Dabarar rashin dabara irin ta Tony Anenih

An ce jam’iyyar PDP tamkar zabuwar da ba ta iya goge zanen jikinta ba ce.  Shi ya sa ake yawan zarginta da aikata laifuffukan da take yawan kwatawa, amma kuma ta kasa dainawa.  Babbar illar wannan jam’iyya, kamar yadda ‘yan siyasa ke kuka da ita shi ne, rashin bin  ka’idojin gudanar da jam’iyyar ko kuma […]

Dabarar rashin dabara irin ta Tony Anenih
Dabarar rashin dabara irin ta Tony Anenih

An ce jam’iyyar PDP tamkar zabuwar da ba ta iya goge zanen jikinta ba ce.  Shi ya sa ake yawan zarginta da aikata laifuffukan da take yawan kwatawa, amma kuma ta kasa dainawa.  Babbar illar wannan jam’iyya, kamar yadda ‘yan siyasa ke kuka da ita shi ne, rashin bin  ka’idojin gudanar da jam’iyyar ko kuma kawar da ita daga tafarkin dimokuradiyya a dukkan lokutan da shugabanninta suka nemi  biye wa son zukatansu  don daure wa karya gindi. A  dukkan lokutan da aka tashi yin zabe a jam’iyyar akan hana ruwa gudu  ta hanyar kaurace wa jefa kuri’u don wasu wakilan ‘ya’yan jam’iyyar su darje wanda suke gani shi ya fi cancanta  a tsayar  a zaben gama-gari, yayin da za a yi ta kawo batutuwan tsayar da dan takarar  da shugabanni za su ce  shi ne bakinsu ya zo daya game da dacewarsa, kuma a kan haka za a tsaya ba lallai sai an jefa kuri’a ba.
Wannan babbar matsala ce da jam’iyyar PDP ta haifar a fagen siyasar kasar nan, wasu jam’iyyun kuma suka yi koyi da ita, har ma suka fi mai kora  yawan shafawa. Dangane da haka ne harkokin siyasa suke kasa yin armashi, aka bar siyasar akida aka rungumi ta kudi, cuwa-cuwa da ha’inci suka kankama,  aka kuma  rika samar da wakilai ko shugabanni marasa inganci, wadanda ba su san makamar mulki  ko nakaltar dabarun muhawara a majalisa ba. Ta haka ne wahaloli suka sauko wa kasar  kamar dango, aka kuma kasa gano hanyoyin  kawar da su.  Ga shi nan yanzu sun gawurta, sun kasaita, sun kuma  addabi kowa da kowa.
To amma duk da haka nan ‘yan siyasa ba su daddara ba, suna nan kan  bakarsu ta ci gaba da assasa wadannan dalilan da suka janyo aka yi tsalle guda aka shiga uku, ga shi nan an yi fiye da dubu ba a fita ba. Da farko dai gwamnonin jihohi su ne  tushen dukkan matsalolin siyasar da ke wahalar da kasar nan. Su ne suke nada wakilai  daga jihohinsu  zuwa manyan tarurrukan jam’iyyu don fitar da ‘yan takarar shugabancin kasa ko na gwamnoni,  maimakon su bari jama’a su zabi son ransu. Haka nan kuma wadannan gwamnonin ne ke dagewa don yin  aringizon kuri’u wajen tabbatar da nasara ga ‘yan takarar da suka shafe da mai. To ba  a nan ba kadai suka tsaya;  babu wani dan majalisa, walau na jiha ne ko na tarayya da zai yi galaba a zabe ba tare da sa hannun gwamnar jiharsa ba, walau ta ingantacciyar turba  ko ta barauniyar hanya.  
Wannan ne ya hana majalisun kasar nan katabus, domin gwamnoni da shugaban kasa sun  mayar da su ‘yan amshin Shata, sai irin dokar da suke so za a kafa, sai kuma yadda suke so za su karkata akalar majalisun, alhali gashin kansu suke ci, ba zaman gwamnonin suke yi ba. Dangane da haka ne gwamnoni suka zamanto gagarabadau a jam’iyyunsu, sa’anan kuma suka kafa kungiyar da ake amfani da ita don daure wa wanda ake so gindi don tsayawa takara ko don samun nasarar zabe.  Ga dai misalai  nan an sha gani game da irin rawar da wannan kungiyar ke takawa game da haka.
To shi ne kuma a halin yanzu wani jigo a jam’iyyar PDP, Chief Tony Anenih, mutumin da ‘yan siyasa ke yi wa kirari, “jaba sa baki a bar miki dole” a dukkan harkokin siyasa ya sake takalo batun da ya yi wa daukacin ‘ya’yan jam’iyyar kuna, wanda kuma aka dade ana kuka game da shi don tasirinsa wajen dagula al’amura. Ana iya cewa santin abincin da ya ci ne a wajen wata  liyafa a fadar Shugaban kasa ta kai Cif Anenih takalo batun kokarin da jam’iyyarsa ke yi don tabbatar da cewa an sake tsayar da shugaban kasa da gwamnonin da ke kan gado na jam’iyyar PDP, masu iya sake wa’adi guda, ba tare da sun yi gogayya da masu sha’awar takarar mukaman ba. A takaice dai ana iya cewa Cif Anenih na so ne ya kwance tsohon gyambon da hatta kotunan kasar nan ma sun nemi a bar shi a daure don ya ji dadin warkewa. Dalili kuwa shi ne dokokin zabe  ba su amince da tsayar da dan takarar kowane irin zabe ne ba da sunan daidaiton bakin manyan jam’iyya wajen cancancarta ba tare da ya fafata da sauran masu neman a tsayar da su ba. Wannan ne ya sa ko da kuwa an samu dan takara, guda daya, tilo, ba abokan hamayya, sai wakilai sun jefa kuri’ar amincewa da shi ko akasin haka.
Wasu na cewa ai ko a kasar Amurka, inda muka aro dimokuradiyya, akan ba shugaban kasa ko gwamna damar tsayawa ba tare da yin takara da wasu ba, muddin dai yana da ‘yancin sake tsayawa, ya kuma nuna sha’awar yin haka. To a dimokuradiyyar  Amurka ana iya yin haka, amma ba a Najeriya ba, inda tilas ne a tabbata an ba masu zabe da masu sha’awar tsayawa takara hakkokinsu, ba wai a tsaya ana kumbuya-kumbuya ba don lalubo wanda za a shafe da mai don tsayawa takara. Saboda haka tilas ne jam’iyar PDP ta sake tunani, ko kuma ‘ya’yanta su tayar da kayar baya wajen yakar wannan  manufar da aka dade da tabbatar da cewa tauraruwa mai wutsiya ce, ganinta ba alheri ne ba.