Da zan mutu in sake dawowa aikin jarida zan yi -Mahmun Baba Ahmad
Aminiya ta tuntubi shahararren dan jaridan nan Mahmun Baba Ahmad domin jin tarihinsa da irin nasarorin da ya samu a aikin jarida da kuma matsalolin da ya fuskanta da kuma shawarwarin da zai ba ‘yan baya. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ba mu takaitaccen tarihinkaAn haife ni a Tudun Wadan Zariya ne, kuma a […]

Aminiya ta tuntubi shahararren dan jaridan nan Mahmun Baba Ahmad domin jin tarihinsa da irin nasarorin da ya samu a aikin jarida da kuma matsalolin da ya fuskanta da kuma shawarwarin da zai ba ‘yan baya. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ba mu takaitaccen tarihinka
An haife ni a Tudun Wadan Zariya ne, kuma a nan Zariya na yi makarantar firamare da sakandare, daga baya ne na shiga aikin jarida a shekarar 1970, inda na fara aiki a gidan rediyon tarayya na Kaduna, wanda a lokacin ake kiransa Broadcasting company of Northern Nigeria (BCNN).
Na fara aikin ne a matsayin mai gabatar da shirye-ishirye, na yi shekara daya da rabi a wannan waje, daga nan sai na koma kanfanin buga jaridun New Nigerian. A can sai aka ba ni aiki a matsayin karamin edita, ina nan har na kai editan labaran kasashen ketare. Daga nan sai na zama editan mukalu (Features).
Na shekara uku da rabi a New Nigerian, sai na sake komawa gidan rediyon Najeriya na Kaduna, lokacin ana kiransa Rediyo Telabijin Kaduna, a matsayin jami’in bada rahoto mai daraja ta biyu. Sai kuma aka tura ni jahar Bauchi a matsayin wakilin gidan rediyon. Ina jahar Bauchi na yi shekara daya da wata goma, sai aka bullo da siyasa a watan Satumbar shekarar 1978. Makonni biyu kafin lokacin sai aka yi canje-canjen dukkan masu aiko da rahotanni a arewacin kasar. Daga Bauchi sai aka kai ni Kano, na koma daidai da za a fara siyasa, inda na yi shekara hudu da rabi a can.
Ina can ne har na kai matsayin babban jami’in aiko da rahoto. Sabodsa irin yanayin yadda Kano ya kasance, a wancan lokacin akwai tarzoma, akwai hayaniya, kuma a lokacin muna tsakiyar wadannan abubuwa, saboda muna ‘yan jarida. Saboda wadansu na ganin aikinmu na da hadari saboda muna tona asiri. Babu irin abin da ba a yi mini ba a jahar Kano. An kai hari a gidana, an kai hari a ofishina, ina tafiya an nemi a taka ni da mota, har na karye aka kwantar da ni a asibiti.
Saboda haka da wata shekarar zabe ta sake dawowa sai hukumar gidan rediyon ta ce ai gara a sake mini warin aiki, a koma da ni wata jaha. Shi ne aka yi mini canji zuwa jihar Filato a shekarar 1982. Ina can ma bayan na yi kamar wata biyu, sai babban jami’i mai aiko da rahotanni na rediyon tarayya a Maiduguri, marigayi Umar Yahaya, Allah Ya jikansa. Sai aka ce in yi maza in koma Maiduguri in cigaba da aikinsa.
Na koma Maiduguri jihar Borno. Nan ma an yi gudun gara ne an fada zago. Yadda Kano ke da zafi Maiduguri ma ta fi ta zafi a lokacin. Saboda hayaniyar siyasa da yamutsin siyasa, kusan Kano da maiduguri babu kamarsu a kasar nan. Haka nan na zauna a nan, tun daga watan Maris na shekarar 1983 har zuwa watan Oktoba na wannan shekarar. Watau watanni bakwai ke nan na yi a Maiduguri.
