dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola? 2
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a […]
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola?
daukar matakin bai kamata ba-Samuel Chidera Nidai
Samuel Chidera Nidai: “A gani na bai dace a ce an dauki matakin hana sayar da naman daji ba saboda yadda wasu suke ganin wannan annobar da wata farfagandar kasasshen yamma. Ya kamata mu fahimci cewa akwai cututtuka da dama da yakamata a mayar da hankali a kansu, ba wai kawai cutar Ebola ba.”