Da’awar wayewa ke sa matasa shaye-shaye – Malam Niga
Malam Lawal Yusuf Baduru wanda aka fi sani da (Malam Niga) yana da cibiyar kula da masu tabin hankali a Rigasa da ke Jihar Kaduna. A kwanakin baya ya kira taron manema labarai domin tunawa da ranar masu tabin hankali ta duniya da ake yi duk shekara: Mene ne makasudin kiran wannan taro?Makasudin wannan taro […]
Malam Lawal Yusuf Baduru wanda aka fi sani da (Malam Niga) yana da cibiyar kula da masu tabin hankali a Rigasa da ke Jihar Kaduna. A kwanakin baya ya kira taron manema labarai domin tunawa da ranar masu tabin hankali ta duniya da ake yi duk shekara:
Mene ne makasudin kiran wannan taro?
Makasudin wannan taro shi ne Majalisar dinkin Duniya ta kebe 10 ga Oktoban kowace shekara domin masu tabin hankali saboda a duba matsalolinsu. Walau shaye-shaye ko wasu abubuwan damuwa ko wani abu da ke shafar kwakwalwa har ta samu tabin hankali.
A fahimtarka me ke janyo tabin hankali?
Da farko akwai wadanda damuwa ke jawo musu tabin hankali, haka in shaye-shaye ya yi yawa yakan sa a samu tabin hankali. Sannan akwai wadanda damuwa ta addabe su, musamman matasa saboda rashin aikin yi, sukan samu kansu cikin halin me za su sha ya kwantar musu da hankali. Irin wannan kan sa mutum ya fada cikin halin kaka-ni-ka-yi, har damuwa ta shige shi ya samu tabin hankali.
Wannan cibiya taka tana da dalibai kamar nawa?
daliban wannan cibiya tawa karanci za su kai kamar 1,300.
Mene ne irin matsalar da suke fama da ita a nan?
Suna da matsaloli daban-daban, akwai yara kananan wadanda ba shaye-shaye ce matsalarsu ba, tasu kangara ce saboda sun samu abokai marasa jin magana, sai ya zama sun saka kansu cikin irin wannan hali. Har ta kai yaro ba ya zuwa makaranta ko yana gudun zuwa gidansu. Saboda irin wadannan miyagun abokai sai ka ga ga yaro da gatarsa amma ya shiga matsala. Sannan akwai matasa marasa aikin yi da saboda rashin aiki sai su rika shan kwaya domin ta kwantar musu da hankali, daga nan sai su shiga matsalar da za ta kai su ga kashe iyayensu ba tare da sun sani ba. A yanzu haka akwai wasu kwayoyi da matasa ke amfani da su da za su iya sanya su daba wa iyayensu ko ’yan uwansu wuka ba tare da sun san sun aikata haka ba. Idan ya gagari mutane sai ka ga sun kawo su nan wurinmu.
Shin dalibanka ’yan Najeriya ne ko akwai na wasu kasashen Afirka?
Akwai na wasu kasashen Afirka da aka kawo mana domin ba su magani.
An ce ana koya musu sana’o’i, wadanne irin sana’o’in ake koya musu?
Idan aka kawo mana mahaukaci ko mai tabin hankali mukan ajiye shi karanci wata daya, idan magani ya ratsa masa jiki zai zama mai ladabi, to, sai mu fito da shi waje a ba shi yunifom a koya masa sana’a. Wasu wadanda suka kawo su ne suke zabar irin sana’ar da za a koya musu, wani kuma koda an zaba masa zai ga wata ya ce ita yake son a koya masa. Kuma muna koya yaki da jahilci ga masu bukatar karatu, kuma muna da sashin kwanfuta. Muna da bangarorin koyon aikin kafinta da dinki da yin sabulu da kira da rini da aski da walda. Mata kuma akwai bangaren saka da dinki da ake koya musu.
Shin akwai tallafin da kuke samu daga gwamnati ko kungiyoyi?
Babu wani tallafi da muke samu daga bangaren kungiyoyi sai dai gwamnati, misali akwai lokacin da Gwamnan Jihar nan ya aiko mana da buhun shinkafa 50 domin ciyar da wadannan bayin Allah, muna kuma godiya.
Ka yi bayanin magani kake ba su, na Bature ne ko na gargajiya?
A’a, maganin gargajiya nake ba su ba na Bature ba.
Shin Musulmi ne a nan wurin ko da wadanda ba Musulmi ba?
Ba Musulmi kawai ke nan ba. Akwai yara da mata da dattawa sannan akwai Kirista a nan.
Shin wannan matsala ta shaye-shaye na karuwa ne ko raguwa a tsakanin matasa?
Za mu iya cewa yanzu wayewa ce a ce kana shaye-shaye, idan ba ka yi za a ce kai koma-baya ne a cikin matasa, saboda haka karuwa take yi a cikin al’umma, sai dai mu roki Allah Ya dakushe abin.