Dabarun girki da mata da yawa ba su sani ba

Dabarun da ke amfani da su a ɗakin girke-girke waɗanda idan idan uwar gida ta bi…

Dabarun girki da mata da yawa ba su sani ba

Asalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci, a yau Aminiya ta kawo muku wasu dabarun da ke amfani da su a ɗakin girki, waɗanda idan idan uwar gida ta bi su, insha Allah za ta samu sauƙi da nasarra girkinta.

Ga wasu daga ciki:

Idan kina so ki dafa shinkafarki ta yi wara-wara, to sai ki wanke ta da gishiri, ko ki jika ta a ruwan ɗumi tsawon minti 30 sannan ki dafa.

Idan kuma kina so shinkafar ta yi haske, sai ki ɗan sanya lemon tsami a cikinta, ki tafasa ta, sannan ki ɗauraye, ki mayar kan wuta ta nuna.

Idan farar shinkafa mai karas da “peas” da “green beans” za ki dafa, to sai ki tafasa su a wuri daya, ki sa musu baking powder ki rufe na minti 5, idan sun nuna sai ki tace ruwan zafin ki ɗauraye, ki zuba su a cikin dafaffiyar shinkafarki, za ki ga launin ya fito kuma shinkafar ta yi kyau.

Idan ba ki so kiji yaji a idonki idan kina yanka albasa, to sai ki riƙa tauna cingam ko ki sanya gilashi idan za ki yanka albasa.

Idan kin ƙone da ruwan zafi ko mai mai zafi, kafin komai, ki fara shafa ɗanyen kwai ko ruwan kanwa, in sha’a Allahu wurin ba zai tashi ba.

Idan kina so ki dafa taliyarki ta yi wara-wara, to sai ki tafasa ta da man gyaɗa kamar kokali ɗaya, ki bari ta yi rabin dahuwa, sannan ki wanke sai ki tsiyaye da gwagwa, sai ki canza ruwan, ki mayar da ita kan wuta har sai ta nuna sosai.

Idan miyarki ta yi ruwa, sai ki dan daka dafaffiyar doya ko dankali ki zuba a ciki hakan zai sa miyar ki ta koma yadda kike so.

Idan kina so ki dafa kowane irin ganye, alayyahu, salak, cabbage da sauransu, banda ganyen yauƙi, to sai jika ganyen a ruwan dumi da gishiri, ki ɗauraye sai ki yayyanka a ki sa a girkinki.

Idan kin yanka albasa ko tafarnuwa, kiyi sauri ki wanke hannunki da lemun tsamu saboda gudun wari.

Idan ki gama dafa abinci kuma kina so ya yi ƙamshi sosai, to sai ki soya albasa da tarugu da citta da tafarnuwa da “thyme”, sai ki zuba kori, da albasa da tattassai a ƙarshe cikin abincinki.

Idan miyarki ta yi tsami, ki zuba sukari a ciki zai kashe tsamin.

Idan kuma gishiri ne ya yi yawa a cikin abinci, shi ma sai ki dan zuba sukari, abincin zai dawo daidai.

Ki sani cewa kanwa tana rage wa abinci dandano, don haka a rage zuba kanwa da yawa a cikin abinci.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta