dabi’u da nau’ukan sinadaran da ke cikin ruwa 01
Launi, da Dandano, da Kamshi Bayan haka, a karankanshi yana iya narkewa ne kadai (idan a sandare yake) a yanayi madaidaici. Ma’ana, idan ruwa yana yanayin kankara ne, idan aka kawo shi cikin yanayin mahalli (Temperature) madaidaici, nan take zai kama narkewa. Kamar yadda idan a yanayi mai zafi yake dabi’arsa na iya canzawa. Idan […]
Launi, da Dandano, da Kamshi
Bayan haka, a karankanshi yana iya narkewa ne kadai (idan a sandare yake) a yanayi madaidaici. Ma’ana, idan ruwa yana yanayin kankara ne, idan aka kawo shi cikin yanayin mahalli (Temperature) madaidaici, nan take zai kama narkewa. Kamar yadda idan a yanayi mai zafi yake dabi’arsa na iya canzawa. Idan zafin wuta ne, zai kara narkewa kuma nauyinsa (Density) ya karu saboda tasirin zafi. Idan kuma a narke yake sai aka jefa shi cikin yanayi mai dan karen sanyi, nan take zai sandare, nauyinsa ya ragu. Ba zai koma hakikanin nauyi da mizaninsa ba sai sadda ya sake narkewa. Sannan ba shi da wari, ko kamshi. Kuma dandanonsa bai yi iri daya da kowane irin abu ba. Amma a Hausance akan ce yana da gardi. Amma a kimiyyance Malaman kimiyya kan ce: “Water is tasteless,” ma’ana, ba shi da dandano. Wajen launi fa? Launinsa launin gilashi ne ko karau, wato “Crystal” ke nan a Turance. Idan yana dan kadan kenan. Amma idan mai yawa ne, launinsa kan karkata kadan zuwa launin shudi ko sirkin shudi, wato “Hue Blue” ke nan. Idan kuma yana yanayin iska ne, to idanun dan Adam ba ya ganinsa, sai dai a ji danshinsa a inda yake. Ruwa ke nan!
Alaka da Hasken Infra-red
Daga cikin launukan dake sararin wannan duniya tamu akwai nau’in hasken Infra-red, wanda haske ne kasa da launin ja; ko kace kasa da ganin duk wani mai gani. Irin wannan haske idan ya shiga ruwa ko ya haskaka cikin ruwa, narkewa yake yi nan take. Ma’ana, hasken Infra-red ba ya bayyana a cikin ruwa. Wannan ne ma ya sa shuke-shuke da tsirrai dake cikin kogi, ko rafi, ko teku suke iya rayuwa. Domin hasken rana na iya riskarsu nan take, duk zurfinsu a cikin teku. Kuma idan ba mu mance ba, su ciyayi da itatuwa da shuke-shuke, suna rayuwa ne ta hanyar makamashin hasken rana dake riskarsu a inda suke.
Makamashin Lantarki
Kamar yadda bayani ya gabata a sama, ruwa na dauke ne da sinadarai guda biyu da suka yi gungu don samar da shi; da maddar Hidirojin (Hydrogen) guda biyu, sai maddar Oksijin (Odygen) guda daya. Dukkansu a like suke da juna, kamar yadda yake a hoton dake shafin da mai karatu ke karatun wannan kasida. Wadannan maddoji kowannensu na da kimarsa da nau’in karfinsa a kimiyyance. Maddar Oksijin dai karfin mace take dauke da shi, wato “Negatibe Charge” (alamar – ), a ma’aunin karfin makamashin lantarki. A daya bangaren kuma, maddar Hidirojin na dauke ne da karfin namiji, wato “Positibe Charge” (alamar + ), a ma’unin makamashin lantarki. Wannan nau’in na karfin lantarki dake cikin sinadaran ruwa ne ke sa duk wani abu mai holoko (kamar kwallo, ko balan-balan, ko wani abu rufaffe mai dauke da iska) ya rika yawo a saman ruwan, ba tare da ya nutse ba. Wannan tasiri shi ne Malaman kimiyya ke kira “Capillary Force” ko “Capillary Action.”
Ruwa sinadari ne madaidaici. Wannan na cikin manyan kudororin Allah madaukakin sarki. Abin da wannan ke nufi shi ne, ya dace da yanayin dabi’ar mahallin duniya, domin ita kanta duniyar Allah Ya halicce ta ne cikin yanayin madaidaici, kamar yadda mai karatu watakila ya taba karantawa a kasidar da na gabatar shekaru 4 da suka gabata mai take: “Makamashi da Dukkan Nau’ukansa.” Wannan tsari na daidaito yana cikin ruwa. Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, maddojin Hidirojin dake cikinsa, ita ce kadai maddar da ta dace da yanayinsa. Malaman kimiyya suka ce da za a cire maddar Hidirojin a maye gurbinta da wasu maddoji irin su: Lithium, da Sodium, da Calcium, da Potassium, da Caesium, duk za su kore maddar Hidirojin. Ba wannan kadai ba, nan take ruwan zai canza yanayi, daga ruwa zuwa yanayin maddar Hydrodide, wanda duk wani abu mai dauke da wuta yazo kusa dashi, nan take zai kama da wuta. Ka ga ya tashi daga matsayinsa na ruwa ya koma wani makamashi mai dan karen hadari.
Alaka da Tubalin Halitta (Cells)
Jikin dan Adam na dauke ne da miliyoyin kwayoyin halitta ko kace tubalin halitta, wato Cells kenan. Su ne ke tafiyar da rayuwarsa, domin duk wani bangare na jikinsa; ciki da waje, yana dauke da wadannan kwayoyin halitta. Su ne rayuwar ma dai gaba daya. To, duk da wannan matsayi nasu, asalinsu ruwa ne. yanayinsu ruwa ne. A cikin ruwa suke rayuwa. Idan babu ruwa, ba za su taba iya aiwatar da komai ba. Samuwar ruwa a mahallinsu ne ke taimakawa wajen narkar da su, da mayar da su cikin yanayin da za su gudanar da ayyukansu cikin sauki. Rayuwar wadannan kwayoyin halitta kacokam ya dogara ga ruwa ne.