Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji

Babban Limamin Masallacin Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi  Mukaddima: Bayan haka ya bayin Allah! Daga cikin muhimman lokuta na yin ibada akwai ranaku 10 na farkon watan Zul-Hajji – wata na 12 na shekarar Musulunci, wadanda Allah Ya fifita a kan sauran kwanaki na shekara. Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani […]

Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji

Babban Limamin Masallacin Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi 

Mukaddima:

Bayan haka ya bayin Allah! Daga cikin muhimman lokuta na yin ibada akwai ranaku 10 na farkon watan Zul-Hajji – wata na 12 na shekarar Musulunci, wadanda Allah Ya fifita a kan sauran kwanaki na shekara.

Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani aiki da ya fi alheri irin wanda aka yi a ranaku 10 na farkon Zul-Hajji.” Sai wadansu sahabbai suka ce: “Koda jihadi a tafarkin Allah?” Annabi (SAW) ya ce: “Koda jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya tafi da kansa da dukiyarsa bai dawo da komai ba.” (Buhari). 

Wadannan kwanaki goma manya ne kuma mafiya soyuwa ne a wurin Allah. Ibn Umar (RA) ya ruwaito cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Babu wasu ranaku da suka da girma kuma suka fi soyuwa a wurin Allah fiye da wadannan kwanaki goma na farko Zul-Hajji, don haka ku yawaita tahlili da takbiri da tahmidi a cikinsu” (Musnad Imam Ahmad). Kuma Sheikh Ahmad Shakir ya inganta shi.

Daga cikin darajojin da wadannan kwanaki goma suke da su akwai cewa:

1- Allah Yana yin rantsuwa da wani abu domin Ya nuna muhimmancinsa, kuma Allah Ya yi rantsuwa da wadannan ranaku goma a cikin Alkur’ani Mai girma inda ya ce: “Ina rantsuwa da alfijiri. Da darare goma.” (k:89:1-2).

Malamai magabata da suka hada da Ibn Abbas (RA) sun ce wadannan darare goma da aka ambata a cikin Alkur’ani su ne darare goma na farkon Zul-Hajji.

2- Annabi (SAW) ya ce wadannan darare goma su ne ranaku mafiya alheri na shekarar kamar yadda muka ambata a Hadisi na baya.

3- Su ne ranaku mafiya alheri na yawaita ambaton Allah, kamar yadda Hadisin da ya gabata ya nuna.

4- Sun kunshi ranar Arfa (9 ga Zul-Hajji) wanda a cikinta Allah Ya cika wannan addini. Kuma yin azumi a cikin wadannan ranaku yana kankare kananan zunuban shekarar da ta gabata da shekara da ake ciki, (manyan zunubai suna bukatar tuba da mayar da hakki ga mai shi). 

5- Sun kunshi ranar “Hajji Mafi girma” wato ranar Idin Layya (10 ga Zul-Hajji), kuma wannan rana ita ce rana mafi girma a daukacin shekara.

Don haka ku yawaita karatun Alkur’ani a cikinsu, ku yi sallolin nafila da kiyamul Laili da sadaka da yada ilimi da tuba ga Allah. Ku yawaita neman gafara ta fadin Astagfirulla, ku yi azumi da jikinku, ma’ana ku kaurace wa haram ko fadin haram ko sauraren haram da sauransu, kuma ku yi addu’o’i ga al’ummar Musulmin duniya.

’Yan uwa maza da mata! Ku yi gaggawar ribatar wadannan ranaku kafin lokaci ya kure muku.

Ya bayin Allah! A yau aikin da ya fi hada dukan Musulmi, matasa da dattawa, maza da mata, bakake da farare, kuma yake kawo farin ciki a fuskar kowa, shi ne ibadar Layya. Layya ibada ce ta sadaukarwa ta hanyar yanka dabbobi domin neman yardar Allah. Ana yin ta ce domin tunawa da wani muhimmin abin tarihi da ya auku a lokacin da Allah Ya umarci Sayyidina Ibrahim (AS) ya yi layya da dansa Sayyidina Isma’il (AS), kuma a lokacin da yake shirin aiwatar da umarnin Allah, sai Allah Ya musanya masa da rago wanda Sayyidina Ibrahim (AS) ya yanka.

