Da zafi-zafi a kan bugi karfe…

Sakamakon fito-na-fiton da kungiyoyin kwadago suka yi niyyar yi da gwamnatocin jihohi game da batun da ake yi cewa, suna kokarin rage albashin ma’aikata mafi karanci na Naira dubu 18 a wata,  Gwamnan Jihar Zamfara, kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Abdulaziz Yari ya bayyana a makon jiya cewa,  gwamnonin jihohin kasar nan ba su […]

Da zafi-zafi a kan bugi karfe…
Da zafi-zafi a kan bugi karfe…

Sakamakon fito-na-fiton da kungiyoyin kwadago suka yi niyyar yi da gwamnatocin jihohi game da batun da ake yi cewa, suna kokarin rage albashin ma’aikata mafi karanci na Naira dubu 18 a wata,  Gwamnan Jihar Zamfara, kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Abdulaziz Yari ya bayyana a makon jiya cewa,  gwamnonin jihohin kasar nan ba su da niyyar zabge albashin ma’aikata daga yadda aka saba biyansu. Ya kuma bayyana cewa, babu inda kungiyar gwamnonin ta yanke shawarar yin haka, amma sai dai gwamnonin sun nuna cewa idan har aka ci gaba a cikin wannan halin matsi, na rashin kudi da gwamnatocin suke fama da shi, to fa tana iya yiwuwa su kasa sauke nauyin da ke wuyansu, ba ma na biyan albashi mafi karanci ba, har ma da na gudanar da muhimman ayyukan ciyar da kasa gaba da inganta  yanayin zamantakewar jama’arsu.
A yanzu dai halin tattalin arzikin kasar nan ya ja da baya, Gwamnatin tarayya ba ta iya samar da kudi ga jihohi yadda aka saba, ita ma sai ta daddage tukuna, kafin ta iya fitar da dan abin da za ta tsuntsunka don biyan muhimman bukatun da ke gabanta. Abin ma har ya kai a halin yanzu wasu gwamnatocin ba su samun abin da ya haura Naira miliyan dubu biyar a wata, kuma daga ciki ne za a ci, a sha, a gudanar da harkokin da suka jibanci tsaro da kuma albashin dubban daruruwan wadanda suka ajiye aiki, suna zura wa gwamnatoci ido don biyansu fansho.
Idan aka yi la’akari da irin alkawuran da shugabannin gwamnatocin kasar nan suka dauka yayin da suke shakar kanshin gidajen gwamnati, sa’ilin da suke yakin neman zabe, sai a fahimci cewa wajibi ne fa a gare su a yanzu su rage buri, su kuma fito fili su fayyace wa jama’a cewa ba su da gashin wance, saboda haka nan ba za su yi kitson wance ba. Tun da dai ruwansu ba zai ishe su wanka ba, sai su su yi alwala da shi , su jira lokacin da Maiduka Zai yaye masu matsalar da ta jefa su cikin matsin.  Shugaba Muhamadu Buhari ya yi alkawarin bayar da Naira dubu biyar-biyar ga matasan da suka kammala karatun jami’a ba su da aikin yi, sa’anan  shi da wasu gwamnonin jihohi sun kudurta aniyar ciyar da daliban makarantun firamare har zuwa wani sashi na sakandare, sun tsara cewa za su dauki dubun-dubatan matasa aiki don su magance masu zaman kashe wando a gaban iyayensu, to amma sai ga shi faduwar farashin man fetur da aka ta’allaka a kansa ya rage wa ayar da suka shuka zaki, albashin ma’aikatan da ake da su ma na neman ya gagare su biya, ballantana kuma batun kara wani nauyi dangane da haka wajen daukar wasu sababbin ma’aikatan da za a biya da daruruwan miliyoyin Naira a kowane wata.
Talakawa sun shiga wani mawuyacin halin matsi a halin yanzu, cefane na gagarar magidanta, haka nan su da iyalansu ke kwana da ta-bahuwa, da safe da wuya ake ganganda garin da za a samu kunun karin kumallo, kuma ko ’ya’yansu sun je makaranta babu abincin da aka alkawarta musu, haka nan za su komo gida, su zura wa iyayensu idanu, suna jirar abincin da ba a san lokacin samuwarsa ba. ’Yan kasuwa na fama da rashin ciniki, masu sana’o’in hannu ba su samun sukunin yin haka don  farashin kayayyakin da suke bukata ya cilla sama, ya kuma ki saukowa don su ci gaba da gudanar da sana’o’in.
