Dabarun ‘yan dandatsa (hackers) da hanyoyin dakile su (II)

Darasi Na (02): “Scanning Networks” Darasi Na (03): “Enumeration”A darasin baya mai karatu ya ji bangarorin dake cikin darasin, da hanyoyinda ake bi wajen tantance na’urori da hanyoyin sadarwar dake dauke kan wani zangon sadarwa.   A darasi  na uku mai  take: “Enumeration,”  cikin fannonin dake karkashin “Ethical Hacking,” dalibi zai koyi yadda ake isa ga […]

Dabarun ‘yan dandatsa (hackers) da hanyoyin dakile su (II)

Darasi Na (02): “Scanning Networks”

Darasi Na (03): “Enumeration”A darasin baya mai karatu ya ji bangarorin dake cikin darasin, da hanyoyinda ake bi wajen tantance na’urori da hanyoyin sadarwar dake dauke kan wani zangon sadarwa.   A darasi  na uku mai  take: “Enumeration,”  cikin fannonin dake karkashin “Ethical Hacking,” dalibi zai koyi yadda ake isa ga hakikanin kafofin sadarwar dake kwamfuta ne, kai tsaye.  

Wannan shi ne matakin dake biye da matakin darasin baya, wato: “Scanning Networks.”Tsarin “Enumeration”Asalin kalmar “Enumeration” na ishara ne ga tsarin kididdige abubuwa ta hanyar sanya musu alama. karkashin wannan darasi na uku, dalibi zai koyi yadda ake isa ga kafofin sadarwar dake kwamfuta, wanda a baya ya samu bayani kan yadda ake gano kafofin, tsakanin wadandan ke bude da wadanda suke kulle. Da masu dauke da wata manhajar sadarwa (NetworkSerbice) da wadanda suke holoko; babu komai a cikinsu.  Kafofin sadarwa, wato:   “System Ports” hanyoyi ne da kwamfuta ke   bi wajen aiwatar da sadarwa tsakaninta da kwamfuta ‘yar uwarta, ta hanyar wasu kananan manhajoji dake kafofin, wato: “Network Serbice.” Shahararru daga cikin wadannan kafofin sadarwa dai sun   hada da: “TCP/UDP 53,” wadda kafa ce dake dauke da tsarin “DNS Zone Transfer”da “UDP 161”, wadda ke dauke da tsarin “Simple Network Management Protocol” (SNMP), wanda tsari ne dake taimaka wa wajen lura da zangon sadarwa dake dauke da na’urori da hanyoyin sadarwa. Sai kafa mai suna: “TCP/UDP 389” mai dauke   da tsarin “Lightweight Directory AccessProtocol” (LDAP) wanda ke  taimakawa wajen tantance gungu-gungu na matattarar bayanai dake zangon sadarwa.  

Sai kafar “TCP 25”, wadda ke dauke da manhajar   karba da aika sakonnin Imel, wato: “Simple MailTransfer Protocol” ko “SMTP” a gajarce. Wannan ka’idar sadarwa ce ke lura da sakonnin Imel dake shigowa cikin kwamfuta a yayin da aka aika su. Sannan ta wannan   kafa, dan dandatsa na iya kutsawa cikin kwamfuta don aiwatar da aika-aikarsa. Sauran kafofin sadarwar sun hada da: “UDP 137” da “TCP 139” wadanda ke dauke da tsarin “NetBIOS Name Serbice” (NBNS) da kuma “NetBIOSSession Serbice” (SMB ober NetBIOS).  Sai kafa mai suna: “TCP/UDP 135”mai dauke da manhaja ko tsarin   sadarwa mai suna: “Microsoft RPC End point Mapper.” Wadannan  su ne shahararrun kafofin sadarwa dake dauke cikin kwamfuta wadanda dalibi zai koyi yadda ake iya isa gare su cikin sauki. Daga   cikin abin da dalibi zai koya a wannan darasi na   “Enumeration” akwai hakikanin abubuwan da ke dauke cikin wadannan kafafen sadarwa da bayaninsu ya gabata a sama. 

Daga cikin mahimman abubuwan da ke dauke cikinsu akwai jerin sunayen kwamfutocin dake zangon sadarwa, da jerin gungun masu   amfani da kwamfutocin dake zangon, wato: “User Domain”. Da   tsarin isa ga nau’ukan bayanan dake dauke cikin kwamfutocin da dai sauransu. Manhajojin “Enumeration” Daga cikin shahararrun   manhajojin da ake amfani da su wajen shiga wadannan kafofin sadarwa da dalibi zai koya karkashin wannan darasi dai akwai manhajar “Super Scan” wacce ke iya zakulo dukkan kafofin sadarwar dake dauke kan kwamfuta, tare da manhajojin dake cikinsu, da sunayen da ke kwamfutar (usernames) da dai sauran bayanai. 

Sai manhajar “Hyena,” da manhajar “WinFingerPrint”, wacce ke iya tantance maka jerin sunayen (username accounts) da ke kan   kwamfuta ko wani zangon sadarwa. Wasu daga cikinsu sun hada da:   “Nbtstat” da ke babbar manhajar Windows, da “Net biew”, da “Net Use”, da “NetScanTools Pro”, da “DumpSec”, da “NessusWd”, da kuma manhajar “Hunt.”  Wannan jeri ne na wasu !tinannun manhajoji da ake amfani da su   don aiwatar dawannan aiki na riskar kafofin sadarwar kwamfuta. Bayan wadannan, akwai jerin manhajoji dake taimaka wa Uban Zangon Sadarwa (Network Adminstrator) wajen tayar da kwamfutoci  a zangon sadarwa. Wadannan jerin manhajoji dai Mark Russonobich ne ya gina su.Ya gina jerin wadannan manhajoji ne sadda yake aiki   da kamfanin Microsoft, cikin gungun kwararrun dake aiki kan   babbar manhajar kwamfuta. Wadannan manhajoji ya sanya musu   suna: “SysInternalsSuite.” Manhajoji ne sama da 40. Shahararru daga cikinsusu ne: “PsEdec”, da “PsList”, da “PsFile”, da PsLoggedOn”, da PsGetSid”,da “PsLogList”, da “PsKill”, da “PsPassword”, da   “PsInfo”, da kuma“PsShutdown.”Wadannan jerin hadakar manhajoji ne da ake amfani da su wajen isa ga kafofin sadarwar dake  kwamfuta, don tatsar nau’ukan bayanan da suka sha masu amfani da ita a zangon da take. 

Hanyoyin Kariya Kasancewar wadannan kafofin sadarwa na kwamfuta suna dauke ne da manhajoji, hanyar kare su daga aika-aikar ‘yan dandatsa sun ta’allaka ne ga sabunta zubinsu a kowane lokaci, da kuma canza tsarin da manhajojin suka zo da su,   wato: “Default Settings.” Domin kasancewar galibin kamfanoni a baya su cika canza tsare-tsaren manhajojin da suke amfani da su a zangon sadarwa ba, ya sa ‘yan dandatsa ke kirdadon tsarinsu na asali, idan ma masu dauke da kalmar sirri ne, kamar na’urar Router misali, sukan yi kirdadon asalin kalmar sirrin da kamfanonin da suka kera suke ba su, don samun isa gare su. Rashin canza wadannan kalmomin sirri, da rashin canza hakikanin tsarin da manhajar ko na’urar ta zo da su ma ya na haddasa barna mai yawa ta bangaren ‘yan dandatsa. A darasi na hudu da za mu kawo mako mai zuwa, mai karatu zai ji bayani kan yadda ake kutsawa cikin kwamfutar dake zangon sadarwa, da yadda ‘yan dandatsa ke mallake kwamfutar bayan sun samu shiga cikinta, da irin dabarun da suke amfani da su wajen boye sawunsu bayan sun gama gudanar da aika-aikarsu. Wannan darasi shi ne ake kira: “System Hacking.”

bdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

08034592444 (tes kawai), [email protected]

http://fasahar-intanet.blogspot.com