Da za a samu irin mahaifina da Nijeriya ta yi dadin zama —Fatima Dangote
Na so a ce muna da mutane koda kadan ne irin mahaifina a Nijeriya.
Babbar Daraktar Harkokin Kasuwanci na Rukunin Kamfanonin Dangote, Hajiya Fatima Dangote, ta yaba wa mahaifinta kan jajircewa da hakurinsa wajen ganin Nijeriya ta dogara da kanta.
Hajiya Fatima Dangote ta bayyana haka ne lokacin da take jawabin godiya a wajen taron manema labarai da Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya gudanar da shugabannin kafosfin watsa labarai da manyan ’yan jarida a harabar matatar da ke Legas.
Hajiya Fatima Dangote ta ce, “Ban taba ganin wani mutum mai aiki tukuru irin mahaifina ba. Ba wai don yana mahaifina ba.
“Wasu lokuta nakan ji mamakin me ya sa bai karaya a kan abin da ya sa a gaba.
“Na so a ce muna da mutane koda kadan ne irin mahaifina a Nijeriya.
“Da kasar nan ta zama mai dadin zama,” in ji ta.