Dabarun farfado da tattalin arzikin kasa
A dan karamin sanina da Allah ya ba ni a fanin tattalin arziki na gano wasu dabaru hudu, wadanda da zarar an bi su za a ceto tattalin arzikin kasar nan daga durkushewa a kasa warwas. Na farko: Ya zama wajibi matukar ana son a ceto tattalin arzikin Najeriya a koma ga fannin noma da […]
A dan karamin sanina da Allah ya ba ni a fanin tattalin arziki na gano wasu dabaru hudu, wadanda da zarar an bi su za a ceto tattalin arzikin kasar nan daga durkushewa a kasa warwas.
Na farko: Ya zama wajibi matukar ana son a ceto tattalin arzikin Najeriya a koma ga fannin noma da kiwo, kamar yadda Najeriya ta kasance a shekarar 1960 zuwa 1967, a shekaru bakwai din can na baya, Najeriya ta dogara ne da noma da kiwo, kuma a yankin Arewacin kasar a kan samar da abubuwa kamar su noman gyada da auduga da alkama da fatu da kiraga da shinkafa da dai sauransu. Wadannan muhimman abubuwa da kudin su ne aka tono man fetur din da kowa yake tinkaho da shi. Don haka ya zama wajibi idan ana son ceto kasar nan ta koma kan wadannan muhimman abubuwa.
Na biyu: Ya zama wajibi a yankin Arewacin kasar a tono ma’adanan da Allah ya ba mu, musamman ganin yadda Allah ya arzurta mu da ma’adanai iri-iri, wadanda suka hada da kwal da azurfa da zinare da farar kasa da dai sauransu.
Na uku: Ya zama wajibi a gyara masana’antun mu domin rage yawan abubuwan da ake shigowa da su kasar nan, saboda kusan kashi 95 cikin 100 na abin da muke amfani da shi a Najeriya shigowa da shi ake yi da shi. Kuma hakan ba karamar barazana ba ce ga tattalin arzikin mu. Saboda babu wata kasa a duniya da za ta ci gaba matukar yawan abin da take shigowa da shi ya fi wanda take fitarwa. Sannan idan aka gyara su za a samar wa matasa aikin yi.
Na hudu: Na karshe, shi ne, ya zama wajibi a daina al’mundana da kudin kasa saboda babu kasar da tattalin arzikin su zai ci gaba matukar kasar tana fama da matsalar cin hanci da rashawa kuma a rage hidindimun da ake yi wa masu rike da mukamin siyasa kamar albashin su da kuma alawus-alawus din su saboda duk duniya babu kasar da ’yan majalisun su suke daukar albashi kamar na Najeriya.
Da fatan Shugaba Muhammadu Buhari zai duba wadannan dabaru hudun da na kawo a dan karamin alimin da Allah ya ba ni a fanin tattalin arziki.
Jingir dalibi ne a tsangayar nazarin tattalin arziki a Jami’ar Musulunci da ke Katsina kuma Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Filato.08067922200 [email protected]