yi. Ka ga yana buga kwallo, yana daukar bulala ya daki mutum da ita, yana iya yin gare-gare da motar sille ta yara. Gaskiya yana ba mu mamaki sosai.’