Daga Borno Zuwa Yobe, Zuwa….

A cikin wannan shafi a watanni da dama da suka wuce na taba yin sharhi da kuma tambayar Yaushe Boko Ya Zama Haram a Arewacin kasar nan, musamman ganin yadda aka yi ta faman yamadidi da ilmin boko da ake ganin shi ne matsala bayan bayyanar wata kungiya da aka sa wa suna BOKO HARAM. […]

Daga Borno Zuwa Yobe, Zuwa….
Daga Borno Zuwa Yobe, Zuwa….

A cikin wannan shafi a watanni da dama da suka wuce na taba yin sharhi da kuma tambayar Yaushe Boko Ya Zama Haram a Arewacin kasar nan, musamman ganin yadda aka yi ta faman yamadidi da ilmin boko da ake ganin shi ne matsala bayan bayyanar wata kungiya da aka sa wa suna BOKO HARAM. Na fada a wancan lokaci cewa a yawancin jihohin Arewacin Nijeriya kurum  ko kuma dukkan fadin Nijeriya da ma wasu sassan duniya, kalmomin nan biyu, wato Boko Haram sun zama ruwan dare a tsakanin al’umma; sun zama kalmomin da za a iya amincewa suna cikin harshen Hausa, sun zaunu cikin kamus ko cikin jawabai na yau da kullum, a tsakanin jama’a ko kuma cikin jaridu da rediyoyi da talbijin. Sai dai kamar yadda na nuna a wancan lokaci, wadannan kalmomi suna da mabambanta ma’anoni, sun kuwa hada da:
•       Ga wasu, Boko Haram, kungiya ce ta addinin Musulunci, wadda ke neman ganin an gudanar da sharia’ar Musulunci a Nijeriya.
•       Ga wasu kuma Boko Haram,  su ne hare-haren bom da tashin hankali da ya dabaibaye wasu sassa na Arewacin Nijeriya
•       Ga wasu kuma Boko Haram su ne wadanda ba su yarda da ilmin boko ba, ba su amince da shi ba, ba su kuma amince cewa zai iya taimakon mutum ba, don haka a yi waje da shi da duk wani mai da’awar sa.
•       Ga wasu kuma ba komai ba ne Boko Haram ba sai gwamnatin PDP da Goodluck Jonathan da suka kasa yin wani katabus wajen kawo sauyi a rayuwar jama’ar kasar nan.
•       Haka kuma wasu na ganin ba wasu ba ne ‘yan Boko Haram sai wasu tsirarun ‘yan siyasa (na kowace jam’iyya) da suka rasa makama tun da aka yi zaben watan Afrilun 2011, suke amfani da wannan dama domin su tada zaune tsaye, ta yadda za su hana ruwa gudu, ko ba komai ai dole a yi da su.
•       Wasu kuma na ganin ba wasu ba ne Boko Haram face sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da suke ta ba-ta-kashi da ‘yan kungiyar Jama’atu Ahlissunna Wal Jama’ati Lidda’awati Wal Jihad.
Ba wani abu ya sa ake da dabaibayi wajen fahimtar abin da ya faro daga jihar Borno ba tun daga wajajen shekarar 2009, ya rarrafa zuwa Yobe da Adamawa da wasu jihohi makwabta sai don kila ba a mayar da hankali waje guda domin fahimtar ainihin matsalar ba, shi ya sa kowa dai da irin yadda yake kallon wadannan kalmomi da kuma abin da ke fita daga ayyukan ta’addanci da ke faruwa daga lakabe musu. Amma tambayar da kullum nake yi ita ce, shin su wane ne ‘yan Boko Haram na gaskiya? Su wa ke ta faman kashe al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba? Su wa ake ta faman yaki da su yau kusan sheka 5 kenan ba kuma alamun kawo karshen wannan badakala? Shin kawo yanzu akwai wani abu ko wata kungiya ko kuma wasu gungun jama’a da za mu iya kira da wannan suna na Boko Haram? Shin hare-hare da kashe-kashe da ake ta faman yi, musamman yanzu a Arewa-Maso-Kudu daga wannan kungiya ce ta Boko Haram ko kuwa wata kullaliyar ce don cin zarafi? Ina batun cewa tuni an kashe da kame jiga-jigan ‘yan kungiyar ta Boko Haram, kuma cikin ‘yan watanni za a kawo karshen matsalar, amma sai ga shi kullum kamar ana kashe gobara ta hanyar watsa mata man fetur?Idan har yanzu akwai wannan kungiya ko gungun mutane ko wasu masu da’awar Boko Haram, me ya kawo kashe-kashe da rushe-rushe da saka bama-bamai, har da kunar Bakin Wake a wasu lokutta a cikin makarantu da kauyuka da garuruwan da ma al’ummar ba su ji ba, ba su gani ba? Shin ko dai abin da wasu ke ta fada ne cewa Boko Haram daban, harin bom da kashe-kashe da tashin hankalin da ya mamaye mu, shi ma daban yake, ma’ana akwai lauje a cikin nadi?
Ya zuwa yanzu duk mai aiki da hankali ya fahimci cewa badakalar da ke tattare da Boko Haram ko kuma kashe-kashe da ake yi da sunan Boko Haram ya wuce dukkan inda tunani zai iya zuwa. Bai yiwuwa a ce an yi sama da shekara 5 ana yaki da kungiya guda, an kashe dubban bilyoyin Nairori, an tura sojojin kasa da na sama, ga ‘yan sanda bila haddin kuma barbaje ko’ina, amma kuma a ce ba alamun nasara, sai fadar da shugabanni ke yi na wai ana samun nasara, tun da an kori masu tada zaune-tsaye zuwa wani sashi na kasar nan kurum. Shin ina amfanin wadannan jami’an tsaro a wannan sashi idan har kowace rana ta Allah za a wayi gari ana rasa rayukan bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba? Ina gaskiyar lamarin da ke nuni da cewa jami’an tsaro ba komai suke ba sai zama ‘yan kallo a lokacin da ake karkashe mutanen ba su ji ba su gani ba.Wannan ba alamun nasara ba ne, kuma hanyar da kurum za a iya tabbatar wa al’umma cewa da gaske ake ita ce a gano masu yin wannan makarkashiya!
Za Mu Ci Gaba