dadu imani ga mai cutar da maqwabcinsa (1)
Littafi na biyar: Sahih Al-bukhari da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Littafin Wasiyya. babi na Farko: Wasiyya bisa fadar Annabin Allah (SAW) cewa: “Wasiyyar mutum ya kamata ta zama rubutacciya ce kullum tare da shi.” Allah Madaukaki Ya ce: “An wajabta (rubutu) a kanku idan mutuwa ta halarci dayanku, idan ya bar wata dukiya, […]
Littafi na biyar: Sahih Al-bukhari
da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Littafin Wasiyya.
babi na Farko:
Wasiyya bisa fadar Annabin Allah (SAW) cewa: “Wasiyyar mutum ya kamata ta zama rubutacciya ce kullum tare da shi.” Allah Madaukaki Ya ce: “An wajabta (rubutu) a kanku idan mutuwa ta halarci dayanku, idan ya bar wata dukiya, wasiyya domin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajibce a kan masu takawa (k:2:180).”
436. Imam Al-bukhari (RA) ya ce: “Abdullahi dan Yusuf ya ba mu labari, ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Malik daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “bai dacewa ga wani mutum Musulmi wanda ke da wata wasiyya da ke son a zartar, har ya kwana dare biyu face wasiyyarsa tana rubuce tare da shi.” Muhammad dan Muslim ya karbo daga Amru daga dan Umar daga Annabi (SAW).
437. Imam Al-bukhari (RA) ya ce: “Ibrahim dan Haris ya ba mu labari ya ce: “Yahya dan Abu bukair ya ba mu labari ya ce, Zuhair dan Mu’awiyya Alju’afi ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari daga Amru dan Haris dan uwar matan Manzon Allah (SAW) Juwairiyya ’yar Haris ya ce: “Manzon Allah (SAW) bai bar wani dirhami ko dinari ko wani bawa ko baiwa ba lokacin rasuwarsa face alfadararsa fara da makaminsa da wata kasa da ya bari sadaka.”
438. An karbo daga khallad dan Yahaya ya ce: “Malik dan Migwal ya ba mu labari ya ce, dalha dan Musrif ya ba mu labari ya ce: “Na tambayi Abdullahi dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da su), cewa: “Shin Annabi (SAW) ya kasance ya yi wasiyya? Sai ya ce: “A’a, na ce: “To yaya ake rubuta wasiyya ga mutane, ko ya ce, yaya ake umurni da rubuta wasiyya? Ya ce (Annabi): “Ya yi wasiyya da (riko da) Littafin Allah.”
439. An karbo daga Amru dan Zuraratu ya ce: “Isma’il ya ba mu labari daga Aunu daga Ibrahim daga As’wad ya ce: “Sun ambata a wurin A’isha (RA) cewa, “Lallai Annabi (SAW) ya nada Aliyu (Allah Ya yarda da shi), halifanci ta hanyar wasiyya. Sai A’isha ta ce: “Yaushe aka yi masa wasiyya, alhali ni na kasance majingininsa (Annabi) a bisa kirjina? ko ta ce, “Na rungume da ni.” Sai ya yi kira da a kawo wata tasa (tire) na ruwa daga nan jikinsa ya yi rauni a dakina ban san cewa: “Lallai shi ya rasu ba, to yaushe ne ya yi wasiyya gare shi (don zama khalifah)?”
babi na biyu: Mamaci ya bar magadarsa suna mawadata ya fi (alheri) da ya bar su suna rokon mutane:
440. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Sa’id dan Ibrahim daga Amir dan Sa’ad daga Sa’ad dan Abu Wakkas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya zo domin ya gaishe ni lokacin ina Makka alhali shi, yana kin mutuwa a kasar da ya yi kaura daga gare ta. Ya ce, “Allah Ya jikan dan Afra’u, na ce: “Ya Manzon Allah, na yi wasiyya da dukiyata dukanta ga sadaka? Ya ce: “A’a, na ce: ‘To rabi,” ya ce, “A’a, na ce: “To daya cikin uku,” ya ce: “daya cikin uku! daya cikin uku na da yawa, lallai kai, a ce ka bar magadarka cikin wadata ya fi alheri da ka bar su talakawa suna rokon mutane cikin hannayensu. kuma duk yadda ka ciyar da wani abu na ciyarwa ga iyalanka lallai za ta zamo maka kamar sadaka har lomar abinci da kake sanya ta zuwa ga bakin matarka. kuma ina fatar Allah Ya daukaka (kara maka tsawon kwana) kuma Ya amfani wadansu mutane da kai, wadansu kuma su cutu saboda kai, (ta wajen yaki). Saboda lokacin ba ya da komai face ’ya mace guda daya.” (daga baya Sa’adu ya haifi ’ya’ya bakwai).