DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna
Shin ko Dokar Kasa ta bai wa shugaban kasa karfin ikon dakatar da gwamnan jiha dama ’yan majalisar dokokin ta?

A karshe dai abin da wasu ke hasashen zai faru a Jihar Ribas ne ya faru inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar kuma ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa da kuma ’yan majalisar dokokin jihar.
Sai dai bayan wannan doka da shugaban kasar ya ayyana ne al’umma da dama ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyin kan wannan batu.
A yayin da wasu ke bayyana cewa dama tuni abin da shugaban kasar yake bukata ke nan, wasu kuwa ke bayyana cewa shugaban kasar ma ba shi da ikon dakatar da zababben gwamna.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan
- DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan shin ko Dokar Kasa ta bai wa shugaban kasa karfin ikon dakatar da gwamnan jiha dama ’yan majalisar dokokin ta?
Domin sauke shirin, latsa nan