Dabi’u da nau’ukan sinadaran da ke cikin ruwa (1)

Matashiya Cikin kasida mai take: “Yadda Ruwa ke Samuwa da Nau’ukan Sinadaran da ke CIkinsa,” mai karatu ya karanta bayanai kan yadda ruwa ke samuwa, da yadda ruwan sama ke samuwa, da yadda tsarin maimaituwansa yake, wato “Water Circle,” da kuma bayani kan mizanin ruwa a duniya, da wasu duniyoyin da ake tsammanin suna da […]

Dabi’u da nau’ukan sinadaran da ke cikin ruwa (1)
Dabi’u da nau’ukan sinadaran da ke cikin ruwa (1)

Dabi’u da sinadaran da ke cikin ruwaMatashiya

Cikin kasida mai take: “Yadda Ruwa ke Samuwa da Nau’ukan Sinadaran da ke CIkinsa,” mai karatu ya karanta bayanai kan yadda ruwa ke samuwa, da yadda ruwan sama ke samuwa, da yadda tsarin maimaituwansa yake, wato “Water Circle,” da kuma bayani kan mizanin ruwa a duniya, da wasu duniyoyin da ake tsammanin suna da ruwa a cikinsu.  Wadannan bayanai sun zo ne cikin shekarar 2011.  Abin da ya rage mai karatu ke binmu bashi shi ne bangaren bayanin da ya shafi sinadarai ko siffofi ko dabi’un ruwa.  Wanann, a kimiyyance, shi ake kira “The Properties of Water.” Ko kace: “The Chemical and Physical Properties of Water.”  Abin da ya dawo damu kan wannan maudu’i kenan a wannan mako.
Me karatu ya ji cewa a duniya babu wani sinadari na kimiyya irin ruwa.  Bayan ni’imar aiko Annabawa da Manzanni da Allah Ya yi wa duniya, babu wani ni’ima da Allah Ya kara baiwa bayinSa (Aljanu da Mutane da Dabbobi da Tsirrai) irin ni’imar ruwa.  Wannan zance kuwa ba wai Malaman musulunci ne kadai suka tabbatar da shi ba, hatta wadanda basu da alaka da addini ma sun yarda cewa ruwa ya sha bamban da duk wani abin da dan Adam ke mu’amala da shi a sararin wannan duniya tamu, wajen tasarrafi.  In kuwa haka ne, bayan duk abin da muka sani a al’adance na siffofi ko matsayin ruwa a gare mu, me ya kara tabbatar masa da wannan matsayi hatta a wajen Malaman kimiyya?  Kafin sanin wadannan abubuwa, ya kamata mu san wai shin, shi ruwa wasu sinadarai ne ke haduwa don samar da shi?

