Dabarun ‘yan dandatsa (hackers) da hanyoyin daqile su (II)
Sai Manzon Allah (SAW) ya umurta da a yi kisasi. Anas ya ce: “Ya Manzon Allah! Ina rantsuwa da Wanda ya aiko ka da gaskiya ba za a karya mata hakori ba saboda ramuwa. Suka yarda da biyan diyya a maimakon ramawa. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai daga cikin bayanin Allah akwai wanda […]
Sai Manzon Allah (SAW) ya umurta da a yi kisasi. Anas ya ce: “Ya Manzon Allah! Ina rantsuwa da Wanda ya aiko ka da gaskiya ba za a karya mata hakori ba saboda ramuwa. Suka yarda da biyan diyya a maimakon ramawa. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai daga cikin bayanin Allah akwai wanda da zai rantse da Allah sai Ya barrantar da shi (daga kaffara).”
497. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Isma’il ya ba mu labari ya ce, dan uwana ya ba ni labari daga Sulaiman ina tsammaninsa daga Muhammad dan Abu Ateek daga dan Shihab daga Kharijat dan Zaid cewa: Lallai Zaid dan Sabit (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na bincika wasu ayoyi daga takardun Alkur’ani don rubutawa sai na rasa wata aya daga cikin suratul Ahza’ab wacce na kasance ina jin Manzon Allah (SAW) yana karanta ta, ban same ta ba face wajen Khuzaimat dan Sabit mutumin Madina wanda Manzon Allah (SAW) ya sanya shaidarsa tana daidai da shaidar mutum biyu. Kuma ayar ita ce, fadar Allah Madaukaki cewa: “Daga cikin mummunai akwai wasu mazaje wadanda suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkawari a kansa….(33:23).”
BABI NA GOMA SHA UKU:-
Gabatar da aikin kwarai kafin zuwan yaki. Abu Darda’ ya ce: “Amma ku sani kuna yakar kafirai ne bisa kyawon aikinku.” Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Don me kuke fadar abin da baku aikatawa. Ya girma ga zama kyama a wurin Allah, ku fadi Abin da ba ku aikatawa…Lallai Allah na son wadanda suke yaki bisa daukaka kalmarSa a cikin sahu kamar su gini ne, mai damfarar juna (61:2-4).”
498. An karbo daga Muhammad dan Abdurrahim ya ce: “Shababat dan Sawwar Alfazzari ya ba mu labari ya ce, Isra’il ya ba mu labari daga Abu Is’hak ya ce: “Na ji Barra’u (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Wani mutum ya je ga Annabi (SAW) mai damarar yaki na bakin karfe. Ya ce, “Ya Manzon Allah! yakin zan fara ko musulunta zan fara? Ya ce, “Ka musulunta, sannan ka fita yaki. Sai ya musulunta sannan da aka fita yakin ya yi ta yakin aka kashe shi (ya yi shahada).” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya yi aiki karami amma an saka masa da lada (sakamako) mai yawa.”
BABI NA GOMA SHA HUdU:-
Wanda aka kashe ta hanyar harbin kan mai uwa da wabi,(ba a san wanda ya harbe shi ba).
499. An karbo daga Muhammad dan Abdullahi ya ce: “Husain dan Muhammad Abu Ahmad ya ba mu labari ya ce, Shaiban ya ba mu labari daga katada ya ce, Anas dan Malik ya ba mu labari cewa: Lallai Umma Rubayyi’a diyar Barra’u ita ce, uwar Haris dan Surakat ta je ga Annabi (SAW) ta ce: “Ya Annabin Allah! Shin ko za ka ba ni labari game da matsayin Harisa? Saboda ya kasance an kashe shi ne a ranar Badar wani harbi kan mai uwa da wabi ya same shi. Idan na cikin Aljanna ne, sai in kara hakuri, idan ba haka ba ne sai in kara kuka a kansa. Sai (Annabi) ya ce: “Ya Umma Harisa, ita Aljanna yawa gare ta, kuma lallai danki ya samu Aljannar Firdausi madaukakiya.”