A cikin wannan lakaci ne aka kafa gwamnatin janhoriya ta uku. A lokacin nan wanda ya ci zabe a jihar Kano, Marigayi Sabo Bakinzuwo, bayan an rantsar da shi sai ya ce ina nake, domin ya yi kokari ya hana ni zuwa Jos don yana so mu yi aiki da shi, saboda sun ji dadin irin aikin da na yi, wanda babu tsoro, ga fadin gaskiya da kuma kamanta adalci a bisa aikina. Saboda haka ya ga ya fi dacewa ya nada ni Janar Manaja na gidan Rediyon jihar Kano.
Saboda haka sai aka bada sanarwar cewa an mayar da ni Janar Manaja na gidan rediyon jihar Kano, su kuma wadanda suka tura ni aiki jihar Kano, watae hukumar gidan radiyon tarayya sai ta ce a’a. Domin idan aka yi haka za a ce an yi mini sakayyane a kan wani aiki da na yi musu. Alhali kuwa ni na yi tsakanina da Allah ne. Su kuma can Kano suka matsa sai na je, su kuma Kaduna suka ja daga.
Su Malam dahiru Modibbo, Allah Ya jikansa da maigidanmu na labarai, Malam Muhammad Sulaiman, da Alhaji Yusuf Ladan, dan iyan Zazzau na yanzu. Suka zauna suka yi shawara cewa mafita daga wannan lamari shi ne su ba da ni aro ga gwamnarin jihar Kano. Kuma haka aka aka yi, inda na tafi jihar Kano a matsayin Janar Manaja na gidan Rediyon jahar, kuma wa’adina na cika sai Kaduna suka ce in dawo. Da na dawo sai aka sa na shugabanci bangaran harkokin yau da kullum. Daga nan ne aka tura ni jihar Legas, inda na zama babban jami’in na masu aiko da rahotanni, wanda a lokacin suna da wakilai a ko’ina a kasar nan.
Ina can sai aka kirkiro jihar Katsina a shekarar 1987, kuma a lokacin nan ma’aikata kwararru a jihar Kaduna sai suka koma jihar Katsina, aka zo ana neman manyan ma’aikata, domin a lokacin akwai Daraktoci da suka koma jahar Katsina. Daga nan sai babbanmu a wajen aiki, Mohammad Sulaiman ya bada sunana ga Sakataren gwamnatin jihar Kaduna domin in zama daraktan yada labarai na gwamnatin jihar Kaduna.
Ni ma labari kawai na ji, zan yi magana sai aka ce an riga an gama. Shi ke nan sai na tattara kayana daga jihar Legas na dawo Kaduna. Bayan na yi shekara hudu da rabi sai aka ce in koma gidan Rediyon jiha . A nan gidan Rediyon jahar na yi shekara uku da rabi, inda kuma na yi ritaya daga aiki.
Aminiya: Dama aikin Jarida kaso yi kana yaro ko kuwa ka tsinci kanka ne a aikin?
Gaskiya ba aikin da na so yi ba ke nan, amma dai bayan na shiga sai na ji ina sha’awar aikin. Shi ya sa ko da na shiga aikin na fara ne a matsayin mai gabatar da shirye-shirye. Amma ko a lokacin abin da na fi so a aikin shi ne in rika aiko rahoto daga wadansu wurare, amma da aka ce da ni ai ban koya ba kuma ban iya ba, don haka abin da za su iya yi mun shi ne in zama mai fassara labarai.
Komawata kamfanin New Nigerian ne ya ba ni damar koyon yadda ake nemo labarai, inda kuma aka tura ni makarantar koyar da aikin jarida da ke Legas. Saboda haka, ni a kowane lokaci ina sha’awar wannan aiki, domin babban wanmu marigayi Aminu Baba Ahmad, shi ma aikin ya yi. Sannan kuma kanina wanda muka tashi tare da shi, Khalifa Baba Ahmad, Allah Ya jikansa, shi ma ya yi wannan aikin. Kuma shi ne ma ya matsa mini na shiga wannan aiki, har Allah Ya sa ina da rabo a cikinsa. Na kai kololuwa a wannan aiki.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu a wannan aiki?
