Dafdalar daular Dala

A yammacin rana ta sili da kwanciyar magirbi ga watan Farion-biri na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, na hadu da Sakataren Lauye-lauyen Dokokin Kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya, inda ya nuna mini battar  koren ganyen shayi da aka sawo daga kasar Sirilanka, a kan Dala babbana lauje da zagaye. […]

Dafdalar daular Dala
Dafdalar daular Dala

A yammacin rana ta sili da kwanciyar magirbi ga watan Farion-biri na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, na hadu da Sakataren Lauye-lauyen Dokokin Kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya, inda ya nuna mini battar  koren ganyen shayi da aka sawo daga kasar Sirilanka, a kan Dala babbana lauje da zagaye. Na cika da mamakin ganin yadda wannan ’yar karamar batta kudinta ya kai Dalar Amurkawa babban lauje da zagaye, ba wani zagaye-zagaye. Abin dai da na fasko shi ne, farashin ’yar karamar battar shayi ya zarta na gangar man tunkuza, wanda a da kasar Haurobiya ta dogara da shi kacokan wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Kai wani babban abin ta’ajibin shi ne, a makon da ya arce da na ziyarci titin gidan giwa da gidan zaki da ke birnin Dabo inda ba a dabo, sai kawai wani mutum da ke zaune a daura da katafaren kantin Sahada (wato ka saka Hauro ka harhada kayayyakin masarufi) ya nusar da ni cewa, hatta mai sayar goriyar marsa da daushe wai yana da masaniyar Dala ta yi tashin gwauron zabo, inda take ta kara taushe Hauro a kowace rana.
’Yan makaranta da dawo birnin Haurubja, wato babban birnin Haurobiya, sai kawai na fasko cewa, kusan ko’ina mutum ya tunkara, musamman ma idan za a yi cefane koda na kayan miya ne, nan take za a nusar da kai/ke cewa, Dala ta haure, inda ta jefa masu mu’amala da Hauro cikin haure-haure da hauragiya a kasar Haurobiya. Uwa-uba, daukacin majalisun al’umma, ban da na Saurayin-kirinki da dogarin wakilan rafkiya ana t ace ce ku ce kan cillawar Dala, tamkar za ta zarce zuwa sararin samaniya.
Tun da aka fara dama-dama da kurda-kurdar wasan Samson siya-siya cikin shekarar alif sili da manuniyar kasa da ta kasa da ta kasa, an samu ministocin Baba-Ojo mai gonakin Ottawa da ake biyansu ladar kwadago a cikin Dalar Amurkawa, sabanin Hauron kasar Haurobiya. Wannan shi ne tushen kafuwar dafdalar daular Dala, ala’amarin da ya jefa gama-garin Haurobiya cikin haure-haure da hauragiya.
Rukunin ministocin da suka rika samun ladar kwadagon su kudin musayar Hauron Haurobiya, bisa kimar kololuwa da aka dora Dalar Amurkawa a kai, tana nuna fifikon su a kan sauran ’yan uwansu Haurobiyawan da suka yi bobo da kwambon bokoko a kasar su ta gado.
Gurgun karatun wasikar jakin dawa da na gida a tsarin jan ragamar al’umma shi yake haifar da irin wannan wala-wala ta biyan ladar kwadago, har ma da la’adar kadago ga shafaffu da mai, ta yadda za su samu damar kafa DAULAR DAFDALA da DALA  a ciki da wajen Haurobiya.
Irin wannan tsari na tsimin tsiyata kasa, shi ke kai al’umma kasa warwas. Domin za mu iya fasko cewa, wanda duk aka ki ba shi ladar kwadagon sa a Dalar Amurkawa, to zai yi kokarin yin kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma, ko ma ya yi sabi ruga, musamman saboda takaicin fifita bakaken Turawa a kan sa.
