Daftarin Kasafin Kudi ya yi batan-dabo a majalisa
A ranar Talatar da ta gabata ce al’ummar Najeriya suka wayi gari da samun labarin cewa an sace Daftarin Kasafin Kudin bana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa.Shugaba Buhari ya mika daftarin ne a ranar 22 ga Disamban bara, sai dai kuma a daidai lokacin da majalisar ta dawo hutu don […]
A ranar Talatar da ta gabata ce al’ummar Najeriya suka wayi gari da samun labarin cewa an sace Daftarin Kasafin Kudin bana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa.
Shugaba Buhari ya mika daftarin ne a ranar 22 ga Disamban bara, sai dai kuma a daidai lokacin da majalisar ta dawo hutu don fara muhawara a kan kasafin sai aka nemi kasafin sama da kasa ba a same shi ba.Amma Majalisar wakilai ta nuna wa duniya nata kwafin.
Jaridar Premium Times ce ta fara fallasa lamarin, inda ta ce Shugaban Masu Rinjaye Sanata Ali Ndume ya shaida wa wani zaman sirri na majalisar cewa an sace daftarin kamar yadda ta ce ta samo labarin ne daga wadanda suke da alaka da lamarin. Majiyarta ta ce Sanata Ndume ya ce ba za a tattauna batun kasafin ba, sai an samo kwafen kasafin daga fadar Shugaban kasa ko Ma’aikatar Tsare-Tsare ta kasa.
Nan take majalisar ta umarci Shugaban Kwamitin Kasafi Sanata danjuma Goje ya gano daftarin kuma ya hada hannu da da Babban Mai tallafa wa Shugaban kasa kan Harkokin Majalisar Dokoki Sanata Ita Enang da kuma Ma’aikatar Tsare-Tsare don warware matsalar.
Ta ce sanatocin sun nemi a danne maanar kada ta fito fili don kada a kunyata fadar Shugaban kasa da majalisar da kuma ita kanta kasar.
Sanatocin PDP sun zargi fadar Shugaban kasa da hannu a sace daftarin, zargin da sanatocin APC suka yi watsi da shi.
Sai dai daga baya Sanata Ndume ya musanta rahotannin da kafafen watsa labaran suka bayar na cewa an sace daftarin kasafin. Ya ce baya ga kwafen biki da Shugaba Buhari ya mika wa majalisar kowane zauren majalisar yana da nasa kwafe na daftarin don haka babu yadda za a yi daftarin kasafin ya bace.
Shi ma Kakakin Shugaban kasa Malam Garba Shehu ya musanta cewa Shugaban kasa ya janye kasafin, inda ya ce ga al’ada da zarar aka mika wa majalisa daftarin kasafin ya koma mallakin majalisa. “ A saninmu shi (Shugaban kasa) bai janye kasafi ba, an mika daruruwan kwafen daftarin kasafin ga zauren majalisun biyu. Ga al’ada idan aka mika kasafi ga majalisa ya fice daga hannunmu. Don haka a tambayi wadanda suka fi dacewa su yi bayani,”inji shi.