Dadina da gobe saurin zuwa
A ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan Najeriya da yawa suka ga ta-leko-ta-koma sa’ilin da Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega ya kuntuka musu bakin cikin da ya hana su barci saboda jirgawa da Zaben da aka tsara za a fara a gobe, 14 ga watannan zuwa ranar 28 ga watan gobe da […]
A ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan Najeriya da yawa suka ga ta-leko-ta-koma sa’ilin da Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega ya kuntuka musu bakin cikin da ya hana su barci saboda jirgawa da Zaben da aka tsara za a fara a gobe, 14 ga watannan zuwa ranar 28 ga watan gobe da kuma 11 ga watan jibi. Majalisar Manyan kasa da ya gana da wadanda ke da ruwa da tsaki game da Zaben duk kuwa da dagewar da ya yi kai-da-fata cewa shi da hukumarsa a shirye suke don gudanar da Zaben yadda aka tsara.
Gurgusawa da zaben kamar yadda farfesa Jega ya yi ya rage masa kima a idanun dimbin talakawan kasar nan, domin kamar yadda ya fayyace, hukumarsa za ta bi shawarar manyan jami’an tsaron kasar nan wadanda suka nuna cewa ba za su iya samar da ingantaccen tsaro ba a rankun zaben, domin kuwa dukkansu za su shiga harkallar da wasu dakarun kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ke yi ne a halin yanzu don korar kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ke baje kolinta a Najeriya.
Hakan kuwa ya saba da matsayin Farfesa Jega, wanda tun da can farko ya tsaya-kai-da-fata cewa hukumarsa ta kammala shirinta tsaf na gudanar da zabe a ranakun da aka tsara, kuma an yi kyakkyawan shirin ba ‘yan gudun hijira a wasu jihohi uku da ake dauki-ba-dadi da ‘yan ta’adda damar jefa kuriunsu. Farfesa Jega na sane da batun rashin tsaro a sashen Arewa-maso-Gabas, ya kuma san cewa hukumar zabe da Jihar Yobe ta gudanar da zaben kananan hukumomi duk da rashin tsaron da ke addabar jihar, kuma ko kadangare ba a kashe ba, kuma idan ba domin kotu ta bayar da umurnin canjin gwamnati ba a Jihar Adamawa a watannin baya, da hukumar Farfesa ta gudanar da zaben da ta yi kyakkyawan shirin samun nasararsa.
Jama’a sun nuna gamsuwarsu game da yadda Jega ya jajirce cewa a shirye yake ya gudanar da zabe, duk kuwa da cewa akwai wata ‘yar miskila da suke fuskanta dangane da karbar katuttukansu na dindin don jefa kuri’a. Hukumar zabe ta tabbatar da cewa ta samar da katuttukan wadanda ta yi wa rajista, ta kuma aike da su wuraren da za a kakkarbe su, amma sai jama’a ba su fito yadda ya kamata ba don karbar katuttukan, inda ya ce har ya zuwa gabannin zaben mutane kusan miliyan hamsin ne kawai suka karbi nasu, sauran kuma na can jibge a wuraren da aka aike da su, ba a kakkarba ba.
Irin abin da Farfesa ya bayyanawa wancan taro na Majalisar kasa ke nan a ranar Alhamis din da ta gabata, kuma duk da cewa manyan jami’an tsaron kasar nan sun hallara a gaban wannan Majalisa don su ma su yi mata bayani game da halin da kasar ke ciki sakamakon rashin ingantaccen tsaro, sun kuma nuna cewa zai yi wuya a gudanar da zabe a irin wanan yanayin, Farfesa Jega bai canja matsayinsa ba na cewa hukumarsa za ta iya gudanar da zaben duk da rashin ingantaccen tsaro. Haka nan aka tashi taron, kowa na tsammani idan Farfesa Jega ya gana da masu ruwa da tsaki cikin harkokin gudanar da zabe zai tsaya kan waccan maganarsa ta cewa a shirye hukumarsa take wajen yin zaben.
Dangane da haka ne a ranar Asabar din makon jiya ya wuni yana gagganawa da jam’iyyun siyasa guda 25 da kuma kwamishinonin zabe na hedkwata guda 15 da kwamishinonin zabe na jihohi da kuma kungiyoyin raji kare hakkin dan Adam don jin tabinsu game da yiwuwar gudanar da zabe a ranakun da aka tsara. Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyun siyasa masu bukatar a ci gaba da zabe kan kari, sun dara masu so a gurgusa da shi zuwa wani lokaci; haka nan kuma kwamishinonin hukumar zaben da kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam duk sun nuna amincewarsu da yin zabubbuka a lokutan da aka tsara. Amma wane tudu, wane gangare Farfesa Jega ya bi, sai ga shi sa’ilin da ya zo yi wa manema labarai jawabi game da matsayin hukumarsa kan ranakun zaben ya ce za a yi karin makonni shida bisa ga wa’adin da tun can farko aka tsara don a bayar da dama ga dakarun Najeriya su fatattaki kungiyar Boko Haram kwata-kwata daga kasar nan. Haka nan nan kawai, zikau-mikau, Farfesa Jega ya waske daga batun cikakken shirin da ya yi don gudanar da zabe, ya koma kan batun rashin tsaron da zai hana aikin zaben, domin kamar yadda ya ce rayukan dimbin mutanen da za su yi aikin zaben na iya halaka a kusan dukkan sassan kasar nan idan har an ce sai an yi zaben a lokacin da aka tsara domin ba wani maikacin hukuma da zai tsare su.. Da wane dalili Farfesa Jega zai canja ra’ayi haka nan siddan-madalakan alhali kuwa sauran kungiyoyi da dukkan wadanda ya tuntuba sun ce ana iya ci gaba, a gudanar da zaben yadda aka tsara?
Wannan dai ba sabon al’amari ba ne dangane da halayyar Farfesa Jega wajen gudanar da zabe. Ko a shekarar 2011 ma ya taba yin haka, sa’ilin da kwanaki biyu kafin farawa ya bayar da sanarwar cewa hukumarsa a shirye take ta gudanar da zabe, kuma dukkan kayayyakin aiki na hannu. To amma ana tsakiyar gudanar da zaben sai ya tsayar, ya kuma gurgusa da shi sati guda, bayan an kira shi a fadar gwamnati, gaban dukkan manyan jami’an tsaro, aka zazzare masa idanu aka tsorata shi matuka, aka nemi ya soke wannan zaben domin gwamnati ta fara ganin alamun cewa jam’iyyarta za ta kashi. Ilai kuwa haka nan aka yi, daga bisani kuma sai ga shi nan hukumar Zaben ta daga wa jam’iyyar gwamnatin kafa, ta ci karenta ba babbaka.
Yanzu ma ga shi nan an sake kwatawa, domin kuwa wadanda ke lura da al’umura a hukumar Zaben sun tabbatar da cewa akwai alamun razana a jikin Farfesa Jega, sakamakon saduwar da ya yi da wasu jamai’an tsaro a ofishinsa, jin kadan bayan ya gama ganawa da masu ruwa-da-tsakin da suka nuna amincewarsu da kada a daga zaben. To, an dage zabe zuwa makonni shida nan gaba, amma ai ko da shekara ne, kaman kwana guda ce, domin ita gobe saurin zuwa gare ta.