Kai har ma akwai ma’aikata a ofishin tsohon Magajin garin Haurubja, babban birnin Haurobiya, da suka karbi lada da la’adar kwadagon su a Dalar Amurkawa.
dimbin kafafen yada kwakwazo da surutu rututu sun soki lamirin biyan lada da la’adar kwadagon Gwamnatin Haurobiya a Dalar Amurka. Kodayake ba za a rasa kamfanoni da suka kwata irin wannan ta’asa da gwamnatin Haurobiya ta fara tafkawa a kwanon tasarta ba. Domin akwai ’yan ciranin da idan suka shigo Haurobiya, dama a kulla yarjejeniya kan lada da la’adar kwadagon su za ta kasance cikin Dala, ta yadda za su samu damar yin dafdala da dulmiyar da dolaye.
Bisa ga la’akari da dimbin ’yan kwadago masu neman kadago ko curin mandako da ake biya lada da la’adar kwadago a Dala, za mu iya fasko cewa, mun tsikaro tsiyar tsiyata kasar mu. Kai ko Barau-dan-canji da ya rika wadaka a baya, yanzu da aka dan taka masa burki ya bambance tsakanin tsaba da tsakuwa.
’Yan watanda da suka yi wadaka a cikin damin Hauron sayen makaman artabu da masu haramta bobo da kwambon bokoko, sun yi zari ruga ne da damin Dalar Amurkawa har gashin balama karamin lauje da malala dari sili. Ta’asar Samun-bom-da-sauki da su In-gwangwaje-in-wala (ko wala-wala) da Mace-da-zane, da daukacin jiga-jigan jam’iyya mai danboto da sanda jirge, kai har ma da wani ba’ari na wadanda suka birkide a cikin jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu, sun yi aika-aikar su ne, don kafa daular Dalar dafdala.
Haurobiyawa, ya kamata mu fasko cewa, masu dafdala da daloli sun taimaka matuka gaya wajen cukurkuda al’amuran sarrafa dukiya a kasar nan. Irin wadannan jiga-jigan jigata al’umma, sun himmatu ka’in da na’in wajen kassara kasa, ta yarda a koyaushe suka haifar da tsilli-tsillin matsalolin da suka yi wa al’umma sasari, sai kawai su barku ku yi ta takaddama kan yadda za ku warware kullin ko yi wa tufakar hanci, alhali su suna da masaniya kan yadda mugun aikin su ya tsikaro tsiyataku.
Masu koyon watsatsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido, lallai mu fasko cewa, idan har gwamnati dungurungum za ta biya lada da la’adar kwadago, har jaridu da makalu da mujallu su caccaketa, su kuma nusar da ita illar yin hakan, to wajibi ne mu daina dora alhakin kassara Hauro a kan Barau-dan-canji, domin shi ma kawowa da karba ake yi a wajensa.
Haurobiyawa, ya kamata mu fasko cewa, akwai dimbin masu biyan kudin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai da ’yan dugwi-dugwi ke yi a kasashen ketare. Sannan a farfajiyar bokan Turai da ke kasar Misirawa da Birtaniyawa da Indiyawa, har har su Tayar-Landan da Indon-Isiya, du kana zuwa neman jike-jike da sinadaran shafe-shafen inganta uwar jiki. daukacin wadannan al’amura da muka jero a farfajiyar wannan makaranta, Haurobiyawa na yin su ne a wajen dafdalar daular Dalar dalar Hauron Amurkawa.
Lokaci dai ya yi da Baban-burimn-huriyya zai yunkura wajen hana kafuwar daular dafdala da Dala, don gudun dulmiyar da dolaye. Haurobiyawa kuwa, lallai su yi wa kan su kiyamul laili wajen amfani da dimbin kayan da ake samarwa a Haurobiya, musamman ma a wannan lokaci da akalar tattali da tanadi ke kokarin juya akala wajen fardar garka da gayauna; da makekiyar makiyayar fullo, inda ake kiwata bisashe.