Dabarun neman bayanai masu inganci a Intanet (2)

8.    Nau’in BayanaiAkwai wasu bayanai masu inganci da galibi ake taskance su a wani nau’in jakar bayanai (wato: File type).  Misali, galibin kasidun binciken ilimi na jami’a ana samunsu ne a nau’in jakar bayanai na “Portable Document Format,” ko “pdf” a gajarce.  Galibin darussan malaman jami’a (Lesson Notes) kuma sukan taskance su ne a yanayin […]

Dabarun neman bayanai masu inganci a Intanet (2)

8.    Nau’in Bayanai
Akwai wasu bayanai masu inganci da galibi ake taskance su a wani nau’in jakar bayanai (wato: File type).  Misali, galibin kasidun binciken ilimi na jami’a ana samunsu ne a nau’in jakar bayanai na “Portable Document Format,” ko “pdf” a gajarce.  Galibin darussan malaman jami’a (Lesson Notes) kuma sukan taskance su ne a yanayin “Power Point” ko “ppt” a gajarce.  Wannan ya fi fa’ida ga daliban ilimi da ke son samun bayanai masu alaka da abin da suke karantawa a jami’a don warware wasu mas’alolin ilimi.  Misali, idan dalibi na son samun kasidu kan tattalin arzikin kasa, amma wadanda aka rubuta su da kwarewa irin ta ilimi (Research Papers), sai ya rubuta:
Filetyp:pdf welfare economics
Nan take za a turo masa kasidu masu take kan fannin “Welfare economics” a yanayin pdf, sai ya saukar.  Idan kuma yana son samun samfurin darussan malaman jami’a kan fannin, sai ya rubuta:
Filetype:ppt welfare economics
Har wa yau, akwai wata kasida da na rubuta a shekarar 2010 kan kabilar Fulani, mai take: “The Cattle Compled Theory”.  Idan mai karatu na son isa ga kasidar kai tsaye, sai a rubuta:
Filetype:pdf The Cattle Compled Theory
Bayan nau’ukan jakar bayanai na pdf da ppt, akwai su word (doc ko docd), da edcel (dls ko dlsd), da html, da kuma tedt (tdt).  
9.    Alamar Zabi (wannan ko wancan)
Alama ko harafin “OR” (da manyan harafi) na taimaka wa mai bincike ne wajen gaya wa masarrafar nemo bayanai na kamfanin Google cewa: “Kalma kaza nake nufi ko kaza,” a misali.    Ana rubuta wannan harafi na OR ne a tsakiyar kalmomin guda biyu.  Mu kaddara ana son bayanai masu dauke da kalmar “Gold” ko kalmar “Silber,”  sai a rubuta:
gold OR silber
Nan take za a samu bayanai masu dauke da dukkan kalmomin biyu, ko dayan cikinsu.  Wannan alama ce ta zabi.  Haka idan ana son mai dauke da kalmar “Islam” ko “Muslim,” sai a rubuta:
islam OR muslim
Nan take za a dace da kowanne.  Ko ana son mai dauke da sunan “Baban Sadik” ko “Baban Sadik” sai a rubuta:
baban sadik OR baban sadik
Babbar fa’idar wannan alama wajen bincike shi ne, tana bayar da damar fadada bayanai ne, da kuma samar da zabi; mai bincike bai takura kansa ba, sannan kuma zai samu bambancin da ke tsakanin kalmomi ko maudu’in ilimi guda biyu masu kama ko masu akasin juna.
10.     Neman Ma’anar Kalma
Masarrafar binciken bayanai na Google wani kamus ne mai zaman kansa.  Idan mai karatu na tare da kwamfutarsa mai jone da Intanet ko wayarsa ta salula, kada wata kalma ta Turanci ko Larabci ta ba shi tsoro.  Idan ana bukatar sanin ma’anar wata kalma, sai a yi amfani da alamar  “define” a biye ta da kalmar da ake so.  Misali, ana son sanin ma’anar kalmar “Islam,” sai kawai a rubuta:
define:islam
Kada a bar tazara a tsakanin alamar “define” da alamar “ruwa biyu” da kalmar da ake son sanin ma’anarta.  Nan take za a samu ma’anar kalmar a shafin farko daga sama.  Wani abin sha’awa ma shi ne, ba wai ma’anar a rubuce ba kadai, za a samu ma’anar a sauti, da bidiyo, da hotuna.  Dankari! 11.     Lissafi
Bayan sanin ma’anar kalma, masarrafar Google ma taska ce ta lissafi.  Mu kaddara mai karatu na son sanin amsar wata ka’ida ta lissafi (Ekuation), yana iya rubuta ta kai tsaye a inda ake shigar da kalma.  Misali, ga wata ka’ida nan:
(3 + 7) * (8 / 2)
Da zarar an shigar da wannan ka’ida ta lissafi aka danna “Enter”, nan take amsar za ta bayyana.  (amsar ita ce: 40.  Saboda 3 + 7 = 10. Sannan 8 / 2 = 4 ne.  Kuma 10 d 4 = 40 ne).  Ba wannan kadai ba, duk lissafin da mai karatu ke son aiwatarwa, ana shigarwa nan take za a ga amsa.  Abin gwanin ban sha’awa.
12.     Ma’aunin Tazara, da Zafi, dsr
Masarrafar Google taska ce da ke tattare da ma’aunin tazara da yawa ko kimar abubuwa (Unit Conbersion).  Misali, idan ana son mayar da tazarar tafiya daga mil (mile) zuwa kilomita (kilometer), abu ne mai sauki.   Mu kaddara mai karatu ya yi tafiya daga Abuja zuwa Birnin Dabo (Kano), sai motarsa ta ba shi tazarar a mil 197 (197 miles), maimakon kilomita.  Don sanin yawan kilomitan, sai a rubuta:
197 miles in kilometers
Nan take za a juyar da wannan tazara daga mil zuwa kilomita.  
Kammalawa
Wadannan kadan ne daga cikin dimbin dabarun da masana ke amfani da su wajen neman bayanai wadanda suka saba wa hanyar da aka saba amfani da ita a al’adance, ta Google.  Da wadannan ma kadai, mai karatu na iya hada dabaru uku ko hudu cikin bincike daya, don samun amsa mai kayatarwa.