DAGA LARABA: Abin ya sa ’yan Nijeriya ke kishin ƙabila fiye da ƙasa

Me ya sa ’yan Nijeriya sun fi nuna kishin ƙabilun da suka fito idan aka kwatanta da kishin ƙasar da suke da shi.

DAGA LARABA: Abin ya sa ’yan Nijeriya ke kishin ƙabila fiye da ƙasa

Wasu daliban Najeriya a kasar waje

Kishin ƙasa na cikin abubuwan da shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Nijeriya a kullum a kansu.

Muhimmancin kishin ƙasa ga ci-gaban al’umma, musamman a ƙasa mai ƙabilu da addinai daban-daban irin Nijeriya, abu ne da ba zai misaltu ba.

Sai dai alamu na nuna cewa ’yan Nijeriya sun fi nuna kishin ƙabilun da suka fito idan aka kwatanta da kishin ƙasar da suke da shi.

Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan wannan batu.

Domin sauke shirin, latsa nan