Ruwa, Waye Kai?
Malaman fannin kimiyya musamman ba su bincike kan sinadaran da Allah Ya hore mana su a sararin wannan duniya, bayan sun gama gwaje-gwajensu, sun tabbatar da cewa ruwa na samuwa ne ta sanadiyyar kawancen wasu sinadarai ko madda na kimiyya guda biyu; da maddar Hidirojin (Hydrogen) guda biyu, da kuma maddar Oksijin (Odygen) guda daya.  A kimiyyance, ga yadda ake rubuta shi: H2O (bangaren farko mai dauke da “H2” na nufin maddar Hidirojin guda biyu ne.  bangaren “O” kuma na ishara ne ga maddar Oksijin, guda daya).  Wadannan maddoji ne guda biyu ke haduwa don samar da sinadarin ruwa kamar yadda muke ganinsa.  A hade suke, kamar yadda mai karatu ke gani a hoton dake shafin nan, shi yasa a kimiyyance ake kiran wannan gungu da suna: “Water Molecle.”  Duk wani sinadarin kimiyya mai iya mannewa a jikin dan uwansa, ana kiransa: “Molecle” ne.
Malaman kimiyya sun tabbatar da cewa, ruwa ne kadai sinadarin dake samuwa a yanayi ko dabi’ar yanayi (Form) iri uku.  Shi kadai ake iya samunsa a yanayi narkakke (Likuid Form), ko yanayi sandararre, a matsayin kankara (Solid Form), kuma a yanayin iska (Gaseous Form), a sararin wannan duniya tamu.  A wannan duniya tamu akwai ruwa a cikin iska (Water bapour), akwai shi a cikin giragizai, akwai shi a cikin teku, akwai shi a yanayin kankarar kan tsauni (Glacier), akwai shi a yanayin kankarar teku (Iceberg), akwai shi cikin dandanon gishiri (Salt Water) a tekuna, akwai shi cikin dandanon gardi a rafuka, da koguna da kuma karkashin kasa.  Wannan yanayin dabi’ar samuwa da siffa, ruwa ne kadai ya kebanta da shi/su.
Har wa yau, ruwa ne kadai daga cikin sinadarai, ke iya gudanuwa a duk inda aka kai shi ko aka ajiye shi, kuma shi ne kadai sinadarai kowane irin abu na da bukatuwa gare shi;  bukatuwa na kusa ko na nesa.  Babban misali shi ne jikin dan adam.  Ruwa a jikin dan adam yana daidaita yanayin jiki; idan zafi ne, ruwan sanyi zai daidaita shi.  Idan sanyi ne ruwan zafi zai daidaita shi.  Sannan ruwa a jikin dan adam na inganta masa mahadar kasusuwan jikinsa, wato “Joints,” su zama masu santsi, mai laudi, kada su bushe su yi kaushi.  Ruwa a bakin dan adam na jike dukkan tantanin dake mahallin ne; daga tantanin idanu (Eye Tissues), da tantanin baki (Mouth Tissues), zuwa tantanin hancinsa (Nose Tissues), duk ruwa na jike su, ya danyantar d asu don kada a samu matsala.  Ruwa ne ke raya dukkan bangarorin jiki dake cikin dan adam; irin su zuciya, da hanta, da koda, da sauransu.  Ruwa ne ke rage wa koda da hanta aikinsu, ta hanyar wanke su fyas, da kwashe dukkan sharar da ka iya toshe musu hanyoyin dake cikinsu don hana su aiki yadda ya kamata.   Sannan, yawan shan ruwa ga wanda ke gudawa yana rage gudawar, idan har an kamu.  Idan ba a kamu da ita ba kuma yawan shan ruwa na hana kamuwa da ita.  Ruwa ne kuma ke daukan sinadaran gina jiki na abinci, da sinadaran iska, don isar da su zuwa cikin kwayoyin halitta (Cells) dake jikin dan adam.  A karshe, yawan shan ruwa iya gwargwadon bukata kan narkar da sinadaran abinci da na abin sha (“Minerals” da “Nutrients”) zuwa sauran sassan jiki, don a samu gamewar fa’idarsu.  Ruwa sarkin aiki!

dabi’u da Sinadarai
“dabi’un ruwa” na nufin siffofinsa na bayyane ne.  A yayin da kalmar “Sinadaran ruwa” kuma ke ishara ga irin abubuwan da suke boye a cikinsa na maddojin kimiyya da idanun dan adam ba su iya gani.  Allah Buwayi Gagara-misali!!!  Ga wasu daga cikin dabi’u da sinadaran dake dauke a cikin ruwa ko tattare da ruwa:
Narkarwa
Ruwa wani irin sinadari ne mai iya narkar da duk wani abin da aka jefa a cikinsa, ma’abocin narkewa; duk wahalarsa wajen narkewa kuwa.  A cikin dukkan sinadaran dake wannan sarari da muke rayuwa, ruwa ne kadai ke iya narkar da duk wata madda ta kimiyya idan ya hadu da ita.  Wannan dabi’a ce tasa masana kimiyyar sinadarai a duniya ke kiran ruwa da cewa: “The Unibersal Solbent.”  Idan aka jefa su gishiri, da sukari, da sinadarin tsami (acid), da iskar da muke shaka, a cikin ruwa, duk yana iya narkar da su, ya hadiye su, su zama a cikinsa don a iya amfanuwa da abin da ke cikinsu.  Shi ya sa ake kiran wadannan sinadarai da suna: “Hydropholic” ko “Water-lobing”, wato masoya ruwa kenan.  Muddin suka shiga cikinsa, to sun zama shi.  Iya gwargwadon yawansu a cikinsa iya gwargwadon tasirinsu da kamantuwar da ruwan zai yi da su.    A daya bangaren kuma, idan aka jefa masa mai daskararre ko narkakke – irin su man ja, da man gyada, da man shanu, da bakin mai, da fetur da dukkan dangoginsu  – ba ya iya hadiye su; ba sa iya sajewa da shi, ba sa iya narkewa a cikinsa.  Saboda su ba masu narkewa ba ne.  Kuma shi ya sa ake kiransu da suna: “Hydrophobic” ko “Water-fearing”, saboda kasa narkewa da suke yi a cikinsa.  Wannan kudura ce mai karfin gaske da Allah Ya baiwa ruwa.

