Dabi Hernandez ya angwance

Shahararren dan kwallon FC Barcelona da kuma Sifen, dabi Hernanded a ranar Asabar da ta wuce ne ya auri ’yar jarida mai suna Nuria Cunillera a gaban baki 180 da suka halarci bikin.Bikin daura auren an yi shi ne a gaban manyan baki da kuma da yawa daga cikin ’yan kwallon Barcelona.Sai dai daya daga […]

Dabi Hernandez ya angwance

Xavi Hernandez tare da amaryarsaShahararren dan kwallon FC Barcelona da kuma Sifen, dabi Hernanded a ranar Asabar da ta wuce ne ya auri ’yar jarida mai suna Nuria Cunillera a gaban baki 180 da suka halarci bikin.
Bikin daura auren an yi shi ne a gaban manyan baki da kuma da yawa daga cikin ’yan kwallon Barcelona.
Sai dai daya daga cikin ’yan kwallon Barcelona Carlos Puyol bai samu halartar daurin auren ba saboda tun kafin a sanya ranar daura auren ya tafi balaguro da budurwarsa don hutawa kafin a fara kakar wasa ta bana.
Amaryar, ’yar kimanin shekara 31, ta fara soyayya da anganonta ne a lokacin da aka yi gasar cin kofin Nahiyar Turai (European Championship) da ya gudana a Poland da Ukraine.
Rahotanni sun tabbatar dan kwallon ya tafi gasar ce tare da budurwarsa kuma kasar Sifen ce ta samu nasarar lashe kofin.
Daga cikin manyan bakin da aka gayyata a lokacin bikin daura auren sun hada da Andres Iniesta tare da matarsa Anna sannan akwai Lionel Messi da matarsa Antonella, Dabid billa da matarsa Patricia, da kuma bictor baldes tare da matarsa.
Sai dai takwaransu golan Sifen Iker Casillas bai samu halartar bikin ba, don shi ma ya tafi balaguro tare da budurwarsa mai juna-biyu don hutawa kafin a fara kakar wasa ta bana.
Tuni ango da amaryar suka tafi kasar Seychelles don shakatawa kuma ana sa ran dabi zai dawo a ranar 29 ga watan nan don cigaba da shirin tunkakar kakar wasa ta bana a kulob din FC Barcelona.