Dabara ta 2: Koyi da sunnar Annabi SAW

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Za mu karasa bayani kan dabara ta 2 daga inda muka kwana a makon da ya gabata.Kamar yadda bayani ya gabata Annabi SAW bai lamunci daya daga cikin matansa ta yi batanci ga daya ba, zai nuna mata ba ta yi daidai bat un a lokacin, […]

Dabara ta 2: Koyi da sunnar Annabi SAW
Dabara ta 2: Koyi da sunnar Annabi SAW

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Za mu karasa bayani kan dabara ta 2 daga inda muka kwana a makon da ya gabata.
Kamar yadda bayani ya gabata Annabi SAW bai lamunci daya daga cikin matansa ta yi batanci ga daya ba, zai nuna mata ba ta yi daidai bat un a lokacin, ya kuma kaurara lafazi wajen ganar da ita wannan kuskurenta; sannan ya bayyanar da bacin ransa gare ta don kada ta sake kwatanta irin haka. Don haka babban kuskure ne ga maigida ya zauna ya saurari daya daga cikin matansa tana muzanta daya da bakinta kuma ya kyale ta bai nuna mata kuskurenta ba. Wani ma da shi ake zama ana munana kalamai ga wata daga cikin matansa. Wannan kuskure ne babba kuma muguwar dabia ce da ba ta dace ba ga duk wani magidanci Musulmi.
Kamar yadda aka ji Annabi SAW ya yi din nan, to duk magidancin kwarai hakan ne mafi dacewa ya rika yi: watau take yanke lokacin da ya ji wata daga cikin matansa ta yi irin haka,  sai ya nuna mata kuskurenta ya kuma bayyanar da bacin ransa gare ta don ta kiyaye kada ta kara maimaita hakan don samun wanzuwar zaman lafiya da aminci tsakanin juna. Mu ji dai yadda Annabi SAW yake kaurara kalamansa ga Ummuna Aisha RA duk lokacin shaukin kishi ya sa ta yi wani kalamin da bai dace ba, duk da cewa matsayinta da girman sonta a wajensa SAW. Don haka komai matsayin mace, komai so da kaunar da ake mata, bai dace maigida ya kyale ta ta shiga hakkin abokiya ko abokan zamanta ba, domin wannan ya ci karo da shari’a kuma ya nuna cewa wannan maigida ba adali ba ne.
2. Haka kuma, Annabi SAW ya kasance yana kyale matansa su mayar wa juna magana tsakaninsu yayin da ya ga ana so a shiga hakkin wata, misalin haka yana a cikin wannan kissa da mai zuwa:
Matan Annabi SAW sun kasance sun rabu gida 2: Akwai ’yan bangaren Ummuna Aisha RA wanda ya kunshi ita Ummuna Aisha, Sauda, Hafsa da Ummuna Safiyya RA, sai bangaren Umm Salama wanda ya kunshi Umm Salama, Juwayriya; Zainab da Maimuna RA.
Sai ya kasance Sahabban Manzo Allah SAW sun kasance suna yawan aiko masa da kyatuttuka duk ranar da yake gidan Ummuna Aisha RA a dalilin sun san ya fi sonta sama da kowa cikin matansa. Sai ’yan bangaren Umm Salma suka tattauna a kan wannan batu, sannan suka bukaci Umm Salma ta yi wa Annabi SAW maganar cewa ya umarci Sahabbansa su rika aiko da kyaututtuka gare shi ranar girkin kowacce daga cikinsu; sai ta yi masa SAW magana ranar aikinta, bai ce komai ba; ’yan bangarenta suka ce ta yi ta tambayarsa har sai ya ba ta amsa; da ta tambaye shi a karo na 3 ne sai ya ce: “kada ku cutar da ni a kan Aisha, domin kuwa wahayi ba ya saukar min a dakin kowaccenku sai a dakinta.” Sai Umma Salma ta ce “na tuba zuwa ga Allah a kan bata maka ran da na yi.”
Sai sauran ’yan bangaren suka nemi Nana Fadima RA da ta ce wa Annabi SAW: “Matan sun ce ka huldance su daidai da yadda kake wa ’yar Abubakar, (watau Aisha RA)” Sai Ya ce: “Yanzu ba ki son abin da nake so Ya Fatima? Sai ta amsa da Tana so. Da ta gaya musu sai suka bukaci ta koma, sai ta ki amincewa.
Daga nan sai Zainab Bint Jahsh ta koma wurin Annabi SAW lokacin yana gidan Ummuna Aisha RA. Ta ce masa cikin kakkausan lafazi: “Matanka sun ce ka daidaita su da ’yar Ibn Abu kuhafa“ Annabi SAW Bai amsa mata ba; sai ta juya ga Ummuna A’isha ta gaya mata maganganu masu zafi. Nana A’isha ta mayar mata daidai da irin yadda ta fada mata ba tare da ta rage ba har sai da Ummuna Zainab ta yi shiru ta rasa abin cewa; sai Annabi SAW Ya kalli Nana Aisha RA ya ce: “Tabbas ita ’yar Abubakar ce!“
Darussan da za su amfani maigida daga wannan hadisi wajen zama da mata sama da 2 sun hada da: *Ba laifi don mata biyu ko uku sun hade ya zamana sun fi shiri da juna indai ba da nufin cutarwa ga sauran kuma ba yawan cece-kuce a dalilin hakan kamar yadda wannan hadisi ya nuna.
*Darasi na 2 shi ne, maigida yana iya yin shiru ba lallai sai ya tanka ga yawan korafe -korafe daga wajen matansa ba; watau har sai in korafin ya wuce kima, sai ya amsa da amsar da za ta yi maganin wannan korafi ya kasance ba zai sake bayyana da wannan siga ba.
*Sannan ba daidai ba ne hana wa daya daga cikin mata wata rahma da Allah Ya zabe ta da ita da bai ba sauran matan ba. Idan muka lura ai Allah ne ya zabi Aisha RA ta zama mowa. Manzon Allah SAW kuma kuma cikin ikonsa ne Sahabbai RA suka ga ya fi dacewa su aika masa kyauta in yana gidanta, don haka ba a shiga hakkin sauran ba.
*Sannan abu na uku shi ne, maigida yana iya kyale wasu daga cikin matansa su yi musayar magana don wacce ake zargi ta fitar da kanta daga zargi ko don a samu karin fahimtar juna kan wata mas‘ala.
*Sannan bai kamata maigida ya tsaya yana musayar maganganu marasa dadi da wata daga cikin matansa ba, shiru ko lafazi kwakkwara daya zuwa biyu shi ya fi dacewa. Don haka akwai alamar tambaya ga mazantakar namijin da zai tsaya yana cacar baki da daya ko sama da haka daga cikin matansa.