Da zarar an janye yajin aiki za a rubuta jarabawa —ASUU

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU), ta yi kira da dalibai ’yan aji uku da ajin karshe a jami’o’i da su himmatu da yin bita a gida ba tare da sun kosa ba. ASUU ta ce akwai yiyuwar nan take a fara jarabawa da zarar aka bude makarantun idan suka daidaita da Gwamnatin Tarayya. ASUU na zargin […]

Da zarar an janye yajin aiki za a rubuta jarabawa —ASUU

Shugaban kungiyar ASUU Farfesa Biodun Ogunyemi

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU), ta yi kira da dalibai ’yan aji uku da ajin karshe a jami’o’i da su himmatu da yin bita a gida ba tare da sun kosa ba.

ASUU ta ce akwai yiyuwar nan take a fara jarabawa da zarar aka bude makarantun idan suka daidaita da Gwamnatin Tarayya.

Kungiyar ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter ‘yan sa’o’i kafin ci gaba da zaman tattaunawarta da Gwamnatin Tarayya.

Idan ba a manta ba ASUU ta kwashe kusan wata takwas tana yajin aiki sabonda rashin samun daidaito da gwamnati kan bukatun ’ya’yanta.

A ranar Juma’a ake sa ran kungiyar za ta kuma zama a teburin sulhu da wakilan gwamnati a ofishin Ministan Kwadago, Chris Ngige.

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa

Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro

Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga