Dadewa a kan shadda ana danna waya zai iya haifar da ciwon Basir – Likita
Sai dai wani bincike ya nuna yin hakan na iya haifar wa mutum ya kamu da cutar Basir.
A zahiri kamar akwai jin dadi sosai idan mutum ya shafe tsawon lokaci a kan shadda yana daddanna waya.
Sai dai wani bincike ya nuna yin hakan na iya haifar wa mutum ya kamu da ciwon Basir.
- Saudiyya ta ba mata damar zuwa Umarah ba tare da muharrami ba
- Yadda ake dahuwar shinkafa ’yar Senagal da kifi
Basir dai wani ciwo ne da ke fito wa mutum a duburarsa, kuma ya kan iya yin girma ya zamar masa kamar wani kari, ta yadda zai hana shi sakat.
Amma a cewar wani likita dan Najeriya, Olufunmilayo, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, dadewar na iya haifar da ciwon Basir.
Ya ce, “Zama a kan shadda na tsawon lokaci – sama da minti 10 – zai iya haifar da cutar Basir.
“Ba saboda sukari ba, ba saboda shan lemuka masu zaki ba. Kuna kamuwa da Basir ne saboda kun mayar da shaddarku wajen zama ku daddanna waya.
“Idan kuka dade a kan shaddar, hakan na kara zafi a duburarku, lamarin da ke sa jijiyoyinku su rirrike.
“Daga bisani sai su fara zafi, su fara tsunkunin mutum, wani lokacin ma su sa ya fara zubar da jini. Wannan shi ake kira da ciwon Basir,” kamar yadda ya wallafa.
Ko a baya dai, Daraktan wata cibiya da ke yaki da cutar kansa a cibiyar Cedar Sinai da ke birnin Los Angeles a Amurka, Samuel Oschin, a wata makala da ya wallafa ya ce, “Ba wai amfani da wayar ne ke haifar da cutar ba.
“Zama a kan shaddar kana yin ko ma mene ne na tsawon lokaci shi ne zai iya haifar da cutar.”