Wasu daga cikin tambayoyinku

Assalamu alaikum, barka da asuba. Don Allah ina neman shawara ne dangane da wayoyin nan guda biyu; HTC Android, da Nokia Lumia 520 ko 625.  Don Allah Malam wacce ta fi inganci ne a tsakaninsu?  A taimaka mini da shawara kan wacce zan saya.  Da yardar Allah zan bi shawararka.  Allah Ya taimaki Malam! – 08065750790

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Baka fadi nau’in HTC din ba, domin kalmar “HTC” sunan kamfanin da ke kera wayoyin salula ne.  Akwai nau’ukan wayoyi da dama da ya kera.  Duk haka, galibinsu suna dauke ne da babbar manhajar Windows, wasunsu kuma na dauke babbar manhajar Android.  Wani abu guda da ke bambance wayoyin HTC da sauran wayoyi shi ne, suna da masarrafai na musamman da kamfanin HTC ke sanya musu, wadanda kuma ba ka iya samunsu a kowace waya.  Bayan haka, suna da kara wajen sauti, sannan gangar jikinsu (Hardware) na da karko sosai. Abu na karshe shi ne, suna da kyau matuka.  Domin tsarin kirarsu ya sha bamban da na wayoyin salula gama-gari.  Shi ya sa ma suke da dan karen tsada.  
A daya bangaren kuma, wayoyin salula nau’in Lumia na kamfanin Nokia ne asali, amma yanzu kamfanin Microsoft ya saye kamfanin ko ince bangaren wayoyin salula na Nokia gaba daya, kuma cikin watan da ya gabata (Afrailu) ne ya karbi wayoyin Nokia gaba.  Nan gaba ya ce zai canza musu suna.  A takaice dai nau’ukan wayoyin Lumia suna dauke ne da babbar manhajar Windows Phone na kamfanin Microsoft, kuma su ma suna da inganci.  Ba nan kadai ba, suna dauke ne da hanyoyin sarrafa waya da suka sha bamban da sauran wayoyi.  Babu wani bambanci mai nisa tsakanin Lumia 525 da Lumia 625, sai na fadin fuska, da tsawon jiki, sai ‘yan kannan bambance-bambance a bangaren masarrafa da ba a rasa ba.
Idan kana neman saukin sarrafawa ne da samun masarrafai na kyauta cikin sauki, kana iya neman HTC mai dauke da babbar manhajar Android. Idan kuma kana bukatar kariyar bayanai ne, amma tare da jure tsaurin hanyoyin mu’amala, sai ka sayi Lumia 625, don ita ce gaba da Lumia 525.  Allah sa a dace.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Don Allah ina son ka yi mini bayani ne kan “Wi-Fi” da yadda ake amfani da shi.  Na gode.  – Mudassir Abdulkadir, Kantin Sauki, Gusau.
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdulkadir.  “Wi-Fi” manhaja ce dake taimakawa wajen hada wayar salula ko kwamfuta da yanayin sadarwa na Intanet a inda mai wayar ko kwamfutar yake.  Idan wannan masarrafa a kunne take, da zarar ka zo inda yanayin sadarwa na Intanet yake (wato “Wireless Connections”) nan take wayar za ta hango su.  Idan na kyauta ne kana iya amfani da su ta hanyar latsa kowanne daga cikinsu, sai ka je “Connect” ka matsa, wayar za ta jonu da wannan yanayin sadarwa, har ka iya mu’amala da Intanet a wajen.  Amma kuma da zarar ka bar wurin wannan yanayi na sadarwa zai dauke.  Kamar tsarin sadarwar wayar salula ne.  Kana iya kira ko amsa kira ne a wurin da akwai yanayin sadarwa (Network Connection), amma idan ka bar wurin shi kenan, sai a yanke ka.  
Idan kuma yanayin sadarwar dake wurin kaje tsararre ne (Secured Connection), dole sai an shigar maka da kalmar shiga, wanda babu mai saninsu kuwa sai wadanda suka mallaki yanayin sadarwar.   Da fatan ka gamsu.