Sayyidina Ibrahim (AS), ya ci jarrabawa, domin ya shirya don yanka dansa saboda bin umarnin Allah. Abokaina yanzu kuna jin wahala ku yi layya da dabba (ta amfani da kudinku) don bin umarnin Allah? Bai kamata ni da ku mu kasa cin wannan jarrabawa ba. duk wanda yake da hali ya yi layya a madadin iyalinsa.

’Yan uwa maza da mata! Za a iya yanka Layya a kowane lokaci bayan Sallar Idi har zuwa faduwar rana ta uku a bayan ranar Idin. Wannan na nufin wuni hudu (wunin Idi da karin wuni uku). Kamar yadda Imam Shafi’i ya nuna. Amma a fahimtar sauran manyan malamai: Abu Hanifah da Malik da Ahmad, ana yin layya ce a cikin wuni uku. A fara da ranar Idi a kare a wuni na biyu bayan wunin Idi lokacin faduwar rana.

Ana iya yanka Layya da rana ko da dare, matukar dai a cikin wadannan ranaku ne, amma yin ta da wuri (jim kadan bayan Sallar Idi) ya fi.

Sunnar Layya ita ce a raba naman uku, kuma ba tilas ba ne a raba daidai-wa-daida. daya a raba wa talakawa da mabukata, dayan a bar wa iyali da makwabta da dangi da abokai, dayan kuma ka yi yadda ka so da shi.

Layya Sunnah ce mai karfi a kan kowane Musulmi mai hali. Wannan shi ne ra’ayin akasarin malamai. Amma a wurin wadansu malaman wajiba ce a kan Musulmin da zai iya. Kuma tana daya daga cikin kyawawan ayyuka a Musulunci kamar yadda A’isha (RA) ta ruwaito daga Annabi (SAW) cewa: “dan Adam bai taba yin wani aiki a ranar Layya da ya fi soyuwa a wurin Allah ba, kamar zubar da jini (yankan Layya).”

Galibin malamai sun ce yanka Layya ya fi alheri da yin sadaka da kwatankwacin kudin abin abin yankar.

Ya ’yan uwa! Ana yin Layyan ne da dabbobin gida wato shanu da rakuma da tumaki da awaki. Kuma yanka rago/tunkiya da bunsuru/akuya ya fi a kan sauran dabbobin, saboda Annabi (SAW) bai taba yin Layya ba face da wadannan dabbobi. Amma ana iya yanka rakuma da shanu lokacin Layya.  Kuma wajibi ne abin yankan ya kasance lafiyayye, kosasshe da za a iya cin namans a matsayin ibada ga Allah kamar yadda Allah Ya ce: “Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne ita (girmamawar) tana daga ayyukan zukata na takawa.” (k:22:32).

Kuma wajibi ne idan rago ne ko tunkiya su haura wata shida kamar yadda Ibn Majah ya ruwaito cea sai Jaza’a za a yi Layya da ita. Ga jinsin akuya wajibi ne ya kai shekara daya, sannan saniya shekara biyu, shi kuma rakumi shekara biyar.

Kuma kada a yi Layya da nakasasshiyar dabba, kamar mai ido daya ko marar lafiya ko gurguwa da hakan ya bayyana ko ramammiya marar nama kamar yadda Buhari ya ruwaito daga Barra’u bin Azib daga Annabi (SAW).

Kuma mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa siffofi hudu da aka ambata a Hadisin za a iya amfani da su wajen hukunci kan duk wata nakasa. Don haka duk wata nakasa da ta kai ta ko ta fi ta ba za a yi Layya da dabbar ba, kamar makauniya ko marar kafa daya.

Kuma ana iya Layya da dabbar da aka dandake, saboda Annabi (SAW) ya yi haka, haka dabbar da aka haifa ba ta da jela ko take da rabinta, amma wadda aka yanke jelarta duka ba za a yi Layya da ita ba.

Sannan tunkiya ko akuya daya ta wadatar mai gida ya yi Layya da ita ga kansa da iyalansa. Kuma ya halatta mutum bakwai su yanka saniya ko rakumi daya a matsayin layyarsu. Kamar yadda Jabir bin Abdullahi (RA) ya ruwaito cewa Annabi (SAW) ya yi haka a shekarar Hudaibiyya. (Muslim).

Kuma mai yin haka zai iya hadawa da iyalinsa a cikin ladan domin a nan daidai yake da mai yanka tunkiya ko akuya.

