“Daga Dajin Sambisa na kawo ’yan mata masu kunar bakin-wake Kano”
Mutumin da ake zargi da horar da ’yan matan da suke kai harin kunar bakin-wake da bama-bamai a Jihar Kano, ya shaida wa jami’an tsaro bayan da suka damke shi a wata maboyarsa cewa daga Dajin Sambisa da ke Jihar Borno ya kawo ’yan matan zuwa Kano.Mutumin mai suna Ibrahim Ibrahim, wanda ya zo hannu […]
Mutumin da ake zargi da horar da ’yan matan da suke kai harin kunar bakin-wake da bama-bamai a Jihar Kano, ya shaida wa jami’an tsaro bayan da suka damke shi a wata maboyarsa cewa daga Dajin Sambisa da ke Jihar Borno ya kawo ’yan matan zuwa Kano.
Mutumin mai suna Ibrahim Ibrahim, wanda ya zo hannu a yayin wata mamaya da jami’an tsaro na hadin gwiwa suka kai inda yake horar da ’yan matan a karamar Hukumar Dala na ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai wajen bayar da bayani kan sabon salon da suka shigo da shi na amfani da ’yan mata wajen kai harin kunar bakin-wake.
Wata majiya da ke da alaka da jami’an tsaro ta shaida wa Aminiya cewa an kama mutumin da ’yan mata 16 ne a yayin da yake koya musu dabarun kai harin kunar bakin-wake da suka fara a wasu sassan birnin Kano. Majiyar ta ce kame mutumin da ’yan matan na daga cikin dalilan dasa aya ga hare-haren da suka shirya kaiwa har na tsawon wata guda.
Sabon salon harin na ’yan matan ya fara bayyana a Kano ne a lokacin bikin karamar Sallah, inda ’yan mata suka kai hare-haren bam a wurare biyar tare da hallaka mutum 30 da raunata wasu da dama.
Wata majiya ta jami’an tsaro da ta tabbatar da kame mutumin da ’yan matan, ta ce, “Mutumin ya zo hannu kuma yana ba da hadin kai wajen bayar da bayanai masu muhimmanci ga jami’an tsaro.” Kuma ta ce a ’yan kwanakin nan sun gudanar da mamaya da dama a mafakar batagari da ake zargi da aikata miyagun laifuffuka.
Kakakin jami’an tsaron na hadin gwiwa, Ikechukwu Ekedia ya tabbatar da damke wanda ake zargin da ’yan matan, sai dai ya ce yawan ’yan matan na tsakanin 13 ne zuwa 16, kuma suna ci gaba da bincike a kan lamarin.