Dadiyata: El-Rufai na neman shafa wa Ganduje kashin kaji — Tsohon Kwamishina
Tsohon Kwamishinan ya roƙi duk wanda ke da bayanai game da ɓacewar Dadiyata ta miƙa su ga hukumomin tsaro.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi na cewa yana da hannu a ɓacewar Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata.
A cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Muhammad Garba, ya fitar, Ganduje ya bayyana zargin a matsayin mara tushe.
- Manufofin tattalin arziƙin da Tinubu ya kawo ba sa aiki — Jigon APC
- Kotu ta umarci sojoji su kawo Sheikh Sani Khalifa Zaria
Ya ce El-Rufai na ƙoƙarin ɗauke hankalin jama’a daga kan jama’a daga ɓacewar Dadiyata a Kaduna zuwa wani waje na daban.
Garba, ya ce al’ummar Kaduna sun san irin sukar da Dadiyata ya dinga yi da kuma inda abin da yake nufi, yana mai cewa alhakin tsaro a lokacin yana hannun Gwamnatin Kaduna da hukumomin tsaro na tarayya.
Sanarwar ta buƙaci a binciki kalaman El-Rufai da kyau, tana jaddada cewa irin waɗannan manyan zarge-zarge dole ne su kasance da hujjoji.
Ta kuma yi gargaɗin cewa janyo Ganduje cikin lamarin ba tare da wata hujja ba na iya mayar da batun na siyasa.
Garba, ya ƙara da cewa a lokacin mulkin Ganduje, gwamnan ta bayar da ƙofar sukarsa tare da kyakkyawar hulɗa da kafafen yaɗa labarai, ba tare da tsangwamar ’yan jarida ba.
Ya miƙa alhininsa ga iyalan Dadiyata, yana cewa abin da ya fi dacewa shi ne a gano gaskiya ta hanyar bincike, ba mayar da lamarin siyasa ba.
Ya kuma buƙaci duk wanda ke da sahihan bayanai kan ɓacewar Dadiyata da ya miƙa su ga hukumomin da suka dace domin a warware batun bisa hujjoji.