To, amma duk da haka nan ya wajaba ga ’yan Najeriya su kara yin hakuri, su rungumi sababbin shugabanninsu da ke kokari, ba dare, ba rana wajen fitar da su daga kangin da gwamnatocin da suka shude suka dade da jefa su ciki. Wannan ba ya nufin cewa, gwamnatin za ta shantake ne ba, ta ki turzawa yadda ya kamata don cire wa talakawa kitse a wuta, tilas ne ta bi alkiblar canjin da ta shafa wa talakawa mai a baki game da shi, ba tare da ta tsaya tsilla-tsilla ko farfagandar siyasa mara tasiri  ba, da sunan yaki da rashawa da ha’inci, domin kuwa kowa da kowa ya zura ido ya ga irin namijin kokarin wannan gwamnati na raba shi da illolin da ke rage masa gardin rayuwa. Kowa kuma ya kosa gwamnatin nan ta nuna masa cewa, zaman jin dadi da walwala yake yi a kasar haihuwarsa mai dimbin arziki, ba jiran mutuwa ba cikin kaskanci da wulakanci a yanayi na shan wuya da bakar ukuba.
A daidai wanan lokaci ne da Gwamnatin Muhammadu Buhari ke kokarin sharewa don ta sha da karari, za ta dora dan ba game da farfado da tsare-tsaren da aka yi a lokutan baya da kuma inganta dabarun da aka bari suka tabarbare don dora Najeriya bisa turbar dogaro da kai, ta fannonin masana’antu da kuma kere-keren abubuwan da za su gaggauta habaka tattalin arziki.  Wannan gwamnati dai ta fadakar da ’yan Najeriya game da dimbin arzikin da ke binne a karkashin kasarsu, ta kuma yi alkawarin tono musu wadannan ababen don su more rayuwarsu.
Muddin dai ba an dage ne  wajen amfani da albarkar da ake samu daga danyen man fetur din da aka dogara kacokan akansa  ba, wajen habaka aikin gona da hako ma’adinan da za a sarrafa a masana’antun da za a farfado da su, a kuma inganta, to babu ta yadda za a yi Najeriya ta dara tsararrakinta, za ta ci gaba ne da komawa baya, har ta zamanto daidai da fakiran kasashen da ke  yawo a kasashen duniya  da kokunan bara a hannayensu. Idan ba Gwamnatin Shugaba Buhari ta dage ne ba wajen  kekkera kayayyakin da za a rika sayarwa ne ba a kasashen ketare, to haka nan za mu yi ta ganin darajar  Nairarmu  na tabarbarewa, Dala da Fam kuma na kara murmurewa, suna yin karfin da zai danne mana tattalin arziki. Ina amfanin farfado da masana’antu idan har aka kasa samar da amfanin gonar da za a sarrafa a cikinsu, sai an yi sautunsu daga kasashen ketare? Tilas ne a inganta harkokin noma yayin da ake farfado da masana’antun.
A yanzu Gwamnatin Buhari ta rigaya ta fada wa talakawan kasar nan mara dadin, cewa arzikin kasarsu ya karye, daraja da farashin man fetur sun fadi kasa warwas a kasuwannin kasashen duniya, kuma watakila a dade ana fama da wannan matsalar. To idan har ba a fahimce shi ba, aka kuma ki daukar matakan kago dabarun ficewa daga cikin matsalolin da ya hango, cewa,  hakan na iya hadasawa, to haka nan jama’ar Najeriya za su ci gaba da kasancewa cikin fatara da mayata a jihohi, a kasa baki daya kuma a yi ta fama da fitintunun da rashin tsaro ke haddasawa da kuwa rashin wadatattun kudin sauke nauyin da ke bisa wuyan Gwamnatin Tarayya, domin kuwa da zafi-zafi a kan bugi karfe, sa’annan sai an kau da kai ake sare tofa.