Da’awar bayyanar Nyas a shago ya jefa ’yar haya a damuwa

Wata mai sayar da haja a shagon da take haya a Suleja ta Jihar Neja ta fada a cikin damuwa, bayan wanda ya ba ta hayar ya rufe shagon, saboda tururuwar da jama’a ke yi a shagon, don ganin marigayi Nyas, wanda aka ce ya bayyana a wata kusuruwar shagon da ke titin Hassan Dallatu […]

Da’awar bayyanar Nyas a shago ya jefa ’yar haya a damuwa
Da’awar bayyanar Nyas a shago ya jefa ’yar haya a damuwa

Wata mai sayar da haja a shagon da take haya a Suleja ta Jihar Neja ta fada a cikin damuwa, bayan wanda ya ba ta hayar ya rufe shagon, saboda tururuwar da jama’a ke yi a shagon, don ganin marigayi Nyas, wanda aka ce ya bayyana a wata kusuruwar shagon da ke titin Hassan Dallatu a Suleja.

Mijin matar Alhaji Shitu ya shaida wa wakilinmu a shekaranjiya Laraba cewa lamarin ya samo asali ne a ranar Talata lokacin da wani da ke taya matar kasa kaya, ya ankarar da ita cewa ga Shehu Nyas ya bayyana a katangar shagonta. Ya ce cikin kankanen lokaci maganar ta kai ga makwabta da masu wucewa, inda aka rika tururuwa zuwa shagon, lamarin da ya kai ga balle taga da kofar shagon tare da yi wa sassansa lahani.
Wanda ya ba ta hayar da ya ki bayyana sunansa ga wakilinmu, ya ce, ya girgiza da abin da lamarin ya jawo a unguwar musamman jifan sojoji da wasu daga cikin jama’ar da suka so kaiwa ga shagon. Ya ce jama’a sun rika taruwa har suka rufe titin Hassan Dallatu daya daga cikin manyan titunan garin Suleja.
Ya ce ya sanar da hukuma kuma sojoji sun yi kokarin raba jama’a da wurin amma ba su samu nasara ba, don haka ne ya yanke shawarar rufe shagon.
Matar, tare da wasu danginta sun nemi ya yi hakuri ya mayar mata da shagon, amma ya ce ya yi wuri a bude shagon a yanzu saboda jama’a na ci gaba da zuwa.
Ya gaya mata cewa ya fi damuwa da matsalar tsaro, ba lahanin da aka yi wa shagon ba.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan yankin Suleja ACP Abubakar Yahaya a ofishinsa an shaida masa cewa yana cikin wani aiki ba zai iya ganawa da shi ba.