Da’awar bayar da kudin ayyuka a mazabu: dan majalisa Faruk ya jefa mu cikin matsala – Mahmud

A kwanakin baya ne aka ruwaito dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bidda, Bala Salihu ya ce ’yan majalisar sun karbi miliyoyin Naira domin gudanar da ayyuka a mazabunsu, Aminiya ta samu tattaunawa da takwaransa na mazabar Agaie da Lapai a Jihar Neja, Honarabul Muhammed Abdulkadir Mahmud wanda ya ce wancan bayani ya jefa su a […]

Da’awar bayar da kudin ayyuka a mazabu: dan majalisa Faruk ya jefa mu cikin matsala – Mahmud
Da’awar bayar da kudin ayyuka a mazabu: dan majalisa Faruk ya jefa mu cikin matsala – Mahmud

A kwanakin baya ne aka ruwaito dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bidda, Bala Salihu ya ce ’yan majalisar sun karbi miliyoyin Naira domin gudanar da ayyuka a mazabunsu, Aminiya ta samu tattaunawa da takwaransa na mazabar Agaie da Lapai a Jihar Neja, Honarabul Muhammed Abdulkadir Mahmud wanda ya ce wancan bayani ya jefa su a cikin matsala, kuma ya tabo batun ’yancin da gwamnatin jihar ta bai wa kananan hukumomin jihar:

dan majalisa Bala Faruk mai wakiltar Bida ya yi ikirarin cewa an ba ku kudi domin gudanar da ayyuka a mazabunku, me za ka ce game kan wannan batu?
Alhaji Mohammed Abdulqadir MahmudGaskiya maganar da ya yi ba daidai ba ce, ba haka take ba kuma ina tabbatar maka cewa Bala ya yi maganar ne cikin kuskure. Saboda ba wanda ya ba mu ko sisi.

Amma shi ya ce an ba shi nasa kuma har ya raba wa mutanen mazabarsa?
Ina mai tabbatar maka wannan magana da ya yi ta son rai ce. Kuma a ra’ayina idan yana so ya yi fice a cikin jama’a ba irin wannan maganar ya kamata ya yi ba, idan zai yi magana to ya fadi gaskiya. Amma duk wanda yake neman jama’a su san shi to ya je mazabarsa ya yi wa jama’arsa aiki ba ya yi karya ba. Ya koma mazabarsa ya yi wa jama’arsa abin da ya kamata, ya rika zuwa suna ganinsa yana jin koke-koke da matsalolinsu ya yi maganinsu. Saboda na san mutanen mazabarsa suna kuka da shi kan rashin ganinsa.

Mene ne matsayinku a kan wannan al’amari?
To a yadda na samu labara, shi da kansa ya karyata kansa. Matakin da ake tunani a da shi ne. Muna daukar matakai don kada a tayar da wata hayaniya ta ba-gaira-ba-dalili a majalisa. Shi ya sa kake ganin muna bin abubuwa daki-daki.

Wadansu na ganin kun tursasa masa ne ya janye maganar da ya yi don ba ku so mutane su gane an ba ku kudi?
Abin da nake so ka gane shi ne babu yadda za a ce an ba mu wadannan makuden kudi haka kawai daga sama, dole sai an bi wasu hanyoyi har ta kai an sanya su a asusun kowane dan majalisa. Saboda haka ina kalubalantar Bala ya zo ya fada wa duniya wa ya ba shi nasa kudin kuma su wa ya ba a mazabarsa?

Tunda kuke majalisar nan akwai ayyuka da kuke yi, ta ina kuke samun kudin da kuke gudanar da ayyukan?
Ai na yi bayani, ayyukan nan da ake yi kudi ne da ake bai wa kowane dan majalisa don ya yi wa jama’arsa aiki. Wadannan kudi ba ba mu su ake yi ba, kai-tsaye ake bai wa ma’aikatun da za su yi aikin. Kai dai a matsayinka na dan majalisa za ka bayyana irin ayyukan da kake so a yi da kuma wurin da za a yi aikin. Saboda haka kamfanonin ne suka san yadda za su gudanar da aiki.

Shin an fara gudanar da irin wadannan ayyuka?
Kamar yadda jama’a suka sani ne, ai sai yanzu aka kai gacin sanya hannu a kasafin kudi. Saboda haka idan komai ya daidaita za a fara gudanar da irin wadannan ayyuka ba tare da bata lokaci ba.

Ka kaddamar da aikin noman rani a mazabarka da sauran ayyuka, ina ka samu kudin da ka kashe a wadannan ayyuka?
Na samu kudin da na gudanar da wadannan ayyuka ne daga dan kudin da ake ba mu a majalisa na albashi da alawus-alawaus, wasu ayyukan kuma daga cikin dukiyata na yi. Sannan ita gwamnati aba ce mai ci gaba. Gwamnatin da ta shude da muka karbi ayyukansu mun ci gaba da gudanar da wadanda ba su kammala ba. Saboda haka idan ka ga mun dan yi wani abu galibi daga kasafin kudin bara muka samu kudinmu.

Wane irin hali kalamin dan majaisa Bala Faruk ya jefa ku?
Gaskiya ya jefa mu cikin mummunan hali kuma mun shiga babbar matsala, saboda mutanenmu suna tsangwamarmu. Idan ka duba dandalin sadarwa za ka ga inda ake cewa har wasu suna zage-zage, na ji wai a Kaduna wasu sun doki dan majalisarsu wasu kuma an jefe su. Saboda haka muna yi masa gargadi kada ya sake yi mana irin wannan muguwar magana mai kama da haka. Idan Bala ya sake yin irin wannan maganar za mu dauki mataki a kansa.

Gwamnatin Jihar Neja ta yi shelar bai wa kananan hukumomin jihar ’yancin gudanar da mulkinsu ba tare da tsangwama ba, mene ne ra’ayinka kan haka?
Gaskiya wannan abu ne mai kyau, amma akwai matsala. Matsalar ita ce mafi yawan kananan hukumomin ba za su iya daukar dawainiyar kansu ba. Hatta albashi ba za su iya biya ba, saboda karancin kudin shiga. Idan ka duba za ka ga suna fuskantar matsalar yawan ma’aikata da ma’aikatan bogi da ma’aikatan da ba su zuwa aiki da kuma wadanda ba su da kwarewa a kan ayyukansu. Shi ya sa muka zauna da duk masu ruwa-da-tsaki a karamar Hukumar Lapai muka tattaunawa wadannan matasaloli don mu kawo gyara a wannan al’amari. Kuma har sarkinmu ya yi kira ga jama’a cewa duk wadanda ba su zuwa aiki su tuba su rika zuwa aiki.

Ita karamar hukumarka ba ta da hanyoyin samun kudin shiga ne?
Gaskiya abin da ake samu ba ya kaiwa ga asusun karamar hukumar saboda wadanda aka dora wa alhakin karbo kudin haraji a karamar hukumar ba sa ba ta. Shi ya sa wannan batu yana daga cikin muhimman abubuwan da muka tattauna don ganin cewa duk kudin haraji ko na shiga na karamar hukuma da ake karba an sanya su a cikin asusun karamar hukumar.