Kuma bai halatta a yanka Layya  kafin yin Sallar Idi ba, duk wanda ya yanka layya kafin Idi ya yanka wa iyalinsa naman sun ci ne amma ba Layya ba, kamar yadda Annabi (SAW) ya nuna. Kuma idan mutum zai yanka layyar ya ambaci sunan Allah, ya ce: “Bismillah, Ya Allah, wannan daga rahamarKa ce kuma dominKa ne.”

An fi so mutum ya yanka Layyarsa da kansa in ba zai yi haka ba, to ya halarci yanka, sannan ya raba uku kamar yadda muka ambata a baya. Ya ci rubu’i daya shi da iyalinsa, ya bayar da daya rub’in sadaka, dayan kuma ya yi kyauta da shi, kamar yadda Annabi (SAW) ya shaida wa ’yarsa Fatima (RA) cewa: “Ki kasance a lokacin da ake yanka Layyarki. Allah Yana gafarta miki a lokacin digar farko na jininta.” (Baihaki da Abdul Razzak).

 Hikimar hukunta Layya:

1 – Neman kusanci ga Allah ta hanyarta.

2 – Raya Sunnar Shugaban Masu Tauhidi Annabi Ibrahim (AS) wanda Allah Ya umarce shi ya yi Layya da dansa Annabi Isma’il (AS) sannan daga baya ya musanya shi da rago, kuma Annabi Ibrahim (AS) ya yanka shi a madadin Annabi Isma’il (AS) din.

3 – Yalwatawa da kyautata wa iyali a ranar Idi.

4 – Fadada jin dadi a tsakanin matalauta da mabukata ta hanyar ba su sadakar naman Layya.

5 – Yin godiya ga Allah kan yadda ya hore mana duka dabbobin ni’ima.

Abubuwan da wanda ya yi niyyar Layya zai guje musu:

Idan mutum ya yi niyyar zai yi Layya to da zarar wata Zul-Hajji ya kama ba zai yi aski ko ya yanke farce ba har sai ya yanka abin Layyarsa. Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa cewa Ummu Salma (RA) cewa, Annabi (SAW) ya ce: “Idan kuka ga jinjirin watan Zul-Hajji kuma dayanku yana da niyyar yin Layya, to kada ya aske gashinsa ko ya yanek farcensa.” (Muslim).

Haka kada a biya ladan mai gyara naman Layya daga abin Layya. Domin Aliyu bin Abu Talib (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya umarce ni da in lura da Layyar wani rakumi, in bayar da namansa da fatarta a matsayin sadaka kuma kada in bayar da komai daga cikinta ga mahauci a matsayin ladan aikinsa. Ya ce, “Zan iya ba shi wani abu daga abin da na mallaka.” (Muslim).

’Yan uwa maza da mata! Ina rokon Allah Madaukaki ya amsa min da kuma ku da sauran Musulmin duniya, kuma Ya sa dominSa kadai muke. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Ya Allah! Ka taimake mu wajen rayuwa bisa koyarwar Alkur’ani da Sunnah. Ya Allah Ka nuna mana gaskiya Ka ba mu ikon bin ta, kuma Ka nuna mana karya Ka ba mu ikon guje mata.

Ya Allah! Ka shiryar da mu, Ka kare mu daga ayyukan jahilci da barna. Ka kare mu daga gazawarmu. Ka sanya karshen ayyukanmu su kasance mafi alherinsu da dacewarsu. Kuma Ka gafarta mana Ya Ubangiji.

Ya ’yan uwa! Duk abin da na fadi mai kyau a Huduba ta yau daga Allah Madaukaki ne, kuma duk wani kuskure daga gare ni kuma muna neman tsarin Allah daga bayar da muguwar shawara da dukan barna da fitina. Kuma ina rokon Allah gafara idan na ketare iyaka a cikin duk abin da na ce ko na aikata.

Godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah da alayensa da sahabbansa.

Ina kammala wannan Huduba ina mai rokon Allah Madaukaki Ya gafarta mana zunbunamu. Ku nemi gafararSa, Lallai Shi Mai gafara ne Mai jin kai.

Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limanin Msallacin Juma’a na Nagazi-Ubete Jumu’ah da Masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene da suke Okene Jihar Kogi, ya gabatar da wannan Huduba ce a ranar Juma’ar da ta gabata 18 ga Agustan, 2017 daidai da 25 ga Zul-kida 1438 Bayan Hijira. Za a iya tuntubarsa ta tarho: +2348038289761.