Babu shakka na samu nasarori iri-iri, domin da farko dai shi ne, burin kowane irin ma’aikaci shi ne ya kai kololuwar aikinsa. Don haka zan iya cewa ni na kai kololuwa, domin kuwa na zama shugabban duk masu aiko da rahotanni na gidan radiyon Tarayya a Legas. Sannan a aikin gwamnati, burin kowane ma’aikaci shi ne ya kai matsayin darakta. Kuma ni na kai matsayin darakta a aikin yada labarai kuma a aikin gwamnati. Saboda haka na yi aikin gwamnati yadda ya kamata, na san yadda gwamnati ke tafiyar da aikinta. Sannan kuma na san aikin jarida.
Sannan a matsayin mai aikin radiyo, burinsa shi ne ya kai Janar Manaja. To, na kai Janar Manaja na gidan radiyon jihar Kano, bama na Kaduna ba. Sannan a matsayin mai aikin yada labarai, na zama Manajan Darakta na gidan Rediyo da Talibijin na kaduna. Da ana kiran wannan gidan rediyo KSBC, ni na canza masa suna zuwa KSMC. Watau wuraren da ake da kafafan yada labarai da yawa.
Saboda a lokacin akwai jarida da mujalla da talibijin, sannan ga rediyo, shi yasa muka mayar da sunan KSMC. Saboda haka babu wani abu da ya rage da za a ce ina kwadayi ko ina sonsa wanda ban yi ba, ko ban kai ba a aikin jarida baki daya.
Aminiya: Wane kalubale ka fuskanta a aikin jarida?
Kowane irin aiki yana da kalubalensa, amma kuma kalubalen kowane irin aiki iri daya ne, watau tsayar da gaskiya da rikon amana. Babu shakka duk mutumin da ke kowane irin aiki ne zai fuskanci jarabawa, zai fuskanci matsaloli, zai kuma hadu da abubuwa da za su faranta masa rai, amma duk maganin wadannan shi ne yadda zai rike gaskiya da amanar da aka ba shi ba tare da sa son zuciya ba, kuma ya yi shi da adalci da kamanta gaskiya. Wannan yana daya daga cikin wahala da mutane suke fuskanta a kowane irin aiki ne.
Alhamdulillah, na yi iya kokarina dangane da haka, saboda na yi sa’ar samun shugabanni wadanda suka dage, suka tabbatar lailai cewa sai an bi gaskiya, an kamanta gaskiya a dukkan abin da ake yi, musamman a aikin labarai.
Babu wani wanda ya fi jami’in aikin watsa labarai adalci, ko da kuwa alkali ne. Domin shari’a ai an dora ta bisa tsanin adalci ne, amma shi dan jarida duk abin da zai yi, zai yi shi bisa adalci ne. Farko ya yi wa kansa adalci, sannan ya yi wa mutanen da yake wa aikin adalci. Kuma ya san cewa amana ce aka ba shi, ba don ya fi kowa ba. Saboda yana da abin magana ko yana da alkalami, wannan ba garanti ba ne ko lasisi da zai je ya rubuta ko ya fadi abin da ya ga dama, domin bata wani wanda bai so.
Saboda haka tun daga wannan matsayi aka fara dasa dan ba kan adalci. Sannan kuma idan ya je ya ji wannan bangare dole ya je ya ji wancan bangaren. Kamar yadda alkali ke yi idan ya saurari mai kara sai kuma ya saurari wanda ake kara, don ya san yadda zai yi ya yanke hukunci. To, shi dan jarida ba alkali ne ba, amma zai ji na nan sai ya ji na can, sannan ya tattara bayanai ya tura wa mai sauraro ko mai karatu domin shi ya yanke hukunci da kansa, bisa yadda ya fahinci abubuwan da aka gabatar masa. Saboda haka idan ka ga ana hayaniya da dan jarida ko kuma dan jarida ya shiga matsala ko kalubalen da suka addabe shi, to, shi ya ja wa kansa, domin bai yi adalci ba, ko bai kamanta gaskiya ba, ko kuma ya bi son zuciyarsa. Shi ya sa a aikin jarida babban abu shi ne kamanta gaskiya. Muddin ba ka yi gaskiya ba ka gama yawo, saboda idan ka rubuta karya ko ka fadi karya aka buga, jama’a suka gane karya kake yi, gobe ko ka fadi gaskiya babu wanda zai saurareka, domin al’amarin kamar wankar wuta ne, sau daya ake yafawa. Saboda haka tilas a kiyaye wadannan abubuwa, domin karekkalubale da ka iya tasowa. Kuma muddin aka kiyaye, babu wani kalubale da zai taso, kuma sai a yi aikin jarida yadda mai wasan maciji yake yi, ‘yan kallo lafiya, mai wasa lafiya.
Aminiya- wace shawara za ka ba wadanda ke aikin jarida yanzu dangane da wannan aiki?
Shi ne su kama mutuncinsu, shi aikin jarida fa bai sha bamban da wadansu ayyuka ba, domin dukkan ka’idoji na sauran ayyuka haka nasa yake. Adalci da kamanta gaskiya a komi fa akwai shi, domin ko a gidanka tsakaninka da matanka dole sai ka kamanta adalci. Kuma kai kanka ma za ka yi wa kanka adalci. Saboda haka babban abin da dan jarida zai yi wa kansa shi ne kare mutuncinsa. Ya kuma kare mutuncin wadanda yake bada labari a kansu. Kada ya zubar da mutuncin kowa, kada ya kuma ci mutuncin kowa, domin idan ya ci mutuncin wani, to ya ci muntucin kansa ne. Idan kuma ya zubar da mutuncin kansa za a kalle bai da mutunci a idon kowa. Ta ya zai yi ya zubar da mutuncinsa, shi ne ya kaskantar da kansa, ya zamanto yana kwadayin abin hannun jama’a, alhali kuwa Manzon Allah (SAW) ya ce mana duk mai son ya tsira da mutuncinsa, to ya guji abin hannun mutane. Idan ko ka guji abin hannunsu za ka tsira da mutuncinka kuma ka samu martaba a idonun jama’a. Idan ka tsayawa gaskiya ka kuma rike mutuncinka, babu yadda za a yi wani abin da zai gagare ka. Mu mun tsaya wa gaskiya a aikin, saboda shugabanninmu a lokacin sun nuna mana cewa wajibi ne mu yi haka, kuma ga shi mun samu daukaka.
Da farko sunanmu ya daga sama, babu inda ba a sanmu ba. Wannan abin alfahari ne, amma dai ba mu bari kuma ya shiga ranmu har mun yi fadin rai ko girman kai da za mu wulakanta jama’a ba. Dama ce Allah Ya ba mu, kuma gobe yana iya bai wa kowa. Sannan babu wata kofa da aka rufe muka kwankwasa ba a bude mana ba. In dai kana dan jaridan gaskiya duk inda ka je ka kwankwasa za a bude maka a kuma yi maraba da kai, amma fa sai idan ka kare kanka.
Ofishohin gwamnoni wadanda ni na shiga da wadanda muka yi hannu da su Allah Ya yi yawa da su. Ofishin shugaban kasa na Najeriya da yawa mun shiga mun kuma yi hannu da su. Kai hatta Sarkin Makka mun yi hannu da shi a matsayina na dan jarida. Mai ya rage kuma. Sannan dan jarida mutum ne da jama’a ke sha’awarsa, wadansu kuma na tsoronsa, wadansu kuma suna kyarinsa, sannan wadansu na yi masa hassada saboda aikinsa.
Akwai wani balarabe da muka taba magana da shi a Saudiya wanda ya fada mini cewa shi a duniya babu wanda yake sha’awa kamar dan jarida, saboda wai idan sarkinsu ya fito yin dawafi a kan hana kowa sai dai shi da mutanensa kawai za su yi, saboda yadda suke girmama shi. Sai ya ce mini amma wata rana sarkin ya tafi filin jirgin sama zai yi tafiya sai dan jarida ya tunkare shi da ‘yar rikodarsa ya kara masa rikoda, sai da suka gama magana sannan sarkin ya wuce. Ya ce mini in ba dan jarida ba waye zai yi wa sarkin haka. To, haka dan jarida yake, amma fa sai idan ya kare mutuncinsa, idan bai kare mutuncinsa ba sai ya zama abin takawa. Saboda haka ni ina jin cewa da za a mutu a dawo duniya a ce wacce sana’a nake son yi zan ce ina son aikin Jarida. Da zan mutu sau goma in sake dawowa sau goma a tambaye ni sau goma, wane aiki zan yi zan ce aikin jarida sau goma.