Da ’ya’yana nake zuwa kamfe —Dan takara
Dan takarar ya ce zai kiyaye abubuwan da za su hana zaman lafiya a lokacin zabe.
Dan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar LP, Bashir I. Bashir, ya ce shi da ’ya’yansa yake fita yawon yakin neman zabe.
Dan takarar gwamnan, ya bayyana hakan ne ga Aminiya yayin da wasu ma’aikatan Rukunin Kamfanin ‘Media Trust Groups masu wallafa jaridar Daily Trust, Aminiya da sauransu suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Kano.
- Fulani makiyaya na ficewa daga Taraba saboda yawan kai musu hare-hare
- Fira Ministar New Zealand, Jacinda Ardern, za ta sauka daga mukaminta
“Wannan ya danganta ga kowane dan takara. Misali ni duk inda zan je kamfe ‘ya’yana maza da mata duk suna bi na.
“Ina tunanin ‘yan siyasa masu yunwar dole sai sun yi mulki ne ke daukar nauyin dabar siyasa. Yana da kyau mutane su guji zabar irin wadannan ‘yan siyasa,” in ji shi.
Bashir ya ce zai martaba yarjejeniyar da ta bukace su shi da sauran ‘yan takarar gwamna a jihar da suka sanya hannu kan dokar zaman lafiya.
Sannan ya roki jami’an tsaro da su hana duk dan takarar da aka same shi da goyon bayan mabiyansa wajen tayar da tarzoma yayin yakin neman zabe a jihar.
Kazalika, ya ce don tabbatar da zaman lafiya ya dore a yayin yakin neman zabe, ya kan dauki ‘ya’yan cikinsa da suka hada da mata da maza don hakan ya zama abin misali ga sauran ‘yan takara.
Har wa yau, ya ce samun zaman lafiya ya danganta da irin shugabancin da jam’iyya take da shi, wanda hakan ne zai samar da